WATA UNGUWA: Fita Ta 13
Yana shigowa ɗakin ya kalle ta a wulaƙance "Rakiya in dai nan ba gidan tsohonki ba ne, ina son yanzu ki bar nan bana son sake ganinki, yaron ma ki ɗauka na bar miki halak malak ki zama uwa da ubansa amma ba zan lamunci wannan iskancin naki ba." Kallonsa ta yi mamaki shimfiɗe a fuskarta 'Lallai lamarinsa azumin ne, ai dai ko wani laifin na yi ya ci ace ya raga mun ko don ganin idon baiwar Allahn nan.' ta faɗa a ranta.
BABI NA SHA UKU
"Tsautsayi ko? Ai kuwa yau za ki ga tsautsayi tunda ke Allah ya yi ki mai kunnen ƙashi ce." Ya faɗa yana huci, ga dukkan alama ransa ya kai ƙololuwar ɓaci.
Durƙusawa ta yi a gabansa tana ƙara roƙarsa "Ka dubi girman Allah Malam ka yi haƙuri wallahi tsautsayi ne ba kai na je duka ba."
"Oh! Ita wacce kika je dukan jakar gidanku ce kenan? Na rasa dalilin da ya sa bakya son zaman lafiya Rakiya, ke kenan kullum cikin masifa tsakanin abokan zamanki? To yau fa na gaji wallahi." Ya kuma faɗa cikin raɗaɗin ciwo tare da ficewa daga gidan, ya nufi kyamis ma fi kusa da su, domin a saka masa maganin da zai tsayar da zubar jinin.
Fitarsa ke da wuya gidan ya kacame, masu dariya na yi masu ƙananun maganganu na yi.
Mama Rakiya bata ce musu kanzil ba duk da tasan da ita suke, amma a yanzu jikinta baya da ƙwarin da zata iya wani kataɓus saboda yanayin zullumi da take ciki ta san halin Malam Audu sarai, ƙaramin aikinsa ne ya furta kalmar saki.
Tunawa ta yi da lokacin baya da suka taɓa samun wata matsala da shi a lokacin ta haifi Amir kenan ko suna ba a yi ba, tana zaune a ɗakinta tare da Hajjo( yayar mahaifinta da ta zo taya ta aikin jego) ya shigo gidan faram-faram ba ko sallama tun daga ƙofar gida yake zage-zage kamar jikan maguzawa.
Ko da yake yan magana sun ce hali zanen dutse, hakan yasa bata wani damu ba, domin inda sabo ya ci a ce duk macen dake gidan ta saba da wannan halin nasa. Domin kuwa duk abun ya motsa masa to ba shakka sai ya yi.
Yana shigowa ɗakin ya kalle ta a wulaƙance "Rakiya in dai nan ba gidan tsohonki ba ne, ina son yanzu ki bar nan bana son sake ganinki, yaron ma ki ɗauka na bar miki halak malak ki zama uwa da ubansa amma ba zan lamunci wannan iskancin naki ba." Kallonsa ta yi mamaki shimfiɗe a fuskarta 'Lallai lamarinsa azumin ne, ai dai ko wani laifin na yi ya ci ace ya raga mun ko don ganin idon baiwar Allahn nan.' ta faɗa a ranta.
Sai dai shi bai damu da hakan ba ya ƙeƙashe ido ya ta tsula ruwan masifa da rashin mutunci, a haka ya fatattake su da sabon jariri suka tattare suka bar masa gidan.
"Su Rakiya hanta ta kaɗa ana tsoron a karɓi jan kati." Inna Halima ta faɗa tare da bushewa da dariya.
Wannan maganar tata ce ta tsinke zaren tunanin Rakiya, Bata tsaya tunanin me zai je ya dawo ba, ta shammaci Halima ta kwaɗa mata lafiyayyen mari.
Dama tana da cikinta, ga shi kuma ta ƙara mata wani haushin shi ya sa ba ta tsaya nazarin komai ba ta aiwatar da tunanin da ya zo kanta.
