Shugaba Buhari Ya Bukaci Yan Nijeriya Su Sake Zabar APC a 2023

Shugaba Buhari Ya Bukaci Yan Nijeriya Su Sake Zabar APC a 2023

Shugaba Buhari Ya Bukaci Yan Nijeriya Su Sake Zabar APC a 2023

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, a gangamin yakin neman zaben shugaban kasa a Yobe, ya bukaci yan Nijeriya su sake zabar jam'iyyar APC a babban zaben 2023 mai zuwa, ya ce gwamnatinsa ta cika dukanin alqawaran da ta dauka, saboda haka a su zabk Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima, kuma a Yobe a sake zabar Gwamna Buni a karo na biyu tare da baki dayan yan takarar jam'iyyar a babban zaben mai zuwa.

Shugaban ya bayyana haka ga cincirindon magoya bayan jam'iyyar APC, ranar Talata a taron gangamin yakin neman zaben Shugaban kasa wanda jam'iyyar ta gudanar a filin wasa na August 27 dake Damaturu, ya ce yan Nijeriya su sake marawa jam'iyyar APC baya saboda su ci gaba da ingantattun ayyukan raya qasa da ya fara, bunqasa tattalin arziki da ci gaba a fannin tsaro ga qasa.

Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi kokarin yin galaba kan yaki da Boko Haram Arewa Maso Gabas, gwamnatin APC, fiye da kowane lokaci, al'amarin da ya zame alakakai ga hadin kan Nijeriya, wannan kadai ya isa hujja ne ga yan kasa.

Har wala yau, ya kara shaida wa dubban magoya bayan jam'iyyar irin mummunan ta'addancin da Boko Haram ya yiwa al'umma, ta hanyar barnata dukiya da yiwa tattalin arziki zagon kasa, kafin sojojin Nijeriya da sauran jami'an tsaro su fattatake su.

Shugaban ya nemi yan Nijeriya su himmatu wajen neman ilimi, su manta da tunanin Boko Haram na adawa da ilimi, ya ce musamman iyaye inda ya ce, ‘‘Ku tabbatar sun tura ya'yanku makaranta, kuma ku yi kokari wajen fahimtar dasu cewa duk abin da ka samu a duniya mai karewa ne idan ba ilimi ba."

‘‘Saboda zan iya tuna maraicin da nayi; wanda ya jawo ban ga mahaifina da idona ba. Kuma sai da na shafe shekaru 9 a makarantar kwana, saboda in nemi ilimi, wanda daga bisani na shiga aikin sojan Nijeriya."

‘‘Zan so ku jaddada imaninku, ku yi kokari wajen tafiyar da rayuwa kuma ku rike ya'yan ku da iyalinku cikin amana da gaskiya. Kar ku ha'inci wanda ya baku amana."

Bugu da kari kuma, Shugaba Buhari ya gargadi yan takara a karkashin jam'iyyar APC, a zabe mai zuwa da cewa su tabbatar sun yi shugabanci nagari, kar su ci amanar talakawan da suka zabesu.

A hannu guda kuma, ya ce jam'iyyar APC ta cika dukanin alkawuran da ta daukar wa yan Nijeriya, cikin shekaru takwas da suka gabata tana mulki a matakin tarayya, inda ya sha alwashin ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba da inganta Nijeriya.

A nashi vangaren, dan takarar Shugaban kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci yan Nijeriya su yi watsi da jam'iyyun adawa, su ci gaba da rike taragon jirgin gwamnatin da Buhari yake tukawa.

‘‘Saboda wannan gwamnati ce ta masoya ci gaban kasa, masu mutunci da gaskiya."

Haka kuma, Bola Tinubu ya jinjinawa Shugaba Buhari a kokarin sa wajen dawo da zaman lafiya a Arewa Maso Gabas, inda ya yi alkawarin ci gaba daga inda Buhari ya tsaya, tare da bunkasa harkokin noma wanda zai mayar da yankin cibiyar noma ta Nijeriya.

‘‘Sannan kuma zamu baku ayyukan da zaku dogara da kanku. Kuma zamu farfado da ayyukan noma, mu kori yunwa kuma mu baku duk abin da ya dace- mu baku tallafin kudi don ku gina gidaje."

Har wala yau, Tinubu ya yi alkawarin idan ya kafa gwamnati yajin aikin kungiyar mallaman jami'o'i ta kasa (ASUU) ya zama tarihi, inda ya kara da cewa al'amarin da zai sanya dalibai zasu kammala karatu cikin lokutan da suka dace.

A karshe Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga al'ummar Yobe da Arewa Maso Gabas su zabi yan takarar APC a babban zabe mai zuwa, inda ya tabbatar da cewa gwamnatin da zai kafa zata dawo da martabar tattalin arziki a Nijeriya.