DUHU DA HASKE: Fita Ta Uku
DUHU DA HASKE: Fita Ta Uku
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 3*
~Yau ake shirya gagarumin taro domin murnan kammala secondary school na manal umar maidawa, duk cikin school ɗin anyi decoration kuma da taimakon manal akayi hakan domin itace take tsara musu yadda zasuyi, bayan an gama guri yayi kyau sai masha Allah, fari da baƙi shine kalan uniform nasu hakan yasa sukayi ƙayata wajen da kayan ado fari da baƙi har zuwa wajen saukan manyan manyan baƙi, bayan ta gama gida ta koma domin yin shiri yau cikin murna take domin dady yayi mata alƙawarin zai mata manya manyan surprise a yau ɗinnan, towel ne ɗaure a kirjinta yayinda ta bazo gashinta da yasha gyara har zuwa tsayin towel ɗin da bai gama rufe cinyarta bama, daga wanka ta fito hakan yasa take ɗan kankame jiki, gaban mirror ta zauna akan stool tana kallon kanta a madubi, murmushi tayi tace "manal babu abinda kika rasa a rayuwa ke kanki kyau kike yiwa kanki bale wa mutane"
shafa fuskanta tayi tace "yau zanyi adon da ban taɓa yin irinshi ba"
kiran wayan Ammi ne ya shigo a hankali ta ɗaga tana shafa mai tasa a handsfree tace "hello Ammi na"
Ammi cikin murnan ganin ƴarta ta girma tace "manal mun tafi da dadynki da fatan idan kin shirya zaki fito da wuri domin dadynki ya aje miki surprise na tsadadden motarki a kofan gida wanda a ciki muke so kizo muci wajen taron karɓan takaddan kammala secondary ɗinki"
cikin jin daɗi tayi murmushi tace "thank you so much mom and dad"
katse wayan ammi tayi, da sauri tayi kwalliya wanda bai fito sosai ba, bayan ta shafa powder ta shafa mascara akan zara zaran eyelashes nata sannan ta shafa lipbalm akan lips nata, gashinta ta kame da ribbon fari sannan ta tashi tana shafa turaren jiki, kayan dake kan tamfatsetsen bed nata ta ɗauko farin riga ne kamar wedding gown da takalminshi me tsini, sawa tayi ta kalli lalle baki da ja dake kwance akan tafin hanunta da bayan hanun, murmushi tayi wanda tana jimawa bata yi ba, idan kaga tayi murmushi to tana tareda ammi ko dady, agogon hanu tasa wanda dady ya siya mata tsadadden rolex ne, ɗankunne da sarka duk na gold Ammi ta siya mata sabida wannan ranan, turare ta fara jiƙa jikinta dashi, ta ɗauko crown ɗin da Ammi ta bata tasa a saman kanta, kallon kanta tayi a madubi tace "wow wow wow kece miss world manal"
wayar da dady ya siya mata iPhone 16 da cover fari ta rike a hanunta kafin ta ɗauko karamin jakan dake ɗauke da adon duwatsu fari mai ɗaukan ido ta rike, fitowa tayi daga ɗakin fuska babu fara'a domin bata saba ba, tafiya take kamar boss, masu aiki sai bata hanya suke tana tafiya bayan riganta yana binta.
a unguwan tudun anan wata kyakkyawar budurwa ta tsaya akan mashin nata me ƙafa biyu, sanye take da riga da wando, wandon a buɗe yake sosai kamar skirt da riga baƙi me ratsin pink a hanu da wuya, hanun rigan a yanke yake, ta ɗaura bakin rigan sanyi a waist nata, gyara baƙin mayafinta take a daidai lokacin ta juyo da kyakkyawar fuskanta, masha Allah wannan yarinyar karshe ce wajen kyau, fara ce sal, ɗaga murya tayi ta buɗe karamin bakinta, da karfi tace "MAAAAAAAAN"
ganin bai leƙo kamar yadda ya saba ba ta ɓata tare tareda turo karamin bakinta ta kuma buɗe murya tace "maaaaaaaaaan"
sau uku tana kiranshi bai amsa ba kuma be fito ba, a yadda suka saba kullum da safe idan tazo nan ɗaukanshi akan mashin nata zai amsa ko kuma ya leƙo, wani ma riganshi a hanu yana sawa yake fitowa, sauka tayi akan mashin ɗin kamar zatayi kuka, fuska a shagwaɓe da gajiyan da takeji ta fara bubbuga kofan gidansu, da alama ta saba da wannan ihun idan zata kirasu tace "man ka buɗe kofa mana kazo zamuyi late"
ji tayi an buɗe kofan kallon matar dake tsaye tana mata murmushi tayi, tasa kafa cikin saurin data saba tace "umma man wai har yanzu bacci yake?"
