ƘADDARA TA: Fita Ta 16

ƘADDARA TA: Fita Ta 16
  ƘADDARA TA:
        Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 16*
                  ~Washe gari ta gama girki zata shiga domin gyara ɗakin da take gyarawa a kullum, hanu tasa zata buɗe kofan a lokacin Aneeta ta fito tayi bala'in kyau cikin dogon rigan shadda yasha zubi me kyau ta ɗaura alkyabba purple akai dogon takalmi me tsini ne a kanta, tana rungume da jaka a kirji, karo sukaci Aneeta takalmin kafarta ya lankwashe ta faɗi kasa takaddun da take rungume dasu suka watse, hotuna ne dayawa da sauri kafin ma ta tashi ta fara tattara hotunan tana ɓoyewa, Aneeta da mamaki take kallonta da alama bataso aga hoton da take ɓoyewa bata damu da faɗuwan da tayi ba burinta ta ɓoye hoton kada a gani, taka hoton dake gabanta tayi da kafa tana kallon Aneeta data gama kwashewa ta ɗago tana share kuran daya ɓata jikinta, wani mugun kallo ta aikawa Asmee batasan dalili ba ta tsani wannan me kama da aljanun, a fusace taje ta wanketa da mari tace "ke makauniya ce da zaki bigeni?"
kanta kasa tace "kiyi hakuri"
tace "wawiya, kazamiya, ƴar kauye, baiwa, kaskantacciya ƴar gidan talakawa, me kama da aljanu"
shiru tayi tana jin zafin zagin da take mata ga kuma marin da har fuskan yayi ja, tsaki taja ta barta a wajen, motarta ta shiga taja da speed ta bar gidan, a hankali ta durkusa ta share hawayen sannan ta ɗauki hoton data taka Aneeta bata gani ba, ɗauka tayi ta tafi ɗaki dashi, ɓoyewa tayi bata bari kowa ya gani ba, saida ta rage ita kaɗai a ɗakin kafin ta kalli hoton taga mutane biyu ne Aneeta da wata a gefe, sunyi bala'in kyau sanye da alkyabba dukansu a jikinsu, da mamaki tace "wacece wannan da Aneeta bataso aga hotonsu tare?"
jin karan kafar mutum tayi saurin ɓoyewa, salma tace "kizo lokacin girki yayi"
taja hanunta tace "salma dan Allah kizo zan tambayeki"
shigowa tayi, nuna mata hoton tayi, dafa kirji salma tayi tace "aina kika samu hoton gimbiya zeenat?"
tace "wacece ita?"
salma tace "tsohuwar matar yarima ce"
tace "me haɗinta da Aneeta?"
kallon hoton ta kara yi, ta dafa kirji tace "Asmee wallahi ina rabaki asmee ki cire idonki akan abinda ya shafi wannan masarautan, amma taya akayi hoton gimbiya zeenat ya haɗu dana Aneeta?"
tace "ba wannan ba hotuna dayawa na gani a wajenta kuma tare sukayi to me haɗinsu? sannan ina zeenat ɗin?"
salma cikin tsoro tace "wannan shine amsan karshe da zan baki Asmee zan iya rabuwa dake na daina haɗa hanya ma dake sabida banaso ki jefani cikin masifa, akwai wata halima da tazo gidannan tasa ido akansu bayan sun san tana bibiyansu sukasa aka ratayeta a gabanmu, ba ita kaɗai ba harda kawarta da suke mutunci saida aka kashe to asmee lokacin rabuwana dake yazo, zeenat ta mutu kuma ana zargin yarima hameed ne ya kasheta, asmee dan Allah kada ki kara cewa kin sanni sabida inason rayuwata"
fita tayi daga ɗakin, Asmee tabi hoton da kallo tace "zeenat ta mutu? to amma me haɗinta da Aneetan?"
