Zaben Gwamnoni: Jerin Jihohi 15 Da PDP Ka Iya Samun Nasara Kan  APC 

Zaben Gwamnoni: Jerin Jihohi 15 Da PDP Ka Iya Samun Nasara Kan  APC 

A ranar 18 ga watan Maris ne yan Najeriya a jihohi mabanbanta za su fita rumfunar zabe domin zabar yan takarar da za su jagorance su a matsayin gwamnoni na tsawon shekaru hudu masu zuwa. 

Za a gudanar da zabukan gwamnonin ne a fadin jihohi 28 daga cikin 36 na Najeriya.
Kamar yadda hasashen kungiyoyin Enough is Enough (EiE) da SB Morgen (SBM) suka nuna, jam'iyyar PDP na iya lashe jihohi 15 a zabe mai zuwa. 
Jihohin sun hada da Sokoto, Kebbi, Oyo, Katsina, Kaduna, Bauchi, Gombe,
Sai kuma Adamawa, Cross River, Akwa Ibom, Rivers, Delta, Taraba, Ebonyi, Plateau.