wacce aka kira da umma kyakkyawar mata ce ta manyanta kaɗan, tana hamma tace "to AMEESHA ai dole yanzu ya tashi tunda kinzo irin wannan buga kofan naki kamar ana yaki ba dole yanzu ya tashi ba"
tana tafiya tana cewa "ai man baya ɗaukan komai serious bai damu da neman aiki ba nice na damu"
bankaɗe kofar ɗakinshi tayi ta shiga, tsayawa tayi tana kallonshi yana bacci ya rungume pillow ya cusa kanshi a cikin pillow, hannu ta ɗaura akan kwankwasonta dake ɗaure da rigan sanyi tana tuna ya zata fara tashin shi a baccin nan, da sauri tayi dariya sannan ta fita ta ɗauko roba a tsakar gidan, ruwa me sanyi ta ɗibo a randa ta ɗaura akanta da kyar ta kama hanyan shiga, wani matashin kyakkyawan yaro da ba zai wuce 20years ba ya fito daga wanka yana tsane jikinshi da towel, ganinta da bokitin ruwa ya buɗe baki zaiyi magana tasa yatsa a baki tareda waro mishi manyan idanunta alaman yayi shiru, cikin sanɗa ta shiga ɗakin taje inda yake kwance akan karamin gadonshi dake gefen na kaninshi ruwan ta juye akanshi, a firgice ya tashi daga baccin yana goge ruwan dake fuskanshi, ido ya zuba mata, subhanallah ashe duk wani me kyau a duniya akwai wanda ya fishi, wannan shine asalin kyau, gashin kanshi a kwance sosai luf, ya kara kwanciya sabida ruwan daya jiƙashi, gashin idonshi kuwa ba'a magana domin baƙi ƙirin kuma a kwance, karami baki ne dashi, idonshi yafi komai ɗaukan hankali a fuskanshi, kallon jikinshi yayi yanda ya jike har zuwa kan gadon, armless ne a jikinshi da wando three quarter, tana rike da waist da hanu ɗaya ɗayan hanun kuma tana nunashi dashi tana dariya kamar zata faɗi kasa, wanda yake tsaye a bakin kofan yasa hanu a baki shima yana toshe dariya, ganin bata daina dariyan ba yaji wani irin haushi, fizgota yayi da karfi ya wurgata kan gadon, waro ido tayi tace "dan Allah...dan Allah...dan"
ragowan ruwan dake cikin bokitin ya juye akanta, ihu tayi tace "sanyi wayyo umma"
tashi yayi yana cire rigan, faffaɗan kirjinshi ɗauke da kwantaccen gashi, yana gama cire rigan ya shiga toilet baiyi magana ba, tashi tayi tana turo baki tace "IMRAN bani riganka"
yana shafa mai yace "a cikin wardrobe"
buɗe wardrobe tayi ta ɗau riganshi me kyau longsleev ta fita, ɗakin umma tayi sallama sannan ta shige a time ɗin umma tana haɗa musu breakfast, da sauri ta fara cire bottle na gaban riganta tace "umma kinga man ya watsa min ruwan sanyi banyi mishi komai ba ko?"
umma tace "na sanki da neman tsokana fa ameesha anya ba kece kika watsa mishi ba?"
turo baki tayi a time ɗin ta cire rigan tasa na imran, ya mata kyau sosai ta bazo gashinta daya jiƙe tana so ya bushe kafin su tafi, umma ganin tayi fushi tace "yi hakuri nasan laifinshi ne, ai tun kuna kanana yake yawan tsokananki"
sai yanzu tayi dariya, fitowa tayi ta koma ɗakinsu bata kame gashin ba, zama tayi a bakin gadon Imran tana ganinshi yana shiryawa tace "man kasan me?"