ɓoye hoton tayi ta yadda babu me gani, fita tayi daga ɗakin taje suka fara girki salma baya baya take yi da ita.
washe gari da safe taje domin girki saida Aneeta ta tafi school kafin taje tana gyara ɗakin, batasan yana ciki ba tayi ta aikinta tayi zaton ma bai kwana a gidan ba, burner ta ɗauka taje tasa garwashi tasa turaren wuta, ɗakin ta nufa yana hayaki yana fita da kamshi, rufe ido tayi tana jin daɗin kamshin, ganin falon ya cika da hayaki da kamshi tace "bari na kai ciki"
shiga tayi dashi ta tsaya tanaso hayakin ya karaɗe ɗakin, kusa da gadon ta tsaya, a hankali ya buɗe kofan bathroom ɗin ya fito ɗaure da towel a kwankwaso, rufe kofan yayi zai wuce ciki yaga hayaki, juyowa tayi jin karan buɗe kofa sukayi ido huɗu, juyawa tayi tana cewa "dan..dan..dan Allah kayi hakuri ban san kana ciki ba"
ji tayi ya faɗi akan gado, da mamaki ta juyo tana kallonshi, baya baya ya fara yana girgiza mata kai, da mamaki tace "menene?"
gani tayi yana zufa idanunshi suna komawa ja, ta kasa fita ta barshi kawai tace "meya faru?"
matsoshi ta fara domin yanayinshi ya bata tsoro, baya ya fara yana ɗaga hannu yana mata alaman dan Allah kada tazo inda yake, gani tayi ya ɗauki pillow yana rufe fuskanshi, tace "ko dai yanada aljanu?"
kuka ya fara mata, ya diro daga gadon ganin tana shirin hawa, aje kaskon tayi tana shirin fara karanta addu'a taji ya kanƙameta yana manna jikinshi da bayanta, a tsorace tace "ka sakeni nikam ka sakeni"
girgiza kai yake yana kara riketa, gani tayi yana nuna wutan alama wutan yake tsoro, tace "wutan kake tsoro?"
jijjiga kai yayi, tace "to ka tsaya zan fitar"
kin sakinta yayi, cikin lallashi tace "ka sakeni zan fitar dashi kaji?"
a hankali ta cire hanunshi daga jikinta wutan ta ɗauka ta fita dashi, dawowa tayi taga ya takure a gefen gadon yayi shiru jikinshi yana rawa, jikinta yayi sanyi, ta buɗe wardrobe ta ɗauko mishi jallabiya tace "gashi kasa"
girgiza kai yayi yana kara ɓoye fuskanshi, tace "kayi hakuri kasa babu wutan yanzu"
shiru yayi yana kallonta, karɓa yayi yasa, kwanciya yayi akan gado, ta juya zata tafi hanunta ya rike, ta juyo tana kallonshi, girgiza mata kai yayi alaman dan Allah kada ta tafi, idonta ne ya cika da hawaye ya nuna mata gefenshi, a hankali ta zauna, ya ɗaura kanshi a cinyarta, da sauri ta ture kanshi, riketa yayi sosai yaki janyewa, a hankali yasa hanunta a kanshi yayi shiru yana hawaye, itama shiru tayi tana share hawayen data rasa na menene, jin yayi nauyi tayi saurin sauke kanshi daga jikinta fita tayi daga ɗakin tace "Asmee ki dawo hayyacinki wanda akace ya kashe matarshi shine zaki ji tausayinshi?"
fita tayi tace "dole nayi nisa dashi"
aikin gabanta taje ta fara yi.
meenat ce tazo da leda a hanu sallama tayi asmee ta amsa, bata ledan tayi tace "gashi wannan ki rabawa kowa"
durkusawa tayi ta karɓa domin haka suke karɓan komai daga hanun yaran sarki sai sun durkusa, juyawa tayi zata tafi tace "Ameena"
tsayawa tayi ta juyo tace "ba Ameena ba sunana meenat"
tace "to meenat nawa nawa zan raba?"
tana amsa kiran da alameen yayi mata tace "biyu biyu za'a shigo miki da sauran"
amsa call ɗin tayi cikin shagwaɓa tace "baby nayi fushi da kai"
sai kuma tayi dariya binta da kallo Asmee tayi, da kyar taja kafa ta tafi.
