Ɗan Majalisar Tarayya Ya Baiwa Sarkin Zuru Kyautar  Dalleliyar Mota

Ɗan Majalisar Tarayya Ya Baiwa Sarkin Zuru Kyautar  Dalleliyar Mota

Dan Majalisar tarayyar Najeriya mai wakiltar kananan hukumomin Zuru, Fakai, Danko, Wasagu, da Sakaba dake jihar kebbi, Honarabul Kabir Ibrahim Tukura, yayi kyautar dalleliyar Mota ga Masarautar Zuru.

Masarautar ta samu kyautar Motar ne daga ɗan majalisar in da ya gwangwaje Sarkin Zuru Drakta  Mohammed Sani Sami Gomo na ll  kyautar mota kirar Lexus jif domin saukakawa mai martaba saukin Zirga-zirgar Masarauta.