ƊANYAR GUBA
Page 17 & 18
Tafe suke a hanya da misalin ƙarfe 8:30 na dare suna nufar titi, lungun da suke ciki ya yi tsit ba ka jiyo hayaniyar komai, sai can jefi-jefi mutane ke wulgawa.
Nu'aymah ta kalli mijinta da fuskar damuwa tana faɗar "Ni fa har cikin zuciyata bana son auren nan na Intisar da za a yi, sam bana goyon bayan ta auri wannan ɗan akuyar."
A kan mene ba kya so ta aure shi? Kin san shi ne?"
"Farin sani ma kuwa, shi ne fa wanda ya biya mini registration fees na shiga poly, ina kyautata zaton ba don Allah yake zaune da ita ba zai gama cin moriyar ganga ne ya yada korenta, ni kuma ba zan so 'yar'uwata ta faɗa halaka ba. Ko ba komai ita ɗin jinina ce 'yar Baffana."
Salis ya ɗan waigo yana jefa mata duban tuhuma, "Ko wani abu ya taɓa shiga tsakaninki da shi ne?"
Ras! Ƙirjinta ya buga da ƙarfi jin wannan tambayar da kuma yanayin yadda ya haɗe fuska. Duk da cewa akwai duhun dare amma ta iya karantar yanayin fuskarsa ta dalilin hasken farin wata da ya haske mata shi.
"Eh." Amsar tambayarsa kenan, wacce kuma idan har gaskiya za ta faɗa masa to wannan amsar ce ya fi dacewa ta ba shi, sai dai ko alama bakinta ba zai iya furta wannan gaskiyar ba, duk da ko ta faɗa ma ba ta tunanin yana da kishin da zai haifar masa da ɓacin ran da zai iya tarwatsa zaman su, iyakaci duk ya yi fushi na ɗan lokaci idan har yanar kwaɗayin abin duniyar da ke idonsa ta kau ma kenan.
"Ina magana kin yi shiru." Ya katse mata igiyar tunani. Sai da ta ƙaƙalo murmushi ta yi kafin ta ce "Sam! Ba wani abu makamancin wannan, kawai dai nasan halinsa ne na kule-kulen 'yanmata da kuma yadda ya ɗauki 'yanmatan tamkar rigar sakawar shi da zai saka wacce yake so a lokacin da yake so ya cire a lokacin da ya yi muradi."
"Hmmm! Shi kenan." Ya faɗa da muryar tantama kafin ya ɗora, "A shawarce ki yi wa Intisar ɗin bayani ko mamanta mai yiwuwa ɗaya daga cikin su ta fahimce ki, duk da na san za ki sha tuhuma amma wannan ce kaɗai mafitarki idan har lallai kina son ki ceci 'yar'uwarki daga hannun wannan mayaudarin" Ya furta ba tare da ya ɗauke dubansa daga kallon gaban shi da yake yi ba.
"Uhm! A tunaninka ban yi hakan ba ne? A yau ɗin nan kusan awanni biyu na kwashe ina ƙoƙarin yi musu bayani, amma a ƙarshe sai da suka tara mini jama'ar gidan kowa ya tofa albarkacin bakinsa. Ita maman Intisar ma gani take yi baƙinciki nake yi wa 'yarta, kasan ma me ta ce mini?"
Ya girgiza kai alamun a'a. "Ce mini ta yi ai Intisar ta yi hankalin da za ta iya tantance daidai da akasin shi ko na manta ita ɗin yayata ce? Don haka ba sa buƙatar wata shawara daga gare ni."
Take a wurin wasu daga cikin 'yanmatan gidan namu suka dinga mini dariya, in taƙaice maka dai saura kaɗan Nusrat ta yaye bargon da muka rufe sirrin gidanmu da shi."
A daidai lokacin da ta dire zancenta suka isa babban titi ya fara ƙoƙarin tsayar da adaidaita da hannunsa ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Wai me Nusrat ɗin ta ce?"