Ashe fa wannan ɗanyen aikin da ta aikata zai janyo mata nadama bata sani ba.
Ita ma Inna Haliman da yake ba haƙuri ne da ita ba sai ta yi kan Rakiya suna ta zage-zage da cin zarafin juna har ta kai su ga dambacewa. Ana tsaka da haka ne kuma Malam Audu ya kutso cikin gidan, dawowarsa kenan daga kyamis ya nufo gida da nufin kwanciya ya ɗan sarara ko ya samu salama sai dai rikicin da ya tarar ana yi yanzu ya dama na ɗazu ya shanye.
Dalili kenan da ya saka ya kasa jurewa, Allah ya gani ba zai iya ɗaukar wannan iskancin ba.
"Ya ishe ku haka!" Ya daka ma su tsawa a maimakon sallama.
Dukkan wanda ke gidan sai da ya razana da jin wannan firgitacciyar tsawa.
A harzuƙe ya ƙaraso inda suke tsaye suna muzurai ya ce "Iskancin nan naku ya ishe ni haka, ku kenan kullum dambe? Kun mayar mun da gida kamar filin wresttling to ba zan iya ba wallahi na gaji da fitinarku.
Rakiya ki je na sake ki saki ɗaya, ke kuma....." Ya mai da dubansa ga Halima da ta dafe kirji da duka hannu biyu tana jiran nata sakamako. Ya ce "Ki je gida sai na neme ki tunda ke kam kin yada zuciyarki kare ya ɗauka, sakinki ba shi da amfani domin har na gaji da kirgen sakin da na miki amma saboda rashin zuciya har yanzu kina zaune tare da ni."
Nan fa sauran mata biyun suka fara ƙumshe dariya, ba damar su fitar da ita a sarari yanzu abun ya shafe su, hakan ne ma ya saka kowaccensu ta sulale zuwa ɗakinta.
Yana gama bada umurnin ya shige ɗakin Lantai ya kwanta.
Ita kuwa Mama Rakiya da baƙar zuciya ko mintuna biyar bata ƙara ba a gidan ta fice zuwa gidansu, yayin da Inna Halima ta yi biris da umurninsa ta share ɗakinta ta yi zamanta. Dama shi da ita kar ta san kar ne.
Can zuwa ƙarfe 1:50 ya farka daga barci mai daɗin da ya sure shi. Ya nufo waje domin ya yi arwalla kasancewar kiran sallar azahar da limamin unguwarsu ya rangaɗa ne ya tashe shi.
Har ya ɗauki buta zai shige banɗaki ya hango Halima kwance a tsakar ɗakinta, mamaki ne ya turniƙe shi. A ransa ya ce 'Anyah! Wannan kanta ɗaya kuwa? Wato ba ta je gidan ba? Ko da yake zata aikata, idan ban manta ba na sake ta ya kai sau goma amma duk a banza domin ba inda take zuwa ta mayar mun da gida tamkar na tsohonta.'
Saurin shigewa banɗaki ya yi, bayan ya fito ne ya nufi ɗakinta domin ayi ta ta ƙare, duk da ya san cewa abinda zai yi shi ake cewa ihu bayan hari.
Cikin haɗe fuska ya shiga ɗakin yana faɗar "Ke Halima wane irin kunnen ƙashi ne dake wai? Ba ki ji me na ce ba ne, ko ba ki ga yar'uwarki ta aiwatar da umurnina ba ne?"
Yar dariya ta yi sannan ta ce "Ayyah! Yi hakuri ai ban ankara ba ne, ko da yake ma ita nata saki ne dole ta tafi, ni kuma sakin har ya zame mini jiki, shi ya sa baya ɗaga mun hankali, zama kuma daram domin a yanzu zaman yayana nake ba naka ba, na sha gaya maka wannan."
Ba ƙaramin hassali shi ta yi ba saboda haka ya afko mata kamar hadarin da ya haɗu lokaci ɗaya yake neman barƙewa da ruwa........