MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum da Aljan, Fita Ta 38 Zuwa 40
MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum da Aljan, Fita Ta 38 Zuwa 40
Page 38-------40
Kai tsaye islamiyar ya wuce gun malam Surajo, bayan sun gaisa ya tambayi abin da ake buƙatar kowane ɗalibi ya kawo mai sauka. Nan take ya bada duk abin da aka buƙata ya bar makarantar, kai tsaye ƙaninsa ya ɗauka suka wuce kasuwa, babban rago ya siya tare da kaji masu yawa yaba ƙaninsa yace ya kai gidansu Bilkisun.
Gun kayan cefane dasu lambu ya koma yayi siyayya mai yawan gaske, ya nufi shagon Babansu Bilkisu ya bashi tare da kuɗi ya nufi inda ya ba da kayan Bilkisu ɗinki ya amsa ya wuce gida.
Kasancewar Inna Huraira bata lafiya kwance take sosai yasa Babansu Bilkisu kiran ƴan'uwansa da nata yace suyi aikin da ake yi tunda Huraira na kwance.
Gida ya kacame da iyaye da abokan arziki anata gyaran kayan miya da sauransu sai ga rago da kayan lambu,aka ce daga saurayin Bilkisu, sai iyaye suka saka guɗa, suna ta godiya da sa albarka.
Bilkisu na zaune ana kwance mata akai ana zana mata ƙunshi Nasir ya shiga da sallamarsa, ya gaisa matan gidan ya shige ɗakinsu Bilkisun dan bai iya shiga ɗakin Babansu.
Gaba ɗaya kunya ta kamata ta rasa yanda zatai sai sunne kai take tana murmushi.
Yana shiga ɗakin ya saki murmushi yanda yaga gimbiyar tasa sai yaji cewar yafi kowa dacen mata kaf zamanin nan .
Daman kayanta ya kawo mata sai yace ta shirya zai turo ƙanwarsa ta rakata ai mata kitso da ƙunshi, dan haka ya fiddo kuɗin kunshi da kitson ya aje saman kayan yayi mata ƴar wasika ya fice yana murmushi mai ƙayatarwa.
Tana ta tunanin yanda zatai sai gashi ya fito ya aje mata takardar ya fice yana tunanin yau ina Innarsu take ? Ya ga anata abu cikin tsari da lumana ba tare da ta watsa gayyar ba, inko hakane to bari yau yayi amfani da damar ya tura ƙannensa gunta, shikenan ya wuce da gun.
Malam Aminu (Ɗan-bahago) ma ba a barshi a baya ba,ya siyo kaji masu yawa ya kai gidansu yasa a soya masa,domin kaima Bilkisu gobe idan Allah ya kaimu zai bata agun saukarsu.
Gaba ɗaya sun natsu suna jiran abin da zai ce masu, ya dubi Badi'atul azam yace, "Ina san gobe duk yanda zaki yi ki yi, ki tabbatar da kin shiga jikin Bilkisu,ki tabbatar da kin aikata abin da zai sa a tsaneta a aibata ta cikin taron nan,ni kuma zan shiga jikin mahaifinta nasa shi ya wulaƙanta ta a wajen. Ya nuna wani baƙin Aljani yace, "Saduƙu kai kuma ka shiga jikin malamin nasu ka tabbatar da nemo laifi mai girma ka ɗora mata wanda mutane za su ƙara tur da ita. Ya dubi su Shamwiylu yace, "Ku ne za ku shiga cikin jikin yaran gun Idan Badi'atul azam ta shiga jikinta ku nuna cewar ita ɗin mayya ce. Cikin murmushin mugunta ya nuna Rayhanatu yace, "Ke ce zaki siffar Innarta Huraira kije gun ki bayyana yanda take wahal da ke duk daren duniya.
Ranar Sauka....
Filin makarantar ya cika maƙil da mutane yara da manya, kowa ka gani fuskarsa a washe, yana cikin murna da farin ciki, an ƙawata wajen da abubuwan birgewa, ɗalibai nata karatu kafin cikar lokacin da za a fara gabatar da saukar.
Bilkisu na ta sauri ta gama shiryawa kenan tayi nufin ɗaura alwalla tayi sallah dan nuna godiyarta ga Allah, da zuwan wannan rana mai muhimmanci a gareta, kawai ta ga jinin al'ada yazo mata.
