Abin Da Babba Ya Hango:'Kai Kanka Kasan Da Inason Sa Allah Ba Yadda Za'a Yi Na Tsaya Saurarenka'
RUBUTAWA; DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM
Waya ce a hannunta sai faman sarrafa ta take yi, gabanta kuwa kayan marmari ne sai faman cika baki take yi da su tana sarrafa wayar hannunta.
Shigowarsa ɗakin ne ya sanya fuskanta canjawa daga yanayin da take ciki zuwa wani launin daban, jikinsa na rawa ya ƙarasa gurinta yana mai faman washe baki, ita kuwa sai ƙara ɗaure fuska take yi haɗi da ɗauke kai daga wurin da yake zuwa wani sashen.
"Dan Allah hubby ki yi haƙuri indan kuɗin da ki ka yi magana ne insha Allahu yau zuwa gobe zan nemo su na baki."
Ƙara ɗaure fuska ta yi sannan cikin ƙasaita ta ce "Okey, za ka iya riƙe duk waɗansu zantuka naka har lokacin da ka zo da kuɗin, kai kullum aka yi ma maganar kuɗi ka iya faɗan babu-babu, kuɗin da shi uban naka ya mutu ya barma fa?, albashin da kake ƙarɓa me kake yi dashi ne?."
Cije leɓensa bakinsa ya yi cike da jin ɗacin furucin ta a gare sa , sai dai ba damar maganar dan ya san ko maganar ya yi wata magana ce za ta ƙara caɓa masa.
Jikinsa a sanyaye ya ƙara kai kallonsa kanta, har ya buɗe baki da niyar yin magana ta yi azamar ɗaga masa hannu sannan ta miƙe hannunta riƙe da tanfatsetsiyar wayarta ta nufi hanyar ficewa daga ɗakin ba tare da ta ba shi izinin yin maganar da yayi niyar yi ba.
Zama ya yi a wurin da ta tashi sannan ya sanya hannunsa na dama ya dafe kansa, lokaci ɗaya yana mai jin kamar ya kurma ihu sai dai ba damar hakan a gare shi.
Miƙewa shi ma ya yi jikinsa a saɓule ya fice daga cikin ɗakin.
A harabar gidan ya same ta zaune a gurin shuke-shuken gidan , an yi sa ne domin shaƙatawa, sai amsa waya take yi, tana faman ɗaure fuska.
Wurin da take ya nufa yana mai addu'ar Allah ya sa ta kula shi a wannan lokacin, sai dai kafin ya isa wurin ta yi azamar miƙewa ta nufi hanyar shiga sashen nata.
Jikinsa a sanyaye ya juya yana mai fito da makulli daga cikin aljihunsa.
Tunkan ya isa gurin da motaci ke ajiye, wata haɗaɗɗiyar mota baƙa dake ajiye a cikin jerin motacin da aƙalla za su kai shida, murfin motar ya buɗe, yana isa gurin ya yi azamar faɗawa cikin motar ya yi mata key.
Mai gadi ne ya yi azamar wangale gate ɗin ganin yadda uban gidan nasa ya janyo motar.
Tafiya ya ke yi amman shi kansa bai san inda ya dosa ba, parking ya yi a gefen titi yana me dukan sitiyarin motar da hannunsa, kana ya kwantar da kansa jikin sitiyarin yana me busar da iskar daya tara cikin bakinsa.
Ya jima a gurin yana me saƙawa da warware wa, sai dai har tsawon 20minutes ya rasa wacce hanya zaibi a wannan lokacin domin ya samowa ZULFA'U kuɗin data ke buƙata ba, gaba ɗaya kansa ya ɗauki caji sai faman tunane tunane ya keyi.
Jan motar ya yi ya koma gidan yana mai addu'ar Allah ya sa wannan karon ta saurare sa.
Sai da yayi addu'oi kana ya sanya ƙafarsa cikin falo, sai dai bakowa a ciki, ya shiga ɗakunan ya fara nemanta amman ko ina ba alamun ta, har banɗaki ya leƙa nan ma bata ciki.
