ANA BARIN HALAL..:Fita Ta 31

ANA BARIN HALAL..:Fita Ta 31

ANA BARIN HALAL..:Fita Ta 31

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* 

*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin Ƙarfe. Burin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*

Idan kana/kina sha’awar:

_**Updates akan tallafin gwamnati (Grant & Loan)._

_**Hanyoyin samun kuɗi ta kasuwanci na online._

_**Sana’ar hannu da za ki iya yi daga gida._

_**Dabarun amfani da waya wajen samun kuɗi._

_To wannan group ɗin na Business/Grant/Loan naku ne! Zaku samu labarai kai tsaye + shawarwari masu amfani in sha Allah._
*Join yanzu don kada ku rasa sabbin damarmaki*
https://chat.whatsapp.com/C64wC3IDhW6FtwjSpWWDiL?mode=ac_t

*Page 31*

*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE  ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559


*********
Yana ɗauka kawai naji yace "mukhtar kai kuma yayah akayi ka kyautar da wurinka wa mace? Ina laifin cikin mu ko ni ko shehu ae sai ka bayar wa ɗaya daga ciki, yanzu fah kaman wa mijinta ma kabayar domin gaba ƴaƴanta ne zasu gaje wurin kaga ya koma na mijinta, kawai kace mata ka fasa, idan yaso sai ka bani ko kabawa shehu".
 "a'a yayah baza ayi haka ba, kaga fah ita umatiti ƴar'uwar muce, kuma itama tana cikin rashin wurin zama, kawai ayi haƙuri da hakan idan muna tare kowa ma zai mallaki nashi, fatan dai Allah ya jiƙan Babah da rahma",   ina jin da ƙyar ya amsa Ameen ɗin, don ba haka yaso ba, kuma babu yadda ya iya dani, tunda gida dai nawa ne, koda goggo taji yadda mukayi da ƴan'uwa na daɗi taji, don ko ita abunda tace kenan, sun raba tsakanina da mahaifina akan gado ne, tou suje gado baya gaban mu, fatan mu kowa Allah ya bashi nashi.

***********
Haka rayuwa tayi taja damu har suka fita Takaba, bayan nan kaɗan umatiti suka fitar da ƙofan da zai shigar da su gidan, kuma wurin yayi kyau, suka tare a ciki, iyaye mata kowa side ɗinta ya fito a gadonta, sannan duka cikin gidan da wani babban fili inda ɗakunan masu aiki da kitchen na waje yake, da wurin packing mota duk gadon su tijjani ne, suma anware wa kowa nashi, babu wuya wurin ubangiji komai namu yayi ta tafiya yadda Allah ya so har muka zo kowa ya samu abunyi,  shi A.G barrister ne, yana aikin shi anan Abuja office ɗinsu ɗaya da Ahmad, sannan akwai wani chamber da suke zuwa chan tare, ni dai Contractor ne, kuma ina ɗan taɓa ƙananun business na fita da abu waje, kaman china, sai kuma na shigo da nasu, Abuja kuma mun sayi gida a wuri ɗaya nida A.G, domin plan ɗinmu kenan, yanzu haka kowa jiran abokiyar zama yakeyi, duk da dai shi A.G ya samu, nine dai nake laluɓe",     ya ƙarasa maganan murmushi ɗauke da fuskan shi, sannan idon shi kuma zube a kaina, ganin haka sai na maida kallona ƙasa,   "kinji taƙaitaccen labarin *MUKHTAR GARBA* Da ɗan'uwan shi *ALIYU GARBA INUWA* Kinji irin abotan da yake tsakanin mu, da amintan da yake tsakanin mu ko, kinji irin rayuwar dana sha a rayuwata mai daɗi da marar daɗi, kinji irin hidima da kyautatawan da A.G da iyayen shi har da kakanun shi sukayi a rayuwata dana ƴan'uwa na har dana yayye na,? Dalilin baki tarihina da labarin rayuwar mu abu ɗaya ne, a tunaninki akwai wani abu wanda bai kaucewa addini na da shari'a ba da A.G zai so naƙi mishi? A tunani na da ana kyautan rayuwa A.G ya chanchanci na mishi, A.G sun inganta rayuwa ta batare da sun goranta mun ko a wasa ba, A.G ya mayar da iyayen shi nawa, ƴan'uwan shi nawa,  mahaifiyar shi ta haɗa ƴar ta aure da yayah na ba tare da shi ya nema ba saboda ta ƙullah dangantaka mai ƙarfi a tsakanin mu, akwai abunda bazan iya yiwa A.G ba don ya samu farin ciki a rayuwan nan ba"?

 Girgiza kai kawai nakeyi ina kallon shi cike da tausayawa, a haka na sake tsinkayo muryan shi ya cigaba da cewa,  "shawaran da nake so muyi da ke, kina ga yakamata na nemi auren ƴar'uwar shi *HEEDAYAH*"?