Dan haka ta aje butar ta kimtsa kanta, ta nufi makarantar farin ciki kamar ta zuba ruwa ƙasa ta sha take jinta yau.
Duk abin da ke faruwa a gaban Bariratul azam aka yi sa, dan haka ta kwashe da wata mahaukaciyar dariya mai ban tsoro ta tunkari Bilkisun da niyyar shiga jikinta, sai dai abin mamaki tana zuwa gab da ita ta ga Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash ta bangajeta sai da ta bugu da bango ta faɗi gefe tana jin wani zafi na tasowa a inda hannun Aljanar ya taɓa ta.
Cikin fusata ta dubi inda Aljanar da tai mata hakan take, amma ganin ko wa ce ce tsaye cikin mugun yanayi yasata shiga cikin firgici mai tattare da tsoro.
Ko da wasa tasan ba zata iya karawa da Raƙiyyatul Zayyanul murrash ba, domin ba ƙaramar hatsabibiya bace ba, cikin sauri tayi nufin ficewa daga gun, sai dai hakan ya kasa samuwa domin wata sanda ta nuna ta da ita, wadda take a gun taji baki ɗaya bata iya motsawa.
Wata mahaukaciyar dariya Raƙiyyatul Zayyanul murrash ta saki kafin ta ɓace ita da Bariratul azam ɗin, baki ɗaya.
Duk abin da ake ba wanda Bilkisu ta gani balle ta sani,domin aikinta kawai take na shirin zuwa gun saukarta.
Cikin daji suka bayyana, da ganin Barriratul azam ta fara galabaita, dan haka Raƙiyyatul Zayyanul murrash ta dubeta fuska a ɗaure tace, "Gayamin shirinku akan Bilkisu da masoyinta yau."
Sanin ko wa ce ce take hannunta yasa ta bayyana mata duk wani tsarinsu a kan Bilkisu na yau .
Dariya ta kece da ita mai firgitarwa tace "Na rantse da Allah ƙarya yake shugabanku san Bilkisu yake, domin da bai santa da tuni ya gama rufe babin rayuwarta a doron duniya, ina san ki koma ki gaya masa ni Raƙiyyatul Zayyanul murrash nace a gaya masa na haramta soyayyarsa da bil'adama wato Bilkisu, domin ita ɗin masoyiya ce ga ubangidana Nasir wanda ni ce mai alhakin kula da rayuwarsa data iyalinsa har ƙarshen rayuwarsu."
Baki ɗaya sai Bariratul azam ta samu kanta da shiga cikin mamaki domin Yah Malam ya tsani Bilkisu mafi munin tsana, ko ta ya zai so wadda ya tsana rayuwarsa ? Haƙiƙa da ba daga bakinki naji wannan batu ba ƙarya tashi zan yi, amma kimun alfarmar tafiya zuwa gunsa na gaya mashi saƙonki."
Dariya ta sake fashewa da ita kafin ta nuna ta da sandar ta ɓace dariyarta na amsa kuwwa a cikin dajin.
Komi yana tafiya yanda aka tsara, yara nata karatun Alqur'ani mai girma, sai ga su Bilkisu sun shigo cikin shigar dogayen riguna da manyan hijabai .
Daga gefe guda kuma Yah Malam ne tsaye daga can gefe, banda Bilkisu babu abin da yake kallo, sai ya samu kansa da tunano ranar haɗuwarsu ta farko da ita, a hankali ya fara tunano wasu abubuwa da suka faru a baya, murmushi ya subuce masa, sanda yake tunano yanda take tsorata idan taga abin tsoro, ga tsoron masifa amma sai nacin ganin ƙwab, duk sanda taji motsi sai taga me ke motsin, amma kuma hanji a burkice.
Wasu kyawawan mutane suka shigo wajen sai ƙamshin turaren miski suke, suna gaisawa da malamai tare da sauran ɗalibai, har suka je suka zauna.
Dakarun da Yah Malam ya turo sai suka samu kansu da firgita ganin waɗannan mutane, wanda kallo guda sukai masu suka gane hadiman masarautar su Raƙiyyatul Zayyanul murrash ne.
Take suka fara neman hanyar guduwa,domin sunfi kowa sanin artabunsu na ƙarshe da su, sai dai kuma suna mamakin yanda akai suka zo gun, bayan babu sauran jikakkiyar adawa tsakaninsu.
Bilkisu na zaune inda aka basu wajen zama, ta fara jin tsikar jikinta na tashi,kanta na neman ciwo, sadda kanta ƙasa tayi tana kiran sunan Allah.