Fitowa ya yi daga ɗakin ya nufi harabar gidan sai yanzu idanuwansa suka sauka a jerin motacin gidan, ba ƙwaya ɗaya "wannan na nufin ta fice kenan?", wai sai yaushe ZULFA'U za ta daina wulaƙanta ni ne?, me take nufi da ni ne?, so take yi na dinga shiga bank-bank ina wawuso mata kuɗaɗe ina kawo mata ne?."
Dafe kansa ya yi dake faman sara masa, ya jima a gurin tsaye yana tunanin ina ta shiga ne?, ganin ba mafita ya sanya komawa cikin ɗakin.
Ruwa ya watso kana ya fito ya nufi kitchin, kamar yadda ya zata hakan ne ya cimma, kwanuka ne watse a ko ina cikin kitchin ɗin , ƙudaje sai faman bibiyarsu suke yi, a haka wai ake rayuwa a cikin gidansa.
Ƙarewa ko ina kallo ya tsaya yi wurin kamar baƙo, lokaci ɗaya zuciyarsa ta dinga juyawa ba shiri ya fice daga kitchin ɗin ba tare daya ɗauki ko cokali daga cikin kitchin ɗin ba.
Parlour ya dawo ya buɗe ƙatuwar freezer dake malale a gurin , sai dai me?, ita kanta freezer yana buɗe ta tsami-tsami ya dinga bugo sa.
Ba shiri ya mayar ya rufe yana mai girgiza kai da neman Allah ya kawo masa ɗauki.
Ɗaki ya koma ya ɗauko ₦500 kana ya fito gurinda mai gadin get, bashi ya yi yana faɗan "dan Allah malam Ayuba taimaka karɓomin RC ƙwaya ɗaya a shagon Inusa".
Ƙarɓar kuɗin ya yi ya fice daga cikin gidan, shi kuwa ya zauna a saman benci yana tagumi.
"Ohni Ƙasim wai ina ZULFA'U ta nufa ne?", ya faɗa yana ƙara rarraba idanuwa a cikin farfajiyar gidan.
★★★★★★
"Ka ga Haruna ka juya ka koma gida, na gaya ma cikin satinnan ina nan zuwa, kuɗin ne ba'a samu ba da zaran ya samo min kuɗin za ka jini."
Wanda aka kira da Haruna ya ɗago kansa yana kallonta sannan ya ce "ni gaskiya na fara gajiya ZULFA'U, ta yaya za ki zo nan ki zauna alhalin kin san kuma kin baro mu can, me hakan ke nufi? kin fi son wannan sakaran dani kenan?."
"Ba haka ba ne Haruna, kai kasan na daban ne kai, ba wani gabanka da bayan ka, kai ne fa zaɓin raina wancan fa, na auresa ne domin mu samu namu rabon".
"Kai kanka kasan da inason sa Allah ba yadda za'a yi na tsaya sauraren ka don kasan ya fi ka da komai."
Ɗaure fuska ya yi tamau kana ya ɗauke kai, ya fara kici-kicin buɗe murfin motar.
Ganin abin da yake da niyar yi ne ya sanya ta saurin dakatar da shi ta hanyar cewa "mi yayi zafi kuma?, gaskiya ce na faɗa ma, kuma kai ne ka nemi hakan ai."
Cikin kakkausar murya ya ce "buɗe min mota na fice ki je can gun wanda ya fini da komai ai dama shi kika zaɓa ni kin watsar dani a titi."
"Sorry nawa , ka dinga tausar zuciyarka mana."
Zip ɗin Jakarta ta zuge sannan ta fito da kuɗi a ƙalla za su kai dubu goma ta ce "ungo wannan kaje a siyawa su baby sweet da rabin kuɗin rabi ka ɗauka naka ne."
Jikinsa na rawa ya sanya hannu ya ƙarɓi kuɗin yana faman washe baki.
"Godiya nakeyi tawa, buɗe min murfin na fita kinga shiddan yamma ta kusa."
"Okey ka kulamin da baby, kwanannan za ta dawo guna ma, insha Allahu."
Ficewa ya yi daga cikin motar yana ɗaga mata hannu.
Ɗan acaɓa ya tara ya haye, tana ganin haka ta yi wa motar ta key ta nufi hanyar gida.....
Za mu ci gaba gobe.
'YAR MUTAN BUBARE