Bafarawa Ne Ba Ya Son Zaman Lafiyar Sakkwato----Ibrahim Lamido
Dan takarar Sanata a yankin Gabascin Sakkwato a jam’iyar APC Honarabul Ibrahim Lamido Isa ya bayyana jagoran tafiyar APC a jiha Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko mutum ne dake son jihar Sakkwato ta zauna lafiya a dukkan abubuwan da yake yi, hakan ya sa yake ta hakuri da kawar da kai ga duk abin da ‘yan adawarsa ke yi masa.
Ibrahim Lamido a zantwarsa da manema labarai a gidansa a birnin Sakkwato ya ce Bafarwa ne baya son zaman lafiyar jihar Sakkwato “ai kowa yasan Bafarawa ne baya son zaman lafiya, a karamar hukumarmu ta Isa kowa yasan abin da aka so a yimin shi yana cikin wanda ake zargi, a kasar nan irinsu na cikin wadan da ba su son a zauna lafiya.
“Mutum ya shekara 70 a duniya sai ya yi magana ya ce ya bar siysa ka ga ya sake dawowa, ai duk wanda yake dattijo ba tsoho ba Magana daya yake yi in ya ce ya bari ba zai sake dawowa ba, ni da kananan shekarruna ina nace na bar siyasa wallahi ba zan sake dawo mata ba,” Kalama Ibrahim Lamido.
Lamido ya godewa magoya bayan jam’iyar APC da suka fito suka zabe su cikin tsanaki ya kuma ba su tabbacin cewa nasara tana gefensu, su kwantar da hankalinsu kalmomin tsoro ne PDP ke yi a Sakkwato.
“Ai mu muka ci zabe ba mu fadi ba, duk wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa wane zabe yake jiran ya ci, PDP ce ta fadi zabe don haka suke son kawo hatsaniya, kuskuren da muka samu a wancan zaben mun fahimce shi kuma mun gyara mun yi shiri wanda yafi nasu ko da mi suka zo mun shirya.
“Za mu yi tsaye mu kare talakkawan Sakkwato domin APC ke da sama kashi 70 na magoya baya a jiha, masu son tayar da fitina sun ga za a yi masu ritaya ne a siyasa mun dauki mataki fiye da nasu, duk wanda ya tayar da fitina jami’an tsaro za su yi aikinsu kan shi, mutane su fito su zabi jam’iyar APC su guje wadda ta kasa magance masu matsalar tsaron da ake fama da shi ga ‘yan gudun hijira ko’ina, kanan hukumomi na cikin wahala da yardar Allah APC za ta samu nasara a zaben Gwamna da sauran zabukkan sanatoci uku da ‘yan majalisar tarayya wanda aka ce bai kammala ba,” a cewar Lamido Isa.
managarciya