Ƙungiyar PDP Mandate Ta Miqa Masu Canja Sheka Sàma Da Dubu Ga Uwar Jam'iyyar PDP A Neja

Ƙungiyar PDP Mandate Ta Miqa Masu Canja Sheka Sàma Da Dubu Ga Uwar Jam'iyyar PDP A Neja




Daga  Awwal Umar Kontagora, Minna.

PDP Mandate ta mika sama da mutum dubu daya yayan jam'iyyun APC, NNPP da PDM da suka yi canjin sheka daga jam'yyun su zuwa jam'iyyar PDP a karamar hukumar Bosso.

Tunda farko a bayaninsa, jagoran matasan PDP kuma jigo a kungiyar, Amb. Nura Hashim ya bayyana cewar wadannan jama'an sun gaji da wannan mulkin na APC tsawon shekaru bakwai da watanni talakawan jihar nan ba su san da akwai gwamnatin jiha ba, domin idan ka dubi yadda aka karya tattalin arzikin talakawa a jihar nan abin bakin ciki ne, garkuwa da mutane a gonakin su, tarwatsa karkaru ana farautar fan Adam kamar ana farautar bera a wannan gwamnatin muka gan shi, saboda haka PDP Mandate ta gabatar min da wasu 'yan jam'iyyu da suke rike da mukaman jam'iyya sun amince su dawo PDP dan mu yi aiki tare.

Kamar yadda muka gudabar da wannan taron yawon a karamar hukumar Bosso, haka za mu yawuta sauran kananan hukumomin jihar nan dan fitar da kitse daga wuta, a shirye muke mu yiwa jam'iyyar PDP aiki dan ganin mun samu nasarar babban zabe mai zuwa, muna kara jaddawa al'ummar jihar nan da yardar Allah idan mun dawo kuskuren da mu ka yi a baya ba za mu sake yin irinsa ba.

Alhaji Garba Danlami, shi ne shugaban PDP a karamar hukumar Bosso, da ya wakilci shugaban jam'iyyar ta jiha, Barista Tanko Beji. Yace batun dawowar wadannan al'umma a PDP abin a yaba ne domin mu da su manufar mu daya ce, itace dawo da martabar jihar nan ta hanyar mutunta tsarin dimukurafiyya.

Saboda daman yayan PDP da  suka tafi cirani kuma sun fahimci gidan da suka bari nan ne mafi dacewa a zaman su, da wanda ya fara PDP 1999 da su da suka shigo yau, da su wadanda  da suka dawo PDP yau duk daya ne a wajen mu.

Beji, ya bada tabbacin a wannan tafiyar ba wanda za a bari baya uwar jam'iyya za ta tabbatar ta tafi da kowa musamman a yanzu da ake sa ran fara yakin neman zaben 2023 ba da jimawa ba.

Daya daga cikin wanda ya jagoranci masu canjin shekar, Hon. Sani Ashiru Bazanga, yace dukkanin wadannan mutanen zangon farko ne da suka nemi dawowa PDP ta hannun jagoran mu, Amb. Nura Hashim a karkashin PDP Mandate kuma yanzu haka akwai wasu jigogin jam'iyyar APC da muke shirin karban su.

Hon. Abdullahi Sa'idu Pyawu, yace wannan ba abin mamaki ba ne, PDP tayi mulkin jihar nan kuma saboda zakuwa da jin dadi al'ummar jiha suka nemi canjin gwamnati wanda APC ta karba shekaru bakwai ke nan da watanni al'umma sun kosa jam'iyyar PDP ta dawo.

Kamar yadda na ji Ambasada Nura Hashim ya fada ne a jawabinsa, wannan gwamnatin ake cewa jiki magayi, kuma duk wanda bai godewa ni'imar Allah ba, ai dole yayi da nasani.

Taron wanda irin shi ne na farko da PDP Mandate ta shirya a sakatariyar jam'iyyar ta karamar hukumar Bosso ta taho da sabon salo domin akwai fuskokin wasu fitattun yan APC da har yanzu ba su bayyana ficewarsu ko cigaba da zama jam'iyyar ba.

Ya samu halartar 'yan takarkarun majalisar jiha da ta tarayya da ya shafi kananan hukumomin Bosso da Paikoro.