Najeeb ne zaune a office nashi yayi bala'in kyau cikin suit baki yana zaune tare da wasu mutane wanda sukazo da jaka a hanunsu cike da diamond, fuskanshi babu walwala sam baya dariya, fatarshi yayi kyau sabida abinci me kyau da kuma ac da yake ciki a kullum a gida da kuma mota, buɗe jakan da suka turo mishi yayi ya ɗauki ɗaya a cikin diamond ɗin ya ɗaga sama yana kallo, ɗaukan wani abu yayi ya gwada yaga ba fake bane, kallonsu yayi cikin rashin magananshi a takaice yace "nawa kuke buƙata?"
sukace "biliyan biyu"
rufe jakan yayi ya aje a kasa kusa dashi yace "deal"
kiran waya yayi fadeel da yake zaune a cikin company yana hira da masu aikin yayi bala'in kyau shima wayanshi yayi kara da sauri ya ɗaga domin babu me kiran wayarshi sai yayanshi wato najeeb, yace "na'am yaya"
tashi yayi yace "to"
kashe wayan yayi ya nufi wani ɗaki dake a keɓe kuɗi masu yawa ya fito dasu a jaka, zuwa yayi da sallama ya shiga cikin respect ya bawa najeeb, karɓa yayi ya mika musu yace "ga kuɗinku"
karɓa sukayi sukayi godiya sannan suka tafi, fadeel zai fita yace "zo"
zuwa yayi yace "zauna"
zama yayi, yace "me yake damunka naga kana ramewa kwana biyu?"
shiru yayi, yace "ba magana nake maka ba?"
a hankali yace "ba komai yaya kawai ina tunanin iyayena da suka mutu ne"
yace "ka daina damuwa da yawan tunani fadeel komai na duniya me wucewa ne kai kaɗai nake dashi, idan ina ganinka cikin damuwa ya kakeso nayi da rayuwata?"
yace "kayi hakuri ya najeeb zan daina"
yace "yawwa dan Allah ka daina"
yace "to"
"zaka iya tafiya ka rage surutu dan naga sai surutu kake"
yace "to yaya"
fita yayi, najeeb ya jingina da kujeran yana juyawa a hankali kanshi na kallon sama, hawaye ya share cikin zafin daya kasa gushewa a ranshi yace "ko suna raye? ko sun mutu? Allah ne kaɗai ya sani"
shiru yayi yana hawaye yana tuna matarshi da kanwarshi da mimi, kowane rana sai yayi sadaka da niyan lada yaje musu a duk inda suke.
shima fadeel kullum cikin sadaka yake Allah yaji kan iyayenshi.
Asmee ido tasa akan Aneeta duk wani motsinta tana kallonta tana biye da ita kuma, yauma kamar kullum ta gama kimtsa ɗakin kenan ta fito taji suna taro a falon kuma harda alameen da mahaifiyarshi da alama fa magana suke akan auren meenat da alameen, a hankali tazo zata wuce meenat tace "ji mana"
tsayawa tayi, tace "kawo ruwa da lemo"
a hankali kamar ba jini a jikinta taje ta kawo ruwan da kuma lemo dayawa tazo ta aje, ji tayi Abi yace "ba zamu sa auren da nisa ba nan da wata ɗaya za'a ɗaura auren"
cikin girmamawa maman alameen tayi godiya, jikin Asmee yana rawa ta tashi ta fita, ɗaki taje tace "na shiga uku aure kuma? akan aure?"
da sauri tace "ina bazan taɓa bari haka ya faru ba saina san duk yadda zanyi na hana wannan auren"
kasa zama tayi, sai kuma tace "to idan na hana inada tabbacin hamma najeeb zai dawo? kada fa na hana kuma ta dawwama babu aure"
meenat ce ta fito tana raka su maman alameen da ƴan uwanta da alama ta saba dasu sosai, har wajen motansu ta kaisu har suka fita tana ɗaga musu hanu, komawa tayi da sauri Asmee ta fito domin yi mata magana, rike kai meenat tayi tace "wayyo inajin jiri"
faɗuwa tayi kasa a sume da gudu Asmee tazo tana bubbugata tana kiran sunanta, ɗagata tayi ta shiga da ita ciki, ammi tace "meya sameta?"
