Za mu cika alƙawalin da muka ɗauka kan matsalar tsaro----Sanata Lamido

Za mu cika alƙawalin da muka ɗauka kan matsalar tsaro----Sanata Lamido

Ɗan majalisar dattijai mai wakiltar Sakkwato ta Gabas Sanata Ibrahim Lamido a tattaunawarsa da manema labarai a Sakkwato ya bayyana dalilin da ya sa yake mayarda hankali kan harkar tsaro da ilmi da matasa fiye da wasu bangarori na rayuwa.

"Harkar tsaro ta zama mai muni kafin mu yi nasara a zaɓe, mun yi alkawarin in mun samu gwamnati za mu mayar da hankali kan tsaro, shi ne ya sa tun farko na fara da shi, a yanzu wani gefe a kananan hukumomin da nake wakilta an samu sauki wani wurin kuma ba a samu ba, amma dai an samu sauki fiye da lokacin baya ina tabbatar maka a shirin da nake yi duk da harkar tsaro ba a fadi, amma da zaran shirin ya kammala nan da dan lokaci kadan kowace karamar hukuma a yankina za su samu zaman lafiya da ikon Allah."

Da juya kan matasa da ilmi ya ce, "ilmi dole ne mu dauke shi da muhimmanci, matasa su ne yakama ataimaka don su ne za su zama jagororin gobe a halin da ake ciki matasa ne ake hasashen sun fi dadewa a duniya, su ne in ka taimaka za su taimaki wasu, hakan ya sa nake kokarin samarwa matasa abin yi, rashin abin dogaro na kara ta'azara rashin tsaro,"a cewar Sanata Lamiɗo.

Sanatan ya mayar da hankali kan hidimar jama'a domin shugabanci abin tambaya ne a gobe kiyama, ya ce "abin da ka baiwa al'umma shi ne naka, ina son na taimaki jama'a.

"A wannan shekarar ta 2025 ina da kudirin abin da zan yi  sai ya fi na shekarar baya in sha Allah,"in ji Lamiɗo.