girgiza kai yayi
tace "yau naji labarin wani company wai suna neman masu aiki shiyasa kaga na fito da wuri"
yana gyara suman kanshi ya lumshe ido a hankali ya kuma buɗewa sannan yace "kullum bakya barina nayi bacci sai zancen aiki aiki aiki"
murmushi tayi fuskanta ya koma serious tace "man ya zama dole ka neme aiki duba da iyayenmu maza basa raye, Abbana da Abbanka abokai ne tun suna yara, abotansu yasa har yanzu muke tare mun zama kamar family ɗaya, sun mutu rana ɗaya sanadin hatsarin mota, Allah bai basu kuɗi ba hakan yasa dole sai mun nema zamu taimaki iyayenmu mata, ka taimaki kaninmu Imran sannan na taimaki kanina farhan da ummanka da mamana, shiyasa kullum nake taƙura maka akan neman aiki"
kallonta yake ta cikin madubi yadda take hawaye tana magana tareda murza yatsanta, girgiza kai kawai yayi baiyi magana ba saida ya gama abinda zaiyi ya ɗauko takaddun school nashi yazo inda take, zama yayi a gefenta ya riko hanunta yana murzawa yace "my meesha ba gashi na ɗauko takaddun zamu tafi ba?"
a hankali ta jijjiga kai idonta yana kara cika da hawaye, kwaɓe kyakkyawan face nashi yayi sannan yace "to ina zanji farin ciki babbar kawata da muka taso tare tun muna yara tana kuka?"
a hankali tayi murmushi kanta kasa, tashi yayi yace "muje na gyara miki gashinki saimu tafi ko?"
share mata hawayen yayi da tafin hanunshi ya kaita gaban mirror, zaunar da ita yayi a gefen gadon Imran dake facing mirror ɗin, yana kallonta ta cikin madubi yana gyara mata gashin, cikin muryanshi me kashe zuciya yace "duk wanda ya auri wannan kyakkyawar kawar tawa gaskiya ya auri rigima"
duka ta kai mishi ya kauce yana dariya, Imran ya shirya tsaf cikin uniform ya rataya jaka saide fuska babu annuri, kallonshi tayi lokacin da zasu fita tace "ya dai? kake haɗa fuska lafiya?"
cikin ɓacin rai kamar zaiyi kuka yace "banida ko biyar a hanuna kuma nasan ya ABDUL ma baida kuɗi da zai bani"
murmushi tayi tasa hanu a aljihun wandonta tace "ga kuɗin mashin naka ga kuma kuɗin kashewanka sai kayi manage kasan tunda wannan rakwaɓaɓɓen motan man ɗin ya ɓaci muka fara tafiya akan mashin ɗina dan nasan motan ba zai taɓa gyaruwa ba"
dariya yayi ya rungumeta yace "thank you Ameesha"
shafa kanshi tayi tace "don't mind"
umma ta fito musu da breakfast tace "Abdul ka tsaya kuci abinci kada ku tafi da yunwa"
zaiyi magana ameesha tace "no ki barshi kawai saimun dawo"
cikin jin haushin aikin data dameshi saiya nema yace "nifa yunwa nakeji"
tace "umma sa mana a flaks"
juye musu tayi a flaks Imran kuma yana tsaye yana ci da sauri kafin su Ankara su hanashi, rikewa tayi suka fita Imran ma ya fita, hawa mashin ɗin tayi shima ya hau ya zauna ta mika mishi flaks tace "gashi rike"
hararan kanta yayi yace "ban gane rike ba"
tace "kafi karfin rikewane malam ABDUL-RAHMAN?"
ganin ba zai karɓa ba ta riko hanunshi ta damƙa mishi taja mashin ɗin suka fara tafiya, cikin jin daɗi tace "first time da mace take jan namiji kenan idan zasu je unguwa akan mashin"
yace "ai kece baki yadda na jamu saiki janyo kowa yayi ta kallon mu kawai"
tace "oho dai ai ban taɓa zubar damu a kasa ba"
rankwashi yayi mata a kanta yace "waye ya taɓa zubar damu?"
tace "kai mana"
suna cikin tafiya har suka isa check point, tsaki taja tace "wallahi na tsani check point yanzu zasu ɓata mana lokaci"
shiru yayi yana kallon mashin da kuma layin motoci, yace "my meesha?"