Zuciyarta ce ta fara kitsa mata cewa ko dai ta ɓoye masa gaskiya, sai kuma ta tuna cewa wannan abu ne da ya shafi rayuwarsu su biyu kuma yasan komai game da abin da suke ciki don haka ba ta ga amfanin ɓoyewa abokin cin mushe wuƙa ba.
Kafin ma ta yi magana wata adaidaitar ta tsaya a gaban su. Ya zagaya ta ɗaya ɓangaren ya shiga ita ma ta shiga ta ɓangaren da take tsaye mai abin hawan ya ja ya cilla kan titi samɓal.
Jin ta yi shiru kamar ba ta da niyyar ba shi amsa ya ce "Ina jin ki, wai me ta ce ne?"
Ba ta da sauran zaɓi don haka ta ce da shi, "Ana tsaka da ka-ce na-ce a kan zancena Nusrat ta yi karaf ta ce "Ni fa na yarda da yaya Nu'aymah, domin kuwa ta san shi, sai dai ban san alaƙar da ke tsakanin su ba." Ta ɗan tsagaita da ba shi labarin tana sauke ajiyar zuciya kafin ta ce
"A lokacin ko ka ji yadda gabana ya yanke ya faɗi? Kar ka so ganin fargabar da na shiga."
"Uhm! Ita ko ta ya ta gano kin san shi?"
"Ina kai ka dai Habibie." Ta tari numfashinsa tare da ɗora labarin nata.
"Da ta ga na kalle ta da alamun mamaki a fuska shi ne ta ce "Yi haƙuri yaya, amma ai na ga hotunansa da yawa a wayarki lokacin da kika same ni da ita a kitchen."
To ni sai a lokacin na fahimci ashe bincike ta yi mini a waya ba haska fitila kawai ta yi kamar yadda ta faɗa ba. Abin da ya ba ni mamaki duk matakan tsaro na wayar nan ta ya ta iya karya su ta shiga har ta ga sirrina?"
Salis ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce "Kin san ta da bin ƙwaƙwafin tsiya ai ba abin da ba za ta iya ba kina ganin ta nan da ido firi-firi. Ba wannan ba Habibtie me kika ce musu a lokacin?"
"Cewa na yi da ita abokin yayanka ne, ni ma hoton ya zo wayata ne a lokacin da ka kwafe abubuwanka a ciki za ka gyara wayarka. Kar ka so ka ga yadda iyayen namu suke ta kallona a farkon maganar kafin na samu mafita."
"Allah ya kyauta, amma don Allah Habibtie ki riƙa sara kina duba bakin gatari, meye amfanin da hotunansu za su yi miki kenan? Ko kina mantawa ke matar aure ce idanu suna kanki?"
"Shi kenan in Sha Allah zan dinga kiyayewa. Hotunan da irin idan an turo mini ɗin nan ne sai na manta da su a wayar, kasan ban cika maida kai da goge abubuwa ba." Daga haka sai dukkanin su suka yi shiru kamar waɗanda aka dakatar da masarrafin tv.
Mai adaidaitar dai bai saka musu baki a zance ba sai girgiza kai da ya yi yana ta mamakin waɗannan ma'auratan a zuciyarsa.
Ba su fi mintuna uku da yin shiru ba adaidaitar ta sauke su a ƙofar gidansu Salis ya buɗe musu suka shige.
Kai tsaye Nu'aymah ta wuce ɗakinta hankali a dungunzume, ba ta bi ta kan Salis ba ballantana ta san inda ya sa gaba tun bayan shigowar su gidan.
Mayar da ƙofar ɗakinta ta yi ta garƙame sannan ta yasu a gefen gado tana tuge ɗankwalin kanta tare da yin jifa da mayafin hannunta. Idanunta suka fara sauya launi zuwa launin gautan da ya fara shan rana.
Ba komai ne ya ɗaga mata hankali ba face zancen auren Intisar da Ma'aruf. Ta sani cewa ko sau ɗaya ba ta taɓa kallon Ma'aruf a matsayin masoyi ba, tana dai kula shi ne da nufin yaudara tun da tana sane da cewa ba a aure a kan aure, amma a yau sai take ji kamar tana kishi a kansa.
