Ɗumbin jama'a na 'tserewa' daga garin Mada na Zamfara bayan harin 'yan bindiga

Ɗumbin jama'a na 'tserewa' daga garin Mada na Zamfara bayan harin 'yan bindiga

Bayanai daga garin Mada na Jihar Zamfara na cewa mutane na tserewa daga garin bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a jiya.

Shaidu sun tabbatar wa BBC cewa ƴan bindigan sun harbi mutum ɗaya sannan suka tafi da wasu mutum huɗu baya ga ɗumbin dabbobi da suka kora.

Sai dai shaidun sun ce sojoji na dakatar da mutane da ke tserewa domin barin garin, inda suke hana su ficewa, lamarin da ya jawo mazauna Mada ke zanga-zanga.

BBC ta ce ta tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara domin ji daga gare shi, amma bai amsa kiran wayar ba.

Wannan hari dai, shi ne irinsa na uku a cikin kwana uku a jere da ƴan bindiga ke kaiwa garin na Mada da wasu garuruwan makwabta.