tace "yes"
yace "watarana zanso na siya mana mota mu rinƙa yawo dake muma mu zama masu kuɗi"
tace "ni kuma banson hakan"
yace "sabida me?"
da mamaki sosai akan fuskanshi yayi mata tambayan, tace "sabida idan ka samu kuɗi harma ka siya mota zaka iya daina jirana mu fita unguwa tare, idan kayi kuɗi zaka iya mantawa dani ni kuma ba zanso haka ba, rayuwarmu a haka yafi min daɗi, dani da kai da Imran da kuma farhan ga mama ga kuma umma muna rayuwa cikin nishaɗi duk da bamuda kuɗi hakan baisa munyi rayuwa cikin kunci ba, sabida mu muke bawa kanmu farin ciki, duk abinda zai tarwatsa wannan abota na tsawon shakera da shekaru wanda ya fara tun akan Abba ba zanso shi ba, kasan kai kaɗai ne abokina bansan kowa ba banida kawa banida sai kai, daga kai sai Imran sai farhan kune abokaina, har mutane suna cewa ni bana yin abu irin na mata kullum ina cikin maza, harma bana iyasa riga da skirt na sake a ciki nafi gane riga da wando kaga ai ba zanso mu rabu ba koda na second ɗaya ne, yanzu ma aikin da zamuje nema nima da takadduna saimu nemi aiki iri ɗaya ko?"
jin yayi shiru tace "ya kayi shiru?"
a hankali yace "koda me na zama a rayuwa bazan taɓa iya mantawa dake ba meesha, dake na saba tun ina yaro kece kusa dani ba zanso abinda zai rabam...."
daidai lokacin taja mashin ɗin suka tafi an basu hanya, manal dake zaune a cikin motarta ta sauke glass sabida batason zufa ya ɓata mata kwalliya tafison iska yana shiganta, ɗan yaye mayafinta tayi ganin an basu hanya taja motar, iska ne ya kwashe mayafin ya fitar waje, da sauri tasa hanu zata rike saide kash mayafin ya riga ya gudu, tsaki taja taji gaba da driving, cikin sanyin murya yace "meesha ai idan mun samu aiki duk problems ɗinsu zamuyi solving domin kuɗi zai rinƙa shigo mana, zan kaiki super market ki siyi duk abinda kikeso da farkon albashina"
tana murmushi ta buɗe baki zatayi magana taga farin mayafi ya rufe mata fuska, waro ido tayi ganin kan mashin ɗin ya suɓuce mata, tangal tangal ta fara dasu man yayi saurin riketa yace "meya faru?"
zuwa yanzu idonta ya rufe sosai da mayafin tambul mashin ɗin yayi suka faɗi kasa, karan azaba tayi jin hanunta kamar baya jikinta, da kyar tace "man kana lafiya"
shima cikin dauriya yace "eh kefa?"
tace "hanuna"
mashin ɗin ya faɗi akansu mutane ne suka ɗaga mashin ɗin suka fara ɗaga man, da sauri ya fara ɗaga ta, cire farin mayafin yayi wanda yake kamshin turare sosai, ya riketa yana goge mata jikinta daya ɓaci da ƙura yace "sannu"
hanunta ta nuna mishi idonta cike da hawaye tace "naji ciwo"
farin mayafin ya ɗaura mata a hanu yace muje chemist"
kwance mayafin tayi ta wurgar a ƙasa tace "wannan mayafin yasa muka kusa rasa rayuwarmu na tsaneshi"
murmushi yayi yace "tunda bamu rasa ba ai bai kamata ki tsana ba"
taka mayafin tayi cikin masifa tace "wallahi da naji kana kareshi sai naji kamar na ƙona"
dariya yayi sosai ya rike hanunta yace "sorry my meesha yanzu bari na kaimu chemist"
tace "a,a muje wajen aikin kada muyi late banji wani ciwo ba"
zaiyi magana tace "mujeeee"
hawa mashin ɗin yayi ta hau bayanshi yaja suka tafi, tana duba address ɗin da aka sanar har suka isa wajen, mutane suka gani dayawa a wajen, ya kalleta itama ta kalleshi, hanunshi ta rike tace "muje"
yace "kinga fa da mutane dayawa"
tace "addu'an samun sa'a zakayi ba wai ka karaya da wuri ba"
a kofa suka zauna kamar yadda mutane suke a zaune, abincin dake kula ta ɗauko da cokali tazo gabanshi ta zauna, kallon kyakkyawan innocent face nashi tayi sannan tace "haaaa"
murmushi yayi yace "meesha banajin yunwa"
tace "ba kaine kace a gida kana jin yunwa ba?"