tace "faɗuwa tayi tana tafiya"
akan sofa suka kwantar da ita, ammi ta ɗaga waya tana kiran kaseem ganin kiran ammi ya ɗauka tace "ka dawo gida meenat tana tafiya kawai ta faɗi"
ya kashe wayan, babu jimawa ya dawo gidan, su hameed duk suna kanta, kallon asmee yayi ya mata alaman meya sameta?
tace "faɗuwa kawai tayi"
yana kallonta yanaso yayi magana amma ya kasa, harara ta banƙa mishi ganin yana mata kallon kamar itace tasa ta faɗi, ganin tana hararanshi ya nuna kanshi alaman ni kike harara?
ɓata rai tayi ta koma bayan ammi ta yadda ba zai iya taɓa ta ba sabida tana ganin yadda yake huci, wani kallon haushi yake mata har ya kaseem ya shigo, fara dubata yayi yace "bari nayi text na jininta"
ɗakinshi ya shiga ita kuma meenat ta buɗe ido tana jin amai sosai, tace "zanyi amai"
Asmee ce ta riketa kafin ma su tashi ta fara amai, asmee tace "sannu sannu"
banda sannun babu abinda take faɗa mata, lumshe ido tayi ta koma ta kwanta tana jin zazzaɓi sosai, asmee cikin rashin kyama ta goge aman, tazo ta zauna kusa da ita ta rike hanunta da yayi zafi tace "sannu Ameenah sannu"
shiru tayi kawai tana lumshe ido, ya kaseem baya ganin hanya me kyau ya fito daga ɗakin, Ammi tace "me yake damunta kaseem?"
yace "ciki"
ba ammi ba har hameed saida ya samu waje ya zauna, itama meenat batasan lokacin data tashi ba duk da jirin da takeji, tace "what?"
wani kallon daya aika mata saida ta koma bayan ammi ta riketa, ammi tace "amma kayi gwaji me kyau?"
yace "ba yau na fara aiki ba ammi meenat ciki take dashi"
girgiza kai tayi tazo gaban hameed daya dafa kanshi ta rike hanunshi tace "wallahi tallahi yaya yarima na rantse muku da Allah ban taɓa zina ba"
fizge hanunshi yayi ya tashi ya nunata da yatsa ga magana babu daman faɗa kawai ya fara kuka, Asmee jikinta yayi sanyi, meenat tazo gaban kaseem ta durkusa tace "na rantse da Allah ya kaseem ban taɓa zina ba, ban taɓa sanin wani namiji ba a rayuwata"
Aneeta tace "kenan a ruwa kikasha cikin meenat?"
tayi magana tana karasowa sanye da wando palazzo da riga na material me kyau kanta da wani hula na material ɗin pink, flat shoe ne a kafarta tace "a ruwa kikasha?"
ta girgiza kai tace "wallahi ban taɓa zina ba kema kin sani...."
da sauri tace "A,a gaskiya ni ban sani ba binki nake duk inda zakije bale nasan ko zakiyi ko ba zakiyi ba?"
hameed juya baya yayi yana hawaye masu zafi, Abi yace "meenat kin san nan gidan sarauta ne ko? meyasa zaki janyo mana wannan abin kunyan?"
tace "wallahi Abi...."
