ANA BARIN HALAL..: Fita 13
ANA BARIN HALAL..:
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
*PAGE* 13
Kullum zuba ido nake naga farare sun zo gidan mu idan Yayah Ahmad yazo amma shiru kakeji, a haka aka kawo kayan auren habiba, domin Abba yace december tare da na yaya Ahmad za'ayi, saboda haka ita mamie tana ta shirye-shiryen ta da ƴan uwanta, don ta ɗaga hankali wa Abba dayace suje su sayi kayi kaya ita da mamah da ummin, amma fir taƙi yadda, shima ya dage bazataje ita ɗaya ba, sai da Aunty Rakiya ta saka baki tukun Abba ya bar mata, amma duk da haka komai na kayan ɗaki da parlor da su electronic Abba ya bawa Aunty Rakiya ta mishi, kayan kitchen da su kayan zaƙi kawai Abba ya bar wa mamie, koda yake Yayah mohd ne ya sayi set na gado duka biyun, da set na kujeru, yayah Ahmad Abba yace ya haƙura yayi hidiman haɗa kayan nashi auren, amma duk da haka sai da ya sayi deepfreazer, T.V da gascooker, Aunty Rakiya kuma ta sayi cottons na gidan gaba ɗaya, Abba dai kayan kitchen da tarkacen kayan zaƙi ya bayan don ko gara Aunty asma'u ne tace a bari zata aiko, bawai don ƙarfin Abba ya gaza bane, no kawai zumunci da ake da shi ne da kuma ƙoƙarin Abba wa kowa a zuriyan.
*Aunty nice* zakiyi mamaki idan nace miki jammy taƙi yadda suyi magana da habiba? Duk yadda habiba taso irin su haɗa kai da jammy abun ya gagara, nima maryam ke bani labarin abun da yake faruwa, ashe haɗa kayan ma mummy ne ta haɗo shiyasa mukayi mamakin ganin kayan, don a matsayin gidan su ba haka mukayi zaton gani ba, sai bakin mamie ya rufu ruff, baka jin wannan rawan kan, sai dai gori da zagin wata bata da farin jini wato ni, wlh ko ajikina, nidai damuwa na yadda habiba taƙi yadda mu tsaran yadda bikin zai tafi, don na rutsata a side ɗin hajiya ummah duk yadda naso ta bani haɗin kai mu maida komai ba komai ba, amma taƙi, sai wani nonnoƙewa ta keyi, ganin bazata bani haɗin kai ba sai na rabu da ita, don ko magana na mata bazata amsa mun yadda ya kamata ba, sai dai tayi murmushi tayi shiru, zuwa wani lokaci kuma sai ta fara share hawaye, ganin haka sai na fara rabuwa da ita, sai dai ina jinta suna waya da ƴan'uwanta na wurin mamin ta, kuma ina jin yadda suke magana akan hidiman bikin, a lokacin naji wai har sun fitar da ashobe.
Washe gari aka kai kayan auren yaya Ahmad, maryam ta shigo gidan mu bayan mun dawo akaiwan, gidan su yarinyar gidan tantsan ƴan boko ne, domin itama ƴar bokon ne, babu ƙaryah ƴan gidansu sun haɗu, hira muka ɓarke ni da maryam, anan ta keta bani labarin yadda mummy take nuna bata son auren Aliyu da habiba, kuma ko a gaban kowa tana kushe auren, jamilah ma ko maganan auren bata son a mata hiran, "chan ta matse musu", na faɗa ina tura baki gaba, a nan na bata labarin yadda mukayi da habiba, zagina maryam ta fara kaman ita ta haifeni, wai bani da zuciya tun da anguje ni da abu na haƙura mana, tagumi nayi na ƙura mata ido har taga ma ban baminta sannan nace, "besty bazaki gane bane, idan na ƙi shiga cikin hidimanta za'ace ko ina kishi ne ko ina mata baƙin cikin samun miji don ni ban samu ba",
Harara na maryam tayi sannan ta ɗaura da tambayan, "dama ita ta samo mijin ko ke kika sama mata, nike meyasa halinki na sokaye ne kam besty? Tou a hirr ɗinki na ganki cikin hidimanta, idan ita tayi niyyah ta nemeki fine, idan bata nemeki ba mu cigaba da hidiman na Yaya Ahmad", muna cikin hiran hafsy ta shigo tana wani ƙyalƙyala dariyan mugunta, har ƙasa ta tsugunawa tana tashi, kallo muka bita da shi, maryam na tambayanta meyake faruwa? Sai da tagama dariyan tukun ta bamu labarin dambatuwan da akeyi acikin gida yanxu, ashe mamie ne ta ɗagawa Abba hankali akan kayan yayah Ahmad, wai wannan kayan ba kuɗin yayah Ahmad bane ya haɗa kayan, dole Abbah ya dafa mishi, tunda hakane kuma dole ya bayar ta sake haɗawa habiba kaya, don na habiba basu da wani quality, shi kuma Abba yace mata bata isa ba, shidai yayi niyyan haɗa mata akwati ɗaya na kayan fitan biki yadda yayiwa Adda lokacin aurenta, daga nan ya ƙira Aunty Rakiya ya gaya mata yadda sukayi,shine fah Aunty Rakiya tazo ta sameta ta watseta, ke kam mamie sai kuka wai ana mata baƙin ciki don anga habiba ta samu miji ke baki samu ba, Aunty Rakiya ta zage ta tas tace wani mijin da sukayi ƙwace? Da ƙyar ummie taje ta kashe maganan, nidai banda dariya babu abinda nakeyi, Adda idan kukaga idon raliya dole kuyi dariya, hafsy ta sake tuntsurewa da dariya maryam na tayata, ni dai banji dariya ba sai wani abu daya tokare ni a zuciyata, wai ni nawa nake nema da mamie ke goranta mun rashin aure? Yaushe ma habiban tayi da za'a fara goranta mun?
