Yadda Goyon Bayan Kudurin Harajin Tinubu Ya Jawo wa Barau Suka a Arewa

Yadda Goyon Bayan Kudurin Harajin Tinubu Ya Jawo wa Barau Suka a Arewa

 
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibrin ya fusata mazauna Arewa saboda fitowa karara wajen goyon bayan kudirin harajin Tinubu. 
Zargin goyon bayan  abun da zai cutar da Arewa, ya na daya daga cikin abubuwan da zai iya kawo nakasu ga tafiyar dan siyasa da ya fito daga yankin. 
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda aka samu masu sukar Sanata Barau I Jibrin, musamman a shafukan sada zumunta bisa zargin fatali da cigaban Arewa.
Guda daga dalilan da aka rika zargin Sanata Barak da rashin kishin Arewa, shi ne yadda ya rika musayar yawu da Sanata Ali Ndume da ke adawa da kudirin. 
Barau, ya nuna goyon bayansa ga kudirin harajin Tinubu, inda wasu ke zargin ya yi haka ne saboda kare siyasarsa. 
Ana zargin siyasar Sanata Barau ta shiga wani hali, bayan an rika wa'azi a masallatan Juma'a, ana zarginsa da goyon bayan kudirin da zai kara talauta Arewa.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Barau I Jibrin ya musanta zargin cewa ba shi da kishin Arewa ko son cigabanta, tare da kare kansa. 
Sanata Barau I Jibrin ya kara da cewa babu yadda za a yi, ya goyi bayan wani kudiri da zai cutar da shiyyar Arewacin kasar nan da ya fito.