tsawa ya daka mata yace "kimin shiru ban haifi ƴar iska ba kuma ba zan haifa ba, sabida haka yanzu zaki bar gidannan"
Asmee ta buɗe baki zatayi magana, maganan salma dana security ne data tuno yasa tayi shiru da bakinta, juyawa tayi zata fita taji kaseem yace "babu inda zataje amma za'a zubar da cikin"
juyowa Asmee tayi jin za'a zubar da cikin da take da tabbacin na hamma najeeb nata ne, da sauri ta fita, tana shiga ɗaki tace "ya zama dole na hana faruwan hakan, na yadda ta haifa ni zan rike yaron zan reni yaron da hanuna amma wallahi ko zan rasa rayuwata ba za'a zubar da cikinnan ba, nasan maganin da zan bata tasha ko zasu kare rayuwarsu wajen zubar da cikin nan ba zai zube ba"
murmushi me kyau tayi tace "kuma saina bata kota halin kaka"
kwanciya tayi har dare babu inda taje sabida sun gama aiki tun ɗazu, saida dare yayi duhu kafin ta saci hanya ta fita a gidan da kafa take tafiya bayan ta tambayi securityn da yake taimakonta inda zata samu daji akwai abinda takeso, kuɗin hanunta ta shiga taxi dashi, har bayan gari ya kaita ta fara tafiya da toci, duk duhun da yake wajen bata damu ba tana jin sautin kukan karnuka, tsakiyan dajin ta shiga cikin rashin tsoro ta fara neman ganyen, bata samu ba saida ta kara gaba, hamdala tayi ganin ganyen fata fito nema tsinka tayi ta haɗa da jijiyan tasa a ledan hanunta, zata tafi ta tuna da maganan hamma najeeb idan kinje tsinkan magani ki rufe ido kiyi addu'a ki roki Allah ya baki maganin da kikaje nema ki faɗi maganin me kikeso kina addu'a kina tafiya har sai kin gama addu'an saiki buɗe ido duk ganyen da kika gani a gabanki ki tsinka kisa a ranki shine maganin ki bada da zuciya ɗaya, da yaddan Allah za'a samu sauki"
murmushi tayi tareda hawaye, rufe ido tayi tace "ya Allah magani nake nema wa yayan matar yayana dan soyayyan da yayana yake yiwa matarshi nakeso na taimaki yayanta hameed, shi kurma ne yana ji amma baya iya mayarwa Allah ka bani magani na bashi yayi sauki nasan koda hamma najeeb yana nan shine babban taimakon da zai musu, inaso na wakilci yayana"
buɗe idon tayi, wani ganye ta gani me kyau dayawa murmushi tayi sannan ta durkusa tasa fararen yatsunta masu kyau da albarka ta tsinki dayawa tasa a ɗayan ledan sannan ta kalli sama tace "Allah na gode ka bani magani"
kallon maganin tayi sannan ta haska hanya ta fara tafiya, da kyar ta fito daga dajin ta fara tafiya ta gaji amma saida ta shigo gari duk da dare yayi saida taje wani chemist ta siyi sirinji kafin ta shiga taxi domin komawa gida, tun daga nesa tace ya ajeta ta biyashi kuɗinshi sannan ta fara tafiya a hankali cikin sanɗa ta saman kofan ta hau zata dira taga mutum tsaye a bakin kofan da alama dawowa yayi sannan cikin sanɗa yake tafiya sai kuma taga ya nufi wani hanya wanda da gani na sirrine a gidan, durowa tayi cikin sanɗa ta fara bin bayan meshi, jin kamar ana bin bayanta ta juyo da sauri Asmee ta ɓuya, sai kuma taga ba'a binta taci gaba da tafiya, itama binta taci gaba dayi, sunyi tafiya me nisa kafin taga ta shiga wani lungu, makulli ta ciro a lokacin ta kunna toci tana haskawa, da sauri tace "Aneeta? me takeyi anan?"
binta tayi ganin ta shiga sai taga kuma ta rufe kofan, zuwa tayi tana neman hanyan shiga babu, saida Aneeta ta jima a ciki sannan ta fito, da sauri ta ɓuya har saida ta tafi kafin ta fito tana kallon wajen ta rufe da makulli tace "me anan? me aka ɓoye?"