Yah Malam duk abin da ake ya lula tunanin yanda sukai ta karo da Bilkisun, sai ya samu kansa da barin wajen ya koma fadarsa ya zauna yana jin alamar tausayinta cikin ƙasan zuciyarsa.
Bariratul azam na gefen Bilkisu tana huro mata iska mai sanyi daga bakinta,wadda ita ce kesa Bilkisun a mawuyacin halin, aka kira sunan Bilkisu gaban taron, taje tai karatu kamar yadda suka tsara tun farko, ita ce zata fara karatun Alqur'ani na suratul Maryam, sai dai ana ta kiran sunan, amma Bilkisu ta gaza miƙewa daga inda ta ke sai kyarma ta ke ta sanyi, daidai lokacin Major Nasir ya shigo gun, yaji ana ambatar sunan masoyiyarsa, kuma yasan tana gun, to me ya hanata fitowa ? Baza idanuwa ya dinga yi ko zai hango ta cikin masu saukar, amma bai ganta ba.
Shema'u Yahaiya ce ta taɓa ta "Ke Bilkisu lafiya ana ta kiranki fa kina ji kinƙi motsawa kin sadda kanki ƙasa kina ta kyarma duk ɗokin a nan ya tsaya ? Kuka Bilkisu ta fashe da shi, "Shema'u ban lafiya ga sanyi ina ji baki ji ba." Tana magana haƙoranta na karkarwa.
Sai lokacin ya hango ta, bai jira komi ba ya nufi gun duk da akwai ƴan hisba da suke hana zuwa gun amma ko kallonsa ba su yi ba, haka ya ratsa maza da mata ya isa inda ta ke .
"Ibnah lafiyarki kuwa ? Cikin sauri ta ɗago kanta dan gasgata kunnuwanta ai kuwa shine sai hawayenta suka ƙara ƙarfi dan zuwa yanzu ji ta ke kamar ƴan hanjinta zasu tsinke dan azabar sanyi.
Raƙiyyatul Zayyanul murrash ce ta bayyana da suffar ɗaya daga cikin malamai mata tace, "Bilkisu Ahmad zo muje kisha magani na kula baki lafiya ko ? Major Nasir yace "Kwarai kam gashi sai nemanta ake." Kama Bilkisun tayi tana cewa "Yanzu zata samu sauƙin jikinta tana shan magani ai."
Sai jin sanarwar Bilkisu uzuri ya hanata bayyana amma Shema'u Yahaiya zata wakilceta.
Suna shiga office ɗin Malamai Raƙiyyatul Zayyanul murrash ta shafa fuskar Bilkisu ta ke barci ya kwashe ta, tayi murmushi tayi girgiza sai gata ta dawo sak Bilkisun, wasu matan Aljanu suka bayyana suka ɓace tare da Bilkisu.
Duk ya bi ya damu da yanayin da yaga Bilkisun ciki, dan haka ya rasa farin cikinsa baki ɗaya, amma jin sautin karatun ta na tashi yasashi ɗagowa cikin farin ciki ya kalli inda yake jiyo karatun nata.
Gabaki ɗaya gun sai yayi tsit, ana sauraron yanda Bilkisu ke kwararo karatun gwanin ban sha'awa, tana ba kowa ne harafi haƙƙinsa, sai da ta kai sumuni sannan ta dakata, baki ɗaya aka ɗauki kabbara yara da manya.
Zuwa lokacin duk wani ɗan aiken yah Malam ya kama gabansa, domin sun fahimci lamarin baki ɗaya ya sauya ba kamar yanda sukai tsammani ba.
Cikin girmamawa da kwanciyar hankali aka gabatar da Bilkisu matsayin ɗaliba mafi ƙwazo da bin dokokin makaranta, aka bata kyaututtukan litattafai da sauran abubuwa.
Kuka mai sauti ya kubcema mahaifin Bilkisu domin yaji daɗi yau shine wanda ake girmama wa saboda ilimin Bilkisu yau sai girmama shi ake, sai bashi daraja ake, ina ma ace Huraira na gun nan tabbas da ta yi hankali ta daina abin da ta ke yi idan taga baiwar da Allah yayi mata ta samun yarinya irin Bilkisu.