girgiza kai yayi yace "ke kici sabida nasan bakici komai ba"
shiru tayi ta ɗibo tasa a baki, sannan ta ɗiba ta kai bakinshi, ganin ta ɓata rai yasa ya karɓa yana ci, da haka har suka cinye tace "good bari na kai kan kulan kan mashin"
zazzafan mota ne yayi parking da alama shine me company ɗin, fasa kai flask ɗin tayi ta aje a wajen tana hamdala, saida ya shiga aka buɗe musu suka shigo, fitowa yayi daga motan yana karewa dukansu kallo, Alhaji faisal shine me wannan company cewar wani dake bayansu ameesha, saida ya shiga ciki da jimawa kafin ya aiko a fara kiransu, koda me kiran yazo da alama shine manager ya nuna manal yace "yace ke ki fara zuwa"
kallon man tayi cike da murna tace "muje"
girgiza kai yayi yace "kece akace ba mu ba"
da sauri tace "ai tare nake da kai"
yace "no kije idan yace nazo saina shigo"
jijjiga kai tayi sannan ta wuce cikin tafiyanta me sauri da ɗaukan hankali, sam bata sani ba idan tana tafiyan duk jikinta na girgiza, knocking tayi yace "yees"
shigowa tayi ta tsaya tana murmushinta me kama da dariya domin ta saba da hakan, sosai yake kallonta bata kawo komai ba tace "good day sir"
wajen zama ya nuna mata, cikin sabo da sa riga da wando ta gyara ɗaurin rigan sanyi da tayi a waist zata zauna yace "kwance rigan sanyin"
sam ameesha bata kawo komai a ranta ta riga ta saba dasu Man tana iya ma canja kaya a gabansu saida umma ta hanata take ɗan dainawa wataran, a ganinta kowa ma haka ne normal, ta kwance rigan sanyin, kallon shape nata yake yana lasan baki, ya kalli gaban riganta data rufe da bottle yace "juya"
juyawa tayi, yace "juyo"
juyowa tayi yace "god of creation amma wannan saurayin da kuke tare baisan kayan da yake tare dashi ba ko?"
bata gane ba kawai tayi mishi murmushi, batada kawaye bale tasan irin wannan maganan na batsa ne, yace "da alama yasan darajanki saboda shape da kike dashi, irin wannan kayan dole ya rinƙa zuwa ko ina dake mana sabida kada wani ya taɓa mishi ke"
shiru tayi zuwa yanzu ta fara tsarguwa, ganin kamar batada wayo sosai yace "sau nawa yake yi dake a rana?"
cikin rashin fahimta tace "me?"
cikin iya barikanci yace "s**"
tashi tayi a fusace ta bige kujeran data zauna akai, tace "dama maganan banza ka kirani kamin?"
tashi yayi ya fara matsowa kusa da ita baya baya ta fara tana neman kofa ta buɗe ta gudu, saida ta jingina da jikin kofan ya matso kusa da ita yace "kina nufin wannan kyakkyawan gayen dana ganki dashi baya taɓa wannan tsadadden jikin?"
yayi magana yana kai hanu kirjinshi, bige hanunshi tayi da karfi tace "maaaaaaan"
toshe mata baki yayi da karfi, hanu yasa a gefen cikinta inda tasa belt na wandon yanaso ya kwance, girgiza kai ta fara tana kwace kanta.