tafiya tayi ta koma ɗaki, banɗaki ta shiga ta dama maganin sosai sannan taja a sirinji ta ɓoye sauran a cikin kayanta, fita tayi daga ɗakin ta hanyan da security ya faɗa mata akwai ɓoyayyen hanya ta wajen tabi ta shiga cikin falon da basu rufe da makulli ba, wutan ɗakin a kashe yake a hankali take tafiya tasan ɗakin ba zai taɓa ɓata mata ba ko a cikin duhu, a bakin kofan ta tsaya tana addu'a sannan ta buɗe ta shiga, hamdala tayi ganin wuta a kashe alluran ta kalla sannan ta shiga ciki, bedroom ɗin ta shiga tana lekawa taga meenat tana bacci, cikin sanɗa ta karasa wuta a kashe bedside lamp kawai ta kunna, pillow ta ɗauka ta danne kan meenat, cikin bacci ta fara harba kafa tana son kwace kanta, alluran ta soka mata saida ta juye ruwan maganin duk a jikinta sannan taci gaba da riketa, tasan yanzu zai sata bacci babu jimawa taji ta daina fizge fizgen, sauke pillow tayi ta gyara mata gashinta da ya barbazu, murmushi tayi ta shafa kyakkyawan fuskanta tace "Allah ya saukeki lafiya matar yaya"
fita tayi cikin sanɗa ta bar ɗakin ta rufe mata sannan ta fara tafiya domin fita, godewa Allah tayi da babu wanda ya ganta har ta koma ɗaki ta kwanta.
washe gari ya kaseem ne ya gama shirya duk wani abinda zai zubar da cikin dashi, Ammi duk cikin damuwa suke babu wanda ya iya koda shan ruwa ne balantana breakfast, kaseem yana fitowa ammi tace "yawwa kaseem gara daka fito kaga duk nan mun kasa cin komai dan Allah a zubar da cikinnan"
meenat wacce take ji a ranta bataso cikin ya zube tayi shiru tana kallonsu, a ranta tace "shiyasa jiya nayi mafarki anzo anyi min allura a cikin baccin"
magani ya bata yace "tashi"
tashi tayi jikinta a mace domin ta rasa me take ciki ta rasa me yasa aljanu zasu mata ciki?
cikin rawan murya tace "ya kaseem ko dai aljanu ne sukamin?"
shiru yayi ya bata ruwa da maganin yace "shanye"
sha tayi, ya ɗau allura yace "juyo"
juyowa tayi ya sauke skirt ɗin kasa kaɗan sannan yayi mata alluran, runtse ido tayi tace "wayyo Allah"
ammi tace "ki rufe mana baki kafin na kai miki mari kin san ansa date ɗin aurenki da alameen idan yasan haka ba zai taɓa yadda ya aureki ba, bama wannan ba zaki ɓata sunan masarautar mu"
shiru tayi tana hawaye bata yadda ta haɗa ido da kowa cikinsu ba, da kyar suka iya breakfast basuci abin kirki ba.
Asmeeta ce ta shigo da niyan yin aiki tazo ta durkusa har kasa ta gaida Abi, amsawa yayi ta gaida ammi sannan ta kalli meenat dake kuka kanta kasa sai hawaye kawai, tausayi taji ta bata, kaseem yace "ki rinƙa zuwa kina kula da ita tunda batada lafiya komai takeso kiyi mata amma ki sani duk ranan da mukaji wani abu daga bakinki zan kasheki"
da sauri tace "to"
tashi tayi zata tafi sai kuma ta dawo tace "mai martaba inason magana da kai idan babu damuwa"
da mamaki suka kalleta, yace "ina jinki"
tace "idan ba damuwa inaso mu keɓe"
duk suka bita da kallon tuhuma, Abi yace "okay muje"
tashi tayi ya bita suka fita waje, ta durkusa kasa tace "mai martaba na taso a gidanmu suna bada magani nima banyi gadon komai ba sai bada magani, akan laluran yarima hameed idan babu matsala abani dama zan bashi magani"
ya kalleta sannan yace "babu abinda nake fata a rayuwata kamar naga hameed ya samu lafiya, babu irin kuɗin da ban kashe ba domin ganin hameed ya fara magana to amma Allah baiyi ba, saide ki gwada amma manyan masu bada magani ma sunyi sun gaji, kawai de kada naki kuma ya zama na raina basiranki na amince ki gwada"
murmushi tayi tace "na gode sosai mai martaba kuma insha Allah za'a dace"
yace "ba komai"
komawa ciki yayi, ya kalli ammi data zuba mishi ido ya faɗa mata duk abinda ya faru tace "kana ganin zata iya? babu fa inda ba'a shiga ba a ganina ta bari kawai bama bukata..."
ya kaseem yace "meyasa zakice bama bukata bacin kin san babu wanda baya bukatan ganin yarima ya samu lafiya? ko dai bakyaso ya fara magana ne?"