Babu wuya wurin ubangiji, cikin satin nan aka fara hidiman auren su Yayah Ahmad da na habiba, gidan mu ya cika da dangin ummie da mamie, sannan kuma ga dangin Abban mu da suka zo, side ɗin su yayah Ahmad ma cike yake da friends ɗinsu, domin yayah umar ya kwashe nashi ya nashi sun koma gidan Aunty Rakiya shida yayah ishaq, sai suka mayar da gidan kaman majalisan angwaye, babu abun da kike gani sai shigan motoci da fitar su, gashi ummie tana wadata su da lafiyayyun abinci da kayan shaye-shaye kala da kala, hankali kwance suke hidiman su, yau ne gidan su amaryan suke liyafa thursday, habiba kuma kaman gobe friday naji hafsy tace za'ayi nata liyafan a farfajiyar gidan mu, wanda ita kuma zatayi ƙauyawa a gidan wan mamanta da yake gida dubu, kuma har lokacin bata ce mana komai ba, duk da ummie tace naje na shiga cikin ƙawayenta ko bazata kula ni ba, amma firr maman su maryam tace haka bazai faru ba, idan wani abu ya faru cewa za'ayi daga garemu ne, magani shi kawai kar a fara.
Wuraren 5:00pm mun gama shiryawan mu tsaf cikin wani arnen lace da yayah mohd ya ɗinka mana mu uku har da raliya, kowa da kalan nata amma zanen su ɗaya, nawa purple anyi mun gown mai lafiyan kyau, gaban an jera bakin lace ɗin tunda ga sama har ƙasa an kuma shiryashi da adon stones masu hasken gaske, dama tun wurin azahar muka dawo daga gidan lalle, dayake Allah ya mana baiwar hasken fata zokiga yadda lallen yayi mana kyaun gaske, ranan laraba yayah umar suka kaimu saloon aka mana gyaran kai har da maryam da ummitah sister ta, yau kuma suka kaimu gidan lalle, nidai mamakin yayah ishaq nakeyi yadda yake ta wani kaffah-kaffah da hafsy, lace ɗin hafsy Red ne, don ita mayyar red abu ne, ita kuma raliya green, amma ban san ko yau zata saka nata ba, don ita ma ɗauke mana wuta tayi, garama mutumiyarta hafsy idan sun haɗu sukan ɗan taɓa hali, kuma dai su basu daina kula juna ba, saidai suyi faɗan kuma suyi hiransu, don komai sai ta bawa hafsy labari, amma yanzu sai naga wani ƙawance na musamman ya shiga tsakanin hafsy da ummitah ƙanwar maryam, don da tsabar kowa danata halin masifan basu zama inuwa ɗaya, daga baya ma tun suna primary ummitah ta koma lagos hannun sister mamansu data girma a gidan, tana aure ta tafi da ummitah sai ta bar anguwan mu, yanzu kuma Auntyn su sun koma spain da mijinta sai maman su tace ummitah ta dawo saboda bata son girman ta achan, tou sai suka ƙulle da hafsy kuma abun ya mun daɗi, saboda ummitah ƴar gayun gaske ne, wanda na lura yanzu hafsy ma tafara koyi da ita, muna shiryawa nida fatiman Aunty Bintu da maryam a side ɗin hjy ummah fatima sai kwashewa da dariyan mu takeyi, nima dai dariyan na fara ina cewa, "wallahi fatima ni a sokanci na ae da binsu zanyi goɗai-goɗai, da badan Aunty Bintu ta tunatar da mu ba ae sokayen yayu za'ayi masu bin ƙanne da masoyan su", dariya dukkan mu uku muka kwashe da shi.