Wani irin mummunan faɗuwan gaba naji yazo mun, har wani rawa naji zuciyata ta nayi, buɗe bakina nayi kaman zanyi magana, amma sai naji yaƙi buɗewa, tsoro da firgici naji sun sauƙa mun a lokaci ɗaya,  "dama M.G ba sona yakeyi ba? dama duk shirme zuciyata take ƙulla mun? Kasa ɗago kaina nayi na dube shi, shiru wurin ya ɗauka na wani lokaci,  chan ya buɗe baki zaiyi magana, kawai naji kaman an zaburar dani,  naji bakina yana furta   "Har zuciyar ka kaji kana sonta ko kuma kawai don ka faranta mishi ne"?

Ido ya zuba mun kaman yana nazari, chan kuma sai naji ya sauƙe ajiyar zuciya a hankali ya fara magana,  "Ayshaa tun ranan da na fara ganinki naji nasamu matar da nake so, matar da rayuwarta, tsarinta, tarbiyanta, komai nata ma ya mun, Allah - Allah nakeyi mu koma gida nayi shawara da A.G,  amma kin san meya faru"?
 Ɗago idanuna nayi na zuba mishi su,  murmushi yayi mai alaman ciwo a zuciya yace,  "muna shiga parlon mu  A.G ya kallo ni fuskan shi cike da fara'an da idan bani ba da dama basu san yana da ita ba yace,   "aboki ina ga nakusa aure",   zaro ido nayi cike da firgici nace,   "ka samu wacce ta maka kenan",?
Duk jikina yana ɗan rawa ta ciki, murmushi yayi ya wuce ya buɗe fridge ya ɗauko bottle ɗin ruwa ya kafa bakin shi yasha mai yawa, sannan ya juyo har inda nake ya saka hannu ya bugi ƙirjina yace,   "matsalan tayi yarinya, kuma bansan  yaya zanyi na tunkareta ba, ban san me zance mata ba",   ya ƙarasa faɗi yana wuce kan kujerun parlon ya zauna fuskan shi da murmushi,    " komai nata yayi mun, ina yawan mafarkinta, ina yawan ganinta a irin yanayin dana ganta yau, sister barrister ta mun, aboki ta mun, amma bansan yayah zanyi ba, sai ta ƙara girma"
Kinji abun da yace mun.
Da sauri na kalle shi raina duk a dagule nace,  "kasan ko habiba yake nufi, kuma gashi tayi aure, sai dai idan yana son cousin ɗin mu, hadiza ko zainab?"  na faɗa kaman babu nutsuwa a tare da ni,  murmushi yayi ya ƙura mun ido,  "kece yake nufi Ayshaa, duk yadda A.G yake gwada miki zakice baki fahimta ba? A.G fah har ciwo yayi saboda zaiyi nesa da ke, da tare zamu tafi karatun amma yayi cancel nawa, yana tsoron kada muyi nesa da ke wani yayi wuff da ke, idan ya dawo ina tunanin zan je nayi nawa, ko kuma ma tachan-tachan kawai na haƙura"   ya faɗa yana murmushi,  "nidai ban fahimci nashi ba, naka kawai na fahimta",  na faɗa ba tare da na so hakan ya fita daga bakina ba,  a razane dukkan mu muka ɗago kai muka kalli juna, ni nayi saurin kai hannu na bakina na rufe, shi kuma ya zaro ido yace,   "Ayshaa son da nake miki yana bayyana kan shi ne? Bayan ke akwai wanda suka fahimci hakan?"   ya faɗa gaba ɗaya a firgice.