Aneeta tace "nima a ganina bai kamata a bari wannan kazamar ƴar kauyen ta bawa yarima magani ba, watakila neman gindin zama kawai take a gidannan"
yace "kamar yadda kika nemi gindin zama?"
shiru tayi yace "wai meyasa bakwaso ya fara magana ne? ko dai akwai abinda kuke ɓoyewa ne?"
hanunshi hameed ya rike yana girgiza mishi kai alaman yayi shiru dan Allah, shiru yayi, sallama Asmeeta tayi sannan ta shigo da kwarya a hanunta, murmushi ta yiwa ya kaseem daya bata wajen zama, hanun hameed ya rike yace "muje"
a kujeran falo suka zauna, ta gama haɗa maganin ta mika mishi tace kayi bismilla kasha"
ganin hararanta da yakeyi itama ta watsa mishi harara harda murguɗa baki tsaban haushin da yake bata sai shegen girman kai gashi ba lafiya ne dashi kamar mutane ba, ya kaseem yana kallonsu a ranshi yace "yarinyar tanada yaranta dayawa"
karɓa yayi yana yamutsa fuska ya fara sha, ganin zai sauke tace "karka kuskura ka sauke dan saika shanye duka"
wani kallon harara daya aika mata itama ta rama, murmushi ya kaseem yayi shanyewa yayi ya sauke kwaryan ɗaci sosai yaji, ta taɓe baki tace "anjima da dare ma sha zaka kara kuma zaifi haka ɗaci"
duk hararan da yake mata ramawa take ta ɗauki kwaryan ta fita, bayanta yabi da harara badan ya kaseem ba da saiya kifa mata mari dan yarinyar batada kunya.
da dare suna zaune suna dinner ta shigo da kwaryan a gabanshi ta tsaya ganin shi baya cin abincin kallo yake, hararan daya bita dashi yasa tace "ko cire idonka zakayi a kaina sai kasha wannan maganin nifa ba dan kai nake wannan taimakon ba ni ba son ganinka na nake ba inayi ne sabida Allah dan kai da ganinka idan kana magana zaka rinƙa gayawa mutane maganganu marasa daɗi"
tana magana tana haɗa maganin kallonta yake har ta gama ta mika mishi kin karɓa yayi, tace "gara ka karɓa dan ni ban damu kai ɗan sarki bane babu abinda ya shafeni"
ya kaseem yazo kawai ya karɓa domin yaji komai data faɗa, sunkuyar da kai tayi tana matukar jin kunyan ya kaseem sosai, sa mishi yayi a baki karɓa yayi badan yaso ba ya fara sha, tashi tayi tace "sai kuma gobe da sassafe kuma sai yafi wannan ɗaci"
ɗakin meenat taje tana kwance akan gado hanunta akan cikinta tana shafawa, murmushi tayi a ranta tace "Allah yasa ta fara son cikin kamar yadda nake so kuma kamar yadda nasan hamma najeeb zai so"
ta ɗan russuna tace "akwai abinda kike bukata?"
ta girgiza kai, murmushi tayi ta juya zata fita sai kuma ta juyo tace "mangoro, agwaluma, tsamiyan biri, ɗata, muruci, gwaiva, duk babu wanda kikeso?"
a hankali ta lumshe ido ta buɗe cikin sanyin murya tace "mangoro"
cikin jin daɗi tace "to bara na kawo miki"
da mamaki take binta da kallo har ta fita, cikin jin daɗi ta fita ta aika driver ya siyo mangoro yana dawowa ta karɓa da sauri ta koma ciki, wankewa tayi ta yayyanka mata sannan ta koma ɗakin, tace "gashi"
karɓa tayi tace "na gode"
tsayawa tayi tana kallonta tana sha, tasha dayawa sannan ta kalleta yadda take kallonta tana murmushi tace "lafiya?"