"*Aunty nice* nifah ban lura akwai wata alaman ƙwollaliya ba tsakanin yayah ishaq da hafsy, yayah umar da ummitah ba, sai da Aunty Bintu tace idan mun shiryah sai mutafi wurin event ɗin tare, ta taho da motan ta, aiko nace mata dasu yayah umar zamu tafi, nan take zayyana mana abun da ta lura yake tsakanin su, tana dariya tace ko wasu irin yayun kawai ne zaku na bin yara goɗai- goɗai da masoyan su"? Dukkan mu dariya mukayi, wato sun raina mana hankali mune ƴan rakiya ko?
Mun fito haraban gidan mu uku muna jiran fitowan Aunty Bintu da ta tsaya suna magana da ummi, hannu na riƙe da Areefh wanda yayi wayo don ya kusa 4month koma ya cika yayi ɓul-ɓul, kaman nin shi da yayah mohd da yayah Ahmad dani ya fito sosai, wani ma idan bai san Baban shi ba zai ce nina haife shi, Allah sarki gashi har irin haƙurin mu ya ɗauko, muna tsaye jikin motan muna jiran Aunty Bintu sai ga su Yayah Ahmad da abokan shi sun fito a side ɗin shi suna wucewa wurin motocin su, muryan yayah Ahmad naji ya ƙirani, juyawan da zanyi kawai sai nayi ido biyu da fararen nan sun sha wani milk colour ɗin filtex, da sauri na ƙarasa wurin yaya Ahmad da yake tsaye yana ɗaura agogon shi, miƙo hannu yayi ya karɓi Areefh yana tambaya na dawa zamu je wurin event ɗin, yana tambayan idon shi yana kan Areefh, murya ƙasa-ƙasa kaman bana so wani yaji nace mishi, "da Aunty bintu zamu tafi" miƙo hannu yayi ya karɓi handbag ɗina, hannu yasaka a aljihun shi ya ciro kuɗi bunch guda ƴan 100 ya saka mun a ciki, idon shi akaina yace "wannan na liƙi ne, ina hafsy kuma"? Ya tamabaya yana duba cikin compound ɗin gida, a hankal nace "sun fita tare dasu yayah umar" sannan na mishi godiya sosai, kawai sai ganin M.G ya matso kusa da mu fuskan shi da murmushi ya miƙa hannu ya karɓi Areefh, idon shi akaina yace, "ƙanwar mu mai kyau wannan babyn kaman ki da shi yayi yawa, ba lallai ki haifi ɗa mai kama da shi ba gaskiya, ɗan wurin Yayan mohd ne"? Ya tambaya gaba ɗaya hankalinshi yana kan Areefh, gaishe shi nayi fuskana cike da murmushi, lokacin Aunty Bintu ta fito, ganin ta fito na ƙara yiwa yayah Ahmad na miƙa hannu zan karɓi Areefh yaro kawai ya wani juya yaƙi zuwa, kuma ban taɓa ganin yayi ƙiwuya ba, dariya M.G yayi yace, "kai yaron nan ya burgeni, kinga shima baya so ki tafi M.G ya daina ganin lallen ki mai kyau ɗin nan," kunya maganan shi ta sakani nayi saurin ɗan yin baya kaɗan ina ɓoye hannu ni fuskana ɗauke da murmushi,
"don Allah kazo muje mana kana ɓata wa mutane lokaci fah", muryan A.G naji yana yiwa M.G magana, ɗago kai nayi da sauri na sauƙe akan shi, shima kuma alokacin gaba ɗaya idon shi yana kaina, saidai babu fara'a ko kaɗan akan fuskan shi, da sauri na juya fuskana na mayar kan M.G da yake miƙo mun Areefh murya ƙasa-ƙasa yace, "karɓi yaron kafin wannan masifaffen yayi yaga-yaga da ni", ina karɓan Areefh ya ɗaura mun wani bounch ɗin ƴan 100 ɗin akan Areefh ɗin, yana cewa "wannan ki ƙara na liƙin ko",
Da sauri nace, "a'a don Allah ka bari yaya Ahmad ya bani".
Cikin tsawa-tsawa kaɗan A.G ya sake cewa, "shi Ahmad ɗin ne yace miki mu ba yayunki bane? Ko kuma idan mun baki abu kada ki karɓa"? Murmushi M.G yayi ya juya suka tafi bai sake cewa komai ba, nima juyawa nayi wurin su Aunty Bintu don mu wuce.
*Aunty nice*
managarciya