Kamfanin NNPC ta gayyaci Obasanjo domin ziyartar matatar mai ta Fatakwal
NNPCL ta gayyaci Obasanjo domin ziyartar matatar mai ta Fatakwal
Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL) ya gayyaci tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo domin ya ziyarci matatar mai ta Fatakwal don tabbatar da yanayin ayyukanta.
Wannan ya biyo bayan wata hira da Obasanjo ya yi da Channels Television, inda ya bayyana shawarar Kamfanin Shell cewa matatar ba za ta iya aiki yadda ya kamata ba.
A cewar tsohon shugaban, wanda aka tuntuba domin samun hannun jari a matatar, ya nuna damuwa game da cin hanci da rashawa da ka iya kawo cikas ga ayyukanta.
Obasanjo ya kuma zargi NNPCL da yaudarar 'yan Najeriya game da yadda matatar ke aiki.
Da yake mayar da martani kan waɗannan zarge-zargen, Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na NNPCL, Mista Olufemi Soneye, ya yi kira ga tsohon shugaban ƙasar da ya kai ziyara a matatar, yana mai jaddada ƙudurinsu na gaskiya da amana.
Soneye ya ce: "Bugu da ƙari, mu na miƙa gayyata ga Shugaba Obasanjo domin ya ziyarci matatun mai da aka gyara don ya shaida ci gaban da aka samu ƙarƙashin sabon tsarin NNPC"
managarciya