da sauri tace "lafiya ƙalau ba komai babu abinda kike buƙata?"
ta girgiza kai, fita zatayi alameen ya shigo da sallama, ji tayi kamar ta bigeshi dan haushi, yace "sannunki"
cikin ɓata rai tace "yawwa"
shiga ciki yayi, meenat tana ganinshi ta tashi ta rungumeshi kawai ta fashe da kuka, yace "shiiii ki daina kuka"
shafa bayanta yake a hankali, tace "ya alameen ina sanka banason abinda zai rabani da kai, banaso ina sanka sosai ya alameen"
yace "stop crying mana baby kinaso zuciyata ta buga ne? banason kina kuka nasan halinki ƙaddara ne ya faɗa kanki kuma inaso ki sani babu abinda zai rabani dake a wannan duniyan har yanzu ina sanki a yadda kike meenat"
zatayi magana yace "shiii kar kice komai"
a hankali Asmee cikin karaya ta buɗe kofan ta fita, duk damuwan duniya ya taru ya mata yawa.
da sassafe yau ta tashi yaune kwana na biyar da zata bashi maganin safe rana dare take bashi, addu'a take Allah yasa maganin yayi aiki, jikinta a mace ta fita zuwa yanzu idan ya ganta ɓata ranshi yake kamar yaga mutuwa sabida ɗacin maganin da take bashi, shigowa tayi ɗakin da sallama itama ta ɓata rai kamar yadda shima ya ɓata, bashi tayi tace "yau idan kasha ko kayi sauki ko kar kayi ni Asmeeta na gaji da kawo maka magani, nifa gani ma nake rashin magana halinka ne ba lalura ba, domin tsaban girman kai ne nakega yake hanaka magana"
wani kallon tsana da yake aika mata tace "duk tsanan da kamin bai kai wanda nayi maka ba bari na faɗa maka kaji"
bashi maganin tayi, ya ɗauke kai bai kara kallonta ba, tace "ka karɓa"
wannan yarinyar tanada fitsara shiyasa baya sonta sannan ga raini gani take kamar tana taimaka mishi, tace "shikenan tunda ba zaka sha ba bara naje na kira ya kaseem yazo ya baka da kanshi"
tafiya zatayi ya rike bakin zaninta, jiyowa tayi da murmushin rainin hankali tace "oho ashe zaka sha"
karɓa yayi ya rufe ido ya shanye, wurgar da kwaryan yayi, ta taɓe karamin bakinta tace "ba dai kasha ba?"
ɗauka tayi ta fara tafiya, buɗe kofan tayi zata fita kamar daga sama taji muryanshi yana crack yace "As...As...As"
juyowa tayi tana kallonshi domin tabbatar da shine yayi maganan ko bashi ba?
taga yana rike wuya cikin azaba yana kallonta idanunshi sunyi jajur, wurgar da kwaryan tayi tazo da gudu tace "ka karasa"
yana kallonta yana hawayen azaba yace "A..A...A"
hannayenshi ta rike ta durkusa a kasa gabanshi tana kallonshi tace "eh ka karasa yarima"
yace "As....meeta"
tsalle ta daka cikin jin daɗi tayi wani irin juyi kamar yarinya ƴar shekara biya da aka yiwa kyautan teddy, ta saba a duk lokacin da hamma najeeb yasa ta bada magani idan an samu dacewa sai tayi tsallen jin daɗi, tsalle ta fara da ido yake binta yana jin wani abu yana sukan zuciyarshi, cikin dariyanta me masifan kyau tace "ka fara magana yarima?"
shiru yayi ya kasa amsa mata, farin cikin da take ciki yafi komai bashi mamaki da kuma birgeshi, ita kuma wannan murnan normal ne a wajenta idan ta bada magani an dace.
_Jiddah Ce..
 08144818849