Nan da nan ta shiga tuhumar zuciyarta da son Ma'aruf. To yaushe kenan ta kamu da ƙaunarsa meye silar hakan? 'kyautatawa mana.' wata zuciyar ta amsa sashin zuciyarta na farko tambayar da ya wurgo mata.
"Tabbas kam kyautatawa tana saka soyayya." Ta faɗa murya ƙasa-ƙasa, ta sani Ma'aruf ya kyautata mata iya kyautatawa, ya so ta da dukkan zuciyarsa a farkon haɗuwar su kafin daga bisani da roƙe-roƙen da take yi da nuna masa son abin hannunsa a fili ya sanya ya rage rawar ƙafa a kanta. Ya so da gaske ya aure ta amma ko sau ɗaya ta ƙi ba shi damar haɗuwa da ɗaya daga cikin danginta a lokacin da ya buƙaci hakan ballantana har a ƙarfafa magana, a kan hakan ya haƙura ya biye mata suka ci gaba a yadda take so. Ita ce kuma ta ribace shi suka faɗa harkar banza don son zuciyarta da son ta ƙara mamaye abubuwan da ya mallaka. Amma da ta sake tuna ita matar aure ce kuma tana son mijinta sai ta shiga ƙaryata sashin zuciyar da ya hakaita mata cewa tana son Ma'aruf ne, ta tsayu a kan ra'ayin cewa kawai tana son tsamo 'yar'uwarta daga hallaka ne domin ko namiji manemin mata ba mijin auren da ake fata ba ne ga kowacce mace ballantana kuma irin Intisar wahala kawai za ta sha a hannunsa.
Zama ta yi ta jingina bayanta da kan gado ta yi shiru kamar mai nazari. Take maɗaukan hoton idanunta suka shiga hasko mata hotunan motsinta a gidansu ɗazu da ta je ake zancen auren Intisar da za a yi nan da wata ɗaya mai zuwa kamar ba za ta tambaya ba kuma sai ta ce,
"Sis Intee shin ba za a nuna mini angon namu ba ne ko ɓoyon shi kike?"
Cikin fara'a Intisar ta ce "Kina da azarɓaɓi Sis, dududu kwana nawa ya rage ki gan shi a wurin shagalin biki? Amma dai shi kenan bari na nuna miki shi kada ki kalle shi da yawa kallo ɗaya za ki masa ki ɗauke ido, kin san an ce ido guba ne." Ita ma cikin murmushi ta ce "Tom shi kenan, bari mu ga wannan wane irin kyakkyawa ne da ake ɓoyon shi haka?" A lokacin ne Intisar take danne-danne a wayarta tana ƙoƙarin nemo mata hoton a wayarta saboda haka ba ta ce komai ba sai murmushi da ta yi don da ma ita Intisar ba ta cika magana ba. Bayan ta nemo hoton ne ta miƙa mata wayar.
Saukar idanunta a kan fuskar wayar kenan ta yi tozali da abin da ba ta taɓa zato ba, a take hannunta ya hau kakkarwa har kamar wayar za ta kufce ta faɗo daga hannunta idanunta suka yo waje, a sa'ilin ne kuma ta tsinkayo sautin Intisar tana faɗar "To ya kika gan shi Sis?"
Ta jiyo tambayar 'yar'uwar tata amma a lokacin ta rasa dalilin da ya saka ta ji bakinta ya yi mata nauyin da ta kasa amsa mata sai ƙara zuƙo hoton take tana ƙare masa kallo don ta tabbatar ba gizo idanunta suke yi mata ba. Can bayan wasu daƙiƙu ta tabbatar da shi ɗin ne dai ba gizo yake yi mata ba amma tana buƙatar yaƙini sama da kokonto don haka ta ta ɗago idanunta ta kalli 'yar'uwarta da murmushin yaƙe a fuskarta ta ce "Ba laifi kyakkyawa ne, ya sunansa ne?"