Man yana tsaye yaji shaƙuwa yana damunshi da sauri yace "tunda ina shaƙuwa akwai abinda yake faruwa da meesha"
shaƙuwan ya kara karuwa, da sauri ya nufi hanyan zuwa office ɗin, tareshi manager yayi yace "dakata idan oga yana ciki babu me shiga"
tureshi yayi yana shaƙuwa yana karuwa, direct kofan office ɗin yaje ya fara knocking, ganin ba'a buɗe ba ya fara bubbugawa da karfi
"meesha? meesha?"
jin tayi shiru yayi baya da karfi yazo ya buga kofan da jikinshi, kara komawa baya yayi ya kara bugawa nan take kofa ya ɓalle waro manyan idanunshi yayi ganin suna kokawa, cikin zafin nama yaje ya janyeshi, maruka ya fara wankeshi dasu, dukanshi ya fara yana cewa "meesha kake yiwa haka?"
cikin zafin rai yace "kasan wacece ita a wajena?"
dukan da yake mishi ya fara bawa Ameesha tsoro karfa ya kasheshi, da gudu taje bayanshi ta rungumeshi tana cewa "mu tafi ka kyaleshi haka"
cikin zafin rai da tsananin huci ya wankeshi da marin da yasa hancinshi ya fara jini, man yanada karfi sosai tafi kowa sanin hakan domin bayason faɗa ko marin mutum yayi zai iya ji mishi ciwo, yace "macen da zata iya sadaukar da farin cikinta sabida wasu kake nema kaci mutuncinta? ameesha dake sona fiyeda yadda take son kanta kake yiwa haka? babbar kawata da banida kamar ta a duniya kake yiwa haka?"
kuka ta fara tace "dan Allah ka kyaleshi"
ganin ba zai kyaleshi ba ya ɗaga hanu zai kara ɗukanshi tace "ya isa Abdool"
cak ya tsaya bai karasa da hanun jikinshi ba, dunƙule hanun yayi ya fesar da Iskan bakinshi, a hankali ta fashe da kuka ta faɗa jikinshi, rungumeta yayi tsam yana shafa bayanta, a hankali yace "shiiii"
jin sautin kukanta kamar ana zuba mishi wuta a zuciya, hanunta ya rike suka fita daga wajen, hawa mashin yayi itama ta hau, shiru sukayi suna tafiya.
ranta a ɓace ta isa wajen taron domin mayafinta daya faɗi ya bata haushi abin, fitowa tayi daga motar tana taku tamkar ɗawisu, kallon mutanen dake wajen tayi komai ya tsaru da kyau, waje ta samu ta zauna tana ɗagawa Ammi da dady hanu, nan aka fara gudanar da taro manal na zauna tana bin kowa da kallo, da haka har aka fara kiran kowa ana basu statement of result nasu tareda iyayensu suna basu kyaututtuka, lokacin da aka iso kan manal duk ƴan matan suka fara hararanta sabida sun tsaneta bata kulasu gata da girman kai da rashin sakewa a wajen mutane, gata da kyau domin duk wajen babu wanda ya kaita kyau a cikinsu, dady ne ya karɓi result ɗin zai mika mata ya haɗa da makulli yace "wannan makullin company ɗinki ne na M.U.M fashion designer, wato manal umar maidawa fashion designer inason kara tallata company ɗinki duk masu buƙatan decoration na kowane event a nemi m.u.m fashion designer"
tafi akayi sosai tareda taya ta murna, sannan ya ɗauko wasu takaddu yace wannan sune takaddun private jet ɗinki wanda nayi miki alkawari tun kina karama"
rungumeshi tayi tana share hawayen farin ciki, ammi ta bata atm tace "wannan atm ɗin account ɗin akwai naira biliyan goma inaso ki zama billionaire ba millionaire ba"
rungumesu tayi dukansu biyu ta karɓi mic cikin murna ta yiwa iyayenta godiya da pure english wanda yasa duk mutanen wajen suka tafa, da haka suka koma wajen zamansu, koda aka tashi dady da Ammi da sauran mutanen suka rakata domin buɗe sabon babban company ɗinta, tun daga kofa tasan dady ba karamin kuɗi ya kashe ba, lokacin da suka shiga ciki saida taji kamar ta haɗiyi dady dan murna, mutane suka tayata murna da kuma fatan alkhairi, cikin jin daɗi suka koma gida, Ammi tana farin cikin ganinta haka tana murna, manal bata sakewa bata dariya koda yaushe fuskanta a ɗaure, bata son wasa tun tana yarinya haka take, wannan yasa ammi take son ganin sun sata farin ciki.
*Jiddah Ce....*
08144818849
managarciya