APC ta tsayar da ranar zaben shugabanninta a jihohi

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da sakataren kwamitin riƙo na jam'iyyar, Sanata John James Akpanudoedehe ya fitar bayan ya sanya mashi hannu.

APC ta tsayar da ranar zaben shugabanninta a jihohi

APC ta tsayar da ranar zaben shugabanninta a jihohi

Jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya ta tsayar da ranar 2 ga watan Oktobar 2021 a matsayin ranar taronta na jihohi da za a zabi shugabanni a matakin jiha.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da sakataren kwamitin riƙo na jam'iyyar, Sanata John James Akpanudoedehe ya fitar bayan ya sanya mashi hannu.

Rahotanni  na cewa bayan tarukan jihohin, jam'iyyar za ta kuma gudanar da tarukan shiyoyi sannan babban taronta na kasa ya biyo baya.

Jam’iyar ta sanya ranar 15 ga watan Satumba za a fara sayar da fom ga wadanda suke sha’awar tsayawa takarar shugabancin jam’iya a matakai daban daban na jiha.