Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Kungiyar Raudhatu-Rasul Ayagi ta yi bikin bayar da kyaututtuka ga zakarun musabakar yabon Annabi Muhammad S.A.W ranar Talata da ta gabata.
Taron wanda shi ne karon na farko ya gudana ne a unguwar Gwauron Dutse, makarantar Hajara Buhari cikin birnin Kano.
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yabawa wannan ƙungiya inda ya ce "muna alfahari da samuwar irin wannan ƙungiyoyi da matasan cikin al'ummarmu ke yi don yadawa da ƙara fito da darajojin da muujizoji na Annabi Muhammad SAW domin koyi da muujjoji da kyawan halayensa domin jama'ar musulmi sunyi koyi da dabi'u sa dIomin jama'ar musulmai su kwatanta koyi da dabi'u sa don yadawa da kulla don neman karin dacewa a rayuwarmu ta duniya da samun tsira a gobe kiyama"
Bilyaminu Zakariyya Ayagi (Abulwarakat) shi ne shugaban kungiyar Raudha ya ce sun shirya taron ne don zaburar da matasa yadda za'a tsabtace yabon maaiki SAW,
Abubakar Nuhu Saleh shi ya zama na uku da maki 73, sai ta biyu Sa'adatu sani Dalhatu da maki 76, Nafisa Usman Abdullahi da maki 84.
Haka kuma wanda yayi na uku ƙungiya ta bashi dubu 50 sai ta biyu ƙungiya ta ba ta dubu 100, yayin na daya kuma ya rabauta da samun dubu 200.
Taron dai ya samu halartar Hakimin Dala Turakin Kano, Abdullahi Lamido Sunusi, wanda shi ne mai masauki baki sai Isma'il a na Abba Afakallahi da Alh. Ado Ahmad Gidandabino da Hajiya Khadija Bayero (ya Malam) Shugabannin Marubuta wakokin Hausa reshen Kano da Malam Bashir Dandago da da Mahmud Nagudu da Sha'irai da sauran ɗalibai maza da mata.