'Yan majalisar dokokin Sakkwato sun yi wa Shugabansu wankin babban bargo

'Yan majalisar dokokin Sakkwato sun yi wa Shugabansu wankin babban bargo

 

Daga Muhammad M. Nasir.

‘Yan majalisar dokokin jihar Sakkwato su 13 daga cikin 15 da aka zaɓa karkashin jam’iyar adawa ta APC sun yi wa Kakakin majalisa Alhaji Aminu Muhammad Achida wankin babban bargo kan takardar ƙorafin zaɓen shugabannin mazaɓu da aka aikawa jam’iyar APC yana cikin waɗanda suka sanya hannu a takardar.

Mambobin majalisar a takardar da suka aikawa shugaban riƙon jam’iyar APC na ƙasa Gwamnan Yobe Mai Mala Buni kuma suka yi kwafinta ga jagoran jam’iyar a jiha Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da shugaban jam’iya na riƙo a jiha Isah Sadik Achida sun ce su 13 za su yi martani ga ƙorafin Kakakin majalisa  da yake cewa ba a yi zaɓe ba, sun tabbatar da an gudanar da zaɓen mazaɓu a jihar Sakkwato lami lafiya da lumana, bisa amincewar mafi rinjayen masu ruwa da tsaki na jam’iya   a  yi zaɓen sasantawa kamar yadda daftarin zaɓen jam’iya ya aminta.

“Biyayyarmu ga jagoran APC a Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko nanan daram  domin ya riƙe jam’iya ba son kai da kasawa tsawon shekarru.

“Mun nisanta kanmu da kakakin majalisa a  maganarsa ta ba a yi zaɓe ba domin wannan zargin nasa abu ne da ke son kawo rabuwar jam’iya bisa ga matsayar  mafi rinjaye, ba mu cikin wannan zargin na cin zarafi da ɓatancin shugabanni da wasu gungun mutane suka yi wanda shugaban majalisa yana tare da su.

“Zargin da kakakin majalisa ya yi abu ne na rashin cancanta, ba shawara ce mai kyau ba hakan na iya taɓa nasarar APC a gaba don haka mun yi tir da amfani da ofis ɗinsa wurin aikata abin da baya da tushe ga hukuncin mafi rinjaye.” A cewar bayanin.

‘Yan majalisar sun jawo hankalin shugaban  cewa a lokacin da ake gudanar da  zaɓen kakakin majalisar baya Nijeriya(ya je Nijar) a takardar ƙorafin da ya sanyawa hannu ma sai da aka jawo kwanan watanta  baya  hakan ya sa sun ƙara jefar da abin da yake riyawa wai shi ne jagoran jam’iya a jiha, sam ba su san da batun ba domin ba haka jam’iya ta tsara ba.

Sun ce  ƙoƙarin kawowa jam’iyarsu cikas da abokan hamayarsu ke yi ba zai samu nasara ba saboda jajircewar shugabaninsu, don haka sun yi kira ga shugabannin jam’iya a matakin kasa su jingine ƙorafin kakakinsu domin ba ra’ayi ne na mafi rinjaye ba.   

A kwanan baya ne aka rubuta takardar koke kan zaɓen da aka yi a jihar Sakkwato in da Ɗan majalisar tarayya mai waƙiltar Gwadabawa da Illela Honarabul Abdullahi Balarabe Salame da Kakakin Majalisar Aminu Achida da Alhaji Sadiƙ Gebe suka sanya hannu kan takardar koken, suna buƙatar uwar jam'iyya ta yi masu adalci.