Hawaye naji yazo mun nasaka hannu na da sauri na shareshi,   "kasan kana so na tou meye hujjan ka naƙi bayyana mun? Meye hujjan ka na takurawa kanka da son auren heedayah? Meye hujjanka M.G?"  na faɗa ina jin wani firgici a zuciyata.
"Duk abubuwan da nagaya miki A.G dafamilyn shi sun mana bai kai na bar abunda nake so don farin cikin A.G ba?"  harara na aika mishi nace,  "har a zuciyarka ban kai kayi fito na fito da kowa ba kenan?"
Murmushi yayi yana duba na yace,  "ban taɓa ganin wata a rayuwa naji ina sonta ba sai akan ki, kuma ɗari bisa ɗari kin mun a matsayin matar aure na, haka A.G ko a wasa ban taɓa jin yayi maganar zaiyi aure ba sai ranan da ya ganki, kuma nayi imani da Allah son da nake miki bai kai wanda A.G yake miki ba, zan iya haƙura da komai a rayuwa idan A.G yana so, ae ba karya ba malam bahaushe yace,    *ANA BARIN HALAL..... (DON KUNYA)* Ayshaa ae da kunya A.G ya nuna mun ga abunda yake so ni kuma nace nima shi nake so,  A.G baya son magana amma akanki yana jure yayi, duk dare idan zamu kwanta zai takurani na bashi labarinki, wanda har na fara ƙure labarin, farin ciki yake shiga idan yaji sunan ki ko wani abu da ya shafeki, nikan ki taimaka ki bani haɗin kai A.G ya samu farin ciki".
Ajiyan zuciya na sauƙe mai ɗan ƙarfi na miƙe tsaye, shima miƙewan yayi yana "yayah naga kaman tafiya zakiyi"? "ehh hakan yafi, don naga baka son farin cikina dana ka, kawai A.G shine damuwanka, baka tunanin kai ma ka auri abun da kake so"?
Matsowa yayi kusa dani sannan yace,  "zan iya son sister A.G, saboda son da nake mishi?"   "ni kuma saboda me zan iya son A.G"?
Ɗago manyan idanun shi yayi ya zuba mun so, "saboda ni da farin cikina zaki so A.G".
Ido muka ƙurawa juna har na tsawon lokaci, a raunane naji muryan M.G yace,   "ki taimaka mun na ɓoye sonki da nakeyi ayshaa, ki taimaka mun na sakawa A.G da alkhairin shi gareni, bana so kowa ya taɓa sanin na soki,  banso zuciyana ya fallasa kanshi a gareki ba, har na fara tsoron kada A.G ya fahimta, ko barrister, kinsan yayanki ma yasan irin son da A.G yake miki, hattah mummyn shi ta sani, don muna hiran da ita sosai, ballantana lokacin da yafara ciwo akan tunanin barinki, don Allah kimun wannan alfarman Ayshaa",  yana faɗa ya ɗaga hannayen shi duka biyu yana roƙo na,  jikina naji gaba ɗaya yayi sanyi, ido na zuba mishi a hankali nace,  "ni dai bam maka alƙawarin zan so shi ba, kuma na maka alƙawarin babu wanda zai san ni ko kai wani yataɓa son wani, amma ni bazan so shi ba, ɗaya kenan, kaima kuma ban amince ka nemi ƴar'uwar shi ba, kajira lokacin da Allah zai haɗaka da wacce kake jin sonta sai ka aura, nima zan jira wanda zai mun na aura", ina faɗa na juya nayi ciki, zuciyata kaman zatayi bindiga ta fashe, zama nayi na zabga wani uban tagumi na faɗa duniyar tunani, ina haka har naji an fara ƙiran sallan magrib,  da ƙarfi na furta,      "nidai A.G bana sonka, tunda M.G yaji baya sona ya haƙura ? Tou nima na haƙura da kowa zan jira wani daban?"  na faɗa idona yana cikowa da hawayw, jin tahowar Aunty J yasaka ni tashi na shige toilet nayi alwalah, har akayi Esha'i ina zaune akan sallayata, bayan na idar na miƙe na ninke abum sallan na chanja kayana, don wankan ma bana jin zanyi, dama tun shigowara na kashe wayata, sai a lokacin na kunnata, ummie na ce ta ƙiran, bayan mun gaisa ta tambayeni yau shiru, murmushi nayi bance komai ba, sai hafsy ta karɓi wayan, bayan mun gaisa take bani labarin, yau ma habiba a gida ta kwana, wai sun sake wani faɗan da Aliyu, wai ta raina mishi ƴan'uwa da iyaye, bata son zuwa ta gaishe su, haka dai abubbuwa babu daɗi wallahi, jikina a sanyaye mukayi sallama, ko whtsapp ban hauba na kwanta nayi shiru ina tnanin rayuwa.


Duk yadda M.G yaso muyi wani magana naƙi bashi dama, domim haushin shi naji ya kamani, shirin komawa na bauchi kawai nakeyi, ranan da zan tafi tun wurin ƙarfe biyu M.G ya kawo mun wani jaka cike ɗa abayu kala-kala masu shegen kyau kusan kala biyar, sai takalma da jaka guda biyu, da wani agogo mai kyaun gaske, sai wasu turare kusan kala uku da body misk, text na mishi ni bazan zoba, kuma kada ya bari yayah ya gane, babu yadda ya iya ya bawa yayah Ahmad ya shigo da shi, sai da yakawo ne yake ce mun wai mummyn suce ta aiko mun, wai duk tsara bane, duk kyaun da suka mun sai naji raina ya ɓaci, domin nasan saboda A.G ta kawo,  amma haka na shirya kayana wurin biyar na yammah jirgin mu ya sauƙa a garin bauchi,  yayah umar ne da yayah ishaq suka ɗauko ni,  murna ummie da hafsy sukayi na dawowa na, ranan kusan raba dare mukayi muna ta hira.


Duk yadda nayi sai da M.G ya shawo kaina muka cigaba da gaiswa ta waya, amma naƙi muyi hiran A.G da shi, haka shima babu wani hira na soyayyah da yake haɗa mu da shi, sai dai muyi labari kawai na ratuwa, ko na school ɗin mu, a haka Yayah Ahmad ya sayi ticket hafsy ta tafi Abuja.

Sorry nayi mistake a baya akan Fatima ta fara ATBU, taso farawa har yaya yasama mata admission Through yayan M.G Hassan da yake lecturing a ATBU, amma sai Yayanta yace ta dawo unimaid kawai, haka bata so ba ta tafi, muma mun cigaba da zuwa school nida Maryam.
A wannan karon kuma aka saka ranan auren fatima da kabir, domin yazo nigeria, sannan aka saka na maryam ma da Dr, duk dai tsakanin bazai wuce 2month ba.

*AUNTY NICE*