Intisar ta yi dariyar farin ciki sa'ilin da take miƙewa daga kishingiɗar da ta yi da jikin kujera tana ɗaga duban ta zuwa ga fuskar yar',uwarta kana ta ce "Ma'aruf sunan shi amma ina yi masa Inkiya da Captain..." Ba ta ƙarasa zancen ba dalilin ganin tashin hankalin da ya bayyana ƙarara zane a allon fuskar 'yar'uwarta don haka ta saki wancan zaren maganar ta kama wani. "Me ya faru sister? Da matsala ne?"
Ta rufe idanunta ruf wanda hakan ne musabbabin daina ganin hotunan afkuwar lamarin.
A lokacin ne kuma Nu'aymah ta tsallake gajimaren tunanin abin da ya faru tsakanin ta da 'yaruwarta ɗazu a gida zuwa kan gajimaren tunanin mafita.
Hanya take nema mai sauƙi da za ta raba Intisar da Ma'aruf, don ta sha alwashin muddin tana raye ba za ta bari wannan ɗan akuyar ya ci mata dunduniya ya aure mafi nutsuwar halittun gidansu ba.
Ko ma ban da tausayin Intisar da take a ɓangare ɗaya tana son rufawa kanta asiri, don ta sani muddin aka yi auren nan to asirinta ya gama fallasuwa Ma'aruf zai iya tarwatsa komai.
Tana zuwa nan a tunaninta a hanzarce ta buɗe ido ta hau waige-waige kamar zararriya can ta yi ido biyu da abin da take nema don haka ba jira ta warto wayar kamar wacce ta ƙwato ta a hannun ɓarawo. Ta shiga laluben numbar da ta jima da zuba ta a kwandon shara.
Ta ɓata mintuna sama da ashirin tana bincike wayar tsakanin manhajar WhatsApp da jerin kiraye-kirayen wayarta da kuma saƙunan kar-ta-kwana, amma da ƙyar da siɗin goshi ta samo number a cikin jerin saƙunan kar-ta-kwana da suka jima a wayarta. Sai a lokacin ma ta ga ashe ya ajiye mata sako tun a ranar da ta watsa shi a Black list amma ba ta duba ba. Don haka ta shige cikin sakon kai tsaye don karantawa.
Ta fara karantawa kamar haka; "Na kira ki ba adadi amma gaba ɗaya wayar ba ta tafiya, don na tabbatar da zargina na saka abokina Sadisu ya kirawo ki da layinsa, abin mamaki sai ga wayar ta shiga har ma kin ɗaga kina murnar yin sabon saurayi tun a wurin na tabbatar kin saka lambata a wani tsarin ne, haka nan duk kin yi blocking ɗina a kafafen sada zumuntar da kike amfani da su. Na fahimci kin daina ƙaunata ni ma ba zan ƙara nemanki ba zan je na samu wata mai gudun duniya ba irinki da kike bin ta aguje ba na gode."
'Hakan na nufin kenan shi ne dalilinsa na nemo Intisar? Hakan na nufin kenan shi mai bin duniya aguje ne yake neman mai gudun duniya a matsayin matar aure? Hakan na nufin ya san Intisar jinina ce shi ya sa ya neme ta?'
"Ina! Ba za ta yi kyau ba wuƙa a maƙogwaro." Ta furta da ɗan ƙarfi sannan ta sake saving lambar tare da fitar da shi daga Black list ta danna masa kira. Ta yi ringi tana katsewa har sau uku ba ya ɗagawa, da alama shi ma ya watsa ta a kwandon mantuwa koma ya goge lambarta gaba-ɗaya, don a iya sanin ta da shi ba ta taɓa kiran shi sau biyu bai ɗaga ba muddin yana kusa, Idan ma ba ya kusa yana dawowa zai biyo kiran.
