Ɗan Gwamna Ganduje ya kai ƙarar mahaifiyarsa Gwaggo gaban EFCC kan zargin rashawa

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana
Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da yake yi mata na almundahana da kuma azurta kanta ta hanyoyin da basu dace ba.
Tuni hukumar EFCC ta aikewa da Hafsat Ganduje mai dakin Gwamnan Kano da goron gayyata domin amsa tambayoyi kan zargin amma taki amsa gayyata, ba  tare da ta bayar da wani uzuri a rubuce ba. 
A cikin wasikar da Abdulaziz Ganduje ya aikewa da EFCC ta shafi  badakalar filaye da kuma kudade. Sai dai kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren yaki cewa komai game da batun da aka yi masa tambaya akai.
Idan ba a manta ba, a baya an zargi Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje da yin badakala ta sama da dalar Amurka miliyan biyar, inda aka nuno shi a wani faifan bidiyo yana karbar dalar Amurka daga cikin kudaden 'yan kwangila, Gwamnan dai ya karyata bidiyon tare da kai karar jaridar Daily Nigerian da mawallafinta Jaafar Jaafar gaban kotu game da batun bidiyon Dala.
Jaridu a online ne suka fitar da maganar wadda har yanzu dai waɗanda lamarin ya shafa ba su ce uffan ba kan lamarin.