Dalilin Rabuwar Jam'iyyar APC Gida Biyu a Sokoto

Sani Yakubu ya shedawa jama'a cewa nan ba da jimawa ba za su bude sakatariyar jam'iyar APC a jiha wadda shuagabanni a kasa suka aminta da ita, haka kuma za su nada sabbin shugabanni domin jan ragamar jam'iyar a matakin jihar Sokoto.

Dalilin Rabuwar Jam'iyyar APC Gida Biyu a Sokoto

Jam'iyar APC mai mulki a jihar Sokoto da ke Arewa maso yammacin Najeriya ta dare gida biyu, sakamakon wani sabon rikici da ya kunno kai a cikinta, har ta kai ga samun wani ɓangare da ke hamayya da ɓangaren da ke biyayya ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da  gwamnatin jiha.

Wasu daga cikin ƴaƴan jam’iyyar na goyon bayan ɓangaren gwamnan jihar da sanata Aliyu Magatakardar Wamakko ke jagoranta, yayin da dayan bangaren kuma ke goyon bayan Sanata Ibrahim Lamiɗo, wanda ake hasashen zai nemi takarar Gwamnan jiha a 2027.

Rikicin dai ya yi ƙamarin da har takai ga wasu da ke goyon bayan ɓangaren Sanata Lamiɗo ajiye muƙaman da suke riƙe da su a jam’iyya da kuma waɗan da ke riƙe da shi a gwamnatance.

Honarul Sani Alhaji Yakubu, daya ne daga cikin ƴan majalisar wakilai daga jihar ta Sokoto, da ke goyon bayan ɓangaren Sanata Ibrahim Lamiɗo ya ce sabuwar tafiya ce ta ɓulla a jam’iyyar APC a jihar Sokoto.

Har ila yau, ya ce, "An tsinci kai a wani yanayi na siyasa wanda mutane da kansu suka fahimci gaskiya, Sanata Lamido wanda shi ne wanda Allah ya bai wa wanna matsayi na shugabanci da ya ke yi, ya zo da salon ci gaban al'umma da tafiya da kowane ɓangaren, shi yasa wadanda ke aiki a wasu wuraren suka ajiye aikinsu suka ga dacewar komawa ƙarkashinsa, saboda kishin jama'ar da ya ke da shi'' inji shi.

"Mu ma mun yarda da abin da mutane da dama suka fada na cewar lallai abin da ake yi ba dai dai ba ne, mun yi magana cewar a sauya ba a yi ba, kuma mun ga abin da ake yi  bai dace ba''

Ya ce suna nan a jam'iyyar APC ba za su sauya sheka ba, illa ma kirkirar wani sabon bangare a jam'iyyar da zai kalubalanci jagorancin gwamnan jihar a jam'iyyar ta su.

Sani Yakubu ya shedawa jama'a cewa nan ba da jimawa ba za su bude sakatariyar jam'iyar APC a jiha wadda shuagabanni a kasa suka aminta da ita, haka kuma za su nada sabbin shugabanni domin jan ragamar jam'iyar a matakin jihar Sokoto.

Sai dai a martanin shugabancin jam’iyyar APC a jihar Sokoto ya ce rikici ne da bai dauke shi komi ba duk da guguwar da ta ja wasu yan jam’iyyar har suna ajiye mukamansu, amma shugaban jam’iyyar a jihar sokoto Sadik isa Achida ya ce kofa a bude take ga duk mai son fita.

"Mu bamu san da wanna rikici ba, sannan babu wani da ya aiko mana takardar cewar ya ajiye mukaminsa, sannan kuma wai wane ne Sanata Ibrahim Lamiɗo ma? Sanata ne kawai da aka zaɓa a Sokoto, bashi da wani muƙami a Sokoto ko a jam'iyya, amma kuma ya sani jam'iyya ce ta yi masa yaƙin neman zaɓe har ya yi nasarar samun kujerar da ya ke a kanta'' inji shugaban jam'iyyar APC a jihar ta Sokoto.

Haka kuma Sadik Isa Achida shugaban jam'iyyar APC a jihar Sokoton ya ce "matsayin Sanata Lamido a wajensu shi ne dan jam'iyya ne shi kawai, kuma bai sanar da mu cewar an masa wani abu ba'', hirarsa da manema labarai.