Don haka sai ta ajiye wayar a kan bedside drawer ta shiga safa da marwa tana saƙa da warwarar yadda za ta ɓullo wa lamarin. Wayarta ta hau ƙugin neman agaji ta kai hannu ta damƙo ta ba tare da duba mai kiran ba, har sai bayan ta ɗaga sannan ta lura da sunan mai kiran.
Ko sallamar da ya yi mata ba ta amsa ba ta fara yaɗa manufarta da kausasshiyar murya, "Ma'aruf ina yi maka kashedi da ka fita sabgar 'yar'uwata wannan ba irin waɗan da ka saba yaudara ba ne. Kada ka cutar da ita, bai kamata ka huce haushina a kanta ba." Ta dasa aya tana sauke huci kaɗan-kaɗan. Tun da ta fara magana bai tamka ba sai murmushi mai kama da dariyar takaici da yake wanda har take iya jiyo sautin murmushin nasa.
Sai da ta dire sannan ya ƙara yin murmushi mai bayyanar da mamaki ƙarara kafin ya ce "Ban gane ba, baiwar Allah wacece ke? A kan wa kike magana?"
Fuska gauraye da yanayin takaici da na mamaki take ba shi amsa haɗe da buga masa kashedin ya fita sabgar 'yar'uwarta ko ta yi masa abin da bai zata ba.
Shi kuwa da dama ya fahimci ita ce sai hakan ya yi masa daɗi domin an zo dai-dai gaɓar da zai huce haushinsa a kanta don haka ya yi 'yar dariyar rainin hankali kafin ya ce "Ayyah! Sayyada Nu'aymah ashe kina da lambata? Ai ban taɓa sanin cewa Intisar jininki ba ce da tuni mun jima da zama ma'aurata. Ashe ke ce sisternta da ta gama ba ni labarin kina son ki kawo shubuha a lamarin aurenmu? Kin ga ban taɓa sanin cewa ke matar aure ba ce sai yau, ashe kin daɗe kina shiga haƙƙin aure kuma kina yaudarata...."
Lokacin da ya ambato kalmar aure ya jingina mata sai da ta ji kamar an kwafɗa mata guduma a tsakiyar maɗiga. Sai a lokacin ta tabbatar ta ɗauko dala ba gammo, ta ji ta yi danasanin kiran shi.
Ƙafafunta ne suka kasa jure ɗawainiya da ita ta faɗi zaune a kan gadon saurin bugun zuciyarta na ƙaruwa. Tuni ta zama bebiya iya kunnuwanta kawai ke aikin ci gaba da zuƙo mata cikon furucin da ya fara.
"Ban taɓa sanin bushewar zuciyarki ya kai ki ci amanar aure ba sai yau na gano dalilin toshe duk wata ƙofa da zan san danginki da kike. Kodayake wannan tsakaninki da Ubangijnki ne bai shafe ni ba. Abin da nake so ki sani shi ne aurena da Intisar ba fashi, ruwanki ne ki shiga a yi shagalin da ke ko saɓanin haka. Gargaɗina na ƙarshe a gare ki kada ki sake tada zancen nan kuma kar ki sake kirana idan ba haka ba...." Sai kuma ya yi shiru amma bai kashe wayar ba.
"Idan ba haka ba sai me zai faru?" Tambayar da ta so yi masa kenan cikin zafin rai amma sai harshenta ya yi mata nauyi. Kamar ya karanto abin da ke zuciyarta sai kawai ta ji ya ce
"Idan ba haka ba kuma ki tuna cewa a tafin hannuna kike, idan na so zan iya mutsike ki. Idan kunne ya ji gangar jiki ta tsira." Yana gama faɗa ya kashe wayarsa. Tashin hankalinta ya ruɓanya sarai ta san shi mai faɗa da cikawa ne amma ba ta jin za ta iya haƙura da wannan zancen ganin take kamar idan ta haƙura ta cutar da 'yar'uwarta ne don haka ta yi ƙwafa a ranta ta ce 'Yaro bai san wuta ba sai ya taka, kuma ma idan kasan wata ai ba ka san wata ba.'
SHARE IT PLS
ƊANYAR GUBA