Malam Aminu cike da farin ciki ya nufi inda Bilkisu ta ke tsaye ana ta ɗaukar ta hotuna ya miƙa mata wata kyakkyawar jikka yace, "Ga kyauta ta gareki a wannan rana mai daraja gareki, ina san wannan ranar ta zamo ranar da zaki dasa ƙaunata a cikin kyakkyawar zuciyarki Bilkisu,domin na jima ina fama da dakon ƙaunarki a zuciya na bari na gaya maki ne a wannan ranar mai daraja a garemu, fatan zaki tausayamin ki amshi kyautar zuciyata ki haɗa da taki ki adana mana su waje guda? Murmushi tayi wanda ya sake bayyana kyawunta sosai, tace "Nagode Malam." Ta juya tana mai girgiza kanta,domin ta lura da yanda Major ke kallonsu ransa a ɓace.
A gefe guda kuma sai Malam Aminu ya dage da rabon sticker da yayi ma Bilkisun mai ɗauke da sunanta da zanen Alqur'ani tayi kyau sosai da sosai, munatane nata mamaki bama kamar ƴan ajinsu Bilkisun da suka san irin wainar da aka toya tsakaninsa da Bilkisun.
Nasir kasa haƙuri yayi sai da yayi masa maganar, sai dai Malam Aminu biris yayi dashi kamar baima san Allah yayi ruwansa a gunba .
Ba dan karda ya ɓata mata ranar nan ba babu abin da zai hana ya ji dalilin shisshigin da Malamin yayi masa, miye nasa na yi mata wata sticker ? Ita kuma hada masa murmushi ta amshi kyautar da ya bata. Jin bai iya jurewa ya yi ma ƙannensa maganar su raba kayan Bilkisu ga mutane shi ya wuce.
Sosai Shema'u tasha jinin jikinta, domin yadda baki ɗaya taga Major Nasir yayi tasan cewa komi zai iya faruwa a gun, sai da ta ga yabar wajen ta samu natsuwar ta sosai.
Alhamdulillah! Taro yayi taro, mutane da dama sun halarta, inda Bilkisu ta fi kowane ɗalibi samun kyauta.
Cike da farin ciki kowa ya bar gun taro ya tashi lafiya, kowa ya buɗe baki yace dama ni ce Bilkisu Ahmad .
Sun jima agun amma bai san da zuwansu ba, domin yayi zurfi akan tunanin yarinyar, sai yanzu ne yake hasko kyawunta, da yawan iliminta, sosai abubuwa suka dinga dawo masa a ransa game da ita da shi, ko shakka babu ya yafe mata laifinta garesa.
Ganin ba zai dawo kansu ba yasa Bariratul azam tayi gyaran murya, sai lokacin ya dubeta, cikin sauri ya miƙe tsaye yana nuna ta da yatsa, "Kardai ace kin aiwatar ? Miyasa me ki ? Nasan ba zata iya maki wannan illar ba,domin bata cikin hayyacinta sosai yau."
Tabbas ta yarda da maganar Raƙiyyatul Zayyanul murrash yanzu, ba shakka Yah Malam ya fara son Bilkisu, Lallai kam akwai mummunan tashin hankali a nan gaba,koma a ce ya zo, domin tasan yanda Gimbiya Suwaibatul Zabbar ke ƙaunarsa ba zata taɓa lamunta ya so wata Aljana ma ba balle wata tsiya Bilkisu ba da ta fito daga jinsin mutane ba.
Cikin ladabi ta bayar masa yanda sukai arba da Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash harta fatattake su ta ɗauke Bilkisun ta koma ita.
Wani uban ihu yayi yace, "Na rantse da Allah idan wani abu ya samu yarinyar sai na wargaza masarautarsu na kamota na maida ita baiwa a gareni." Sai kallo ya koma sama, Shaho ya ɗauki Giwa.
Kasan cewar bata san Bilkisu ta samu kanta da tunanin abin da ke faruwa yasa ta shirya irin walimar a wani daji tasa komi kamar yanda akai a makarantar hatta yanda sukai da Malam Aminu sai da ya faru da Bilkisu tare da wani Aljani .
Dan haka Bilkisu keta sauri a tashi taron ta ga Ibnah dan ta ga ya shiga ɓacin rai daga ganin Malam Aminu na mata magana.
Sai dai ta nemesa ta rasa dole ta haƙura .
Labari ya iske Inna Huraira yanda akai komi sosai taji daɗi sai dai zuwa yanzu bata iya ko motsa bakinta .
Mu haɗu a page Na gaba.
Haupha.
managarciya