Yanda ‘Yan bindiga suka kone Mace Mai Ciki Da Jariri Da   Mutum 23 A  Sakkwato

Yanda ‘Yan bindiga suka kone Mace Mai Ciki Da Jariri Da   Mutum 23 A  Sakkwato

 

A Ranar Litinin data gabata wasu mutane 24 a garin ‘yarbulutu sun shiga motar kasuwa da nufin tafiya Abuja, kan hanyarsu sun isa kauyen Gidan Bawa duk a karamar hukumar Sabon Birni ‘yan bindiga suka tare su suka harbi tankin motar da mutanen suke ciki wuta ta shi, anan kuma suka zagaye mutanen sai da suka kone kurmus sannan suka bar wurin.

Dan majalisa mai wakiltar Sabon Birni Honarabul Aminu Almustapha Boza ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu  ya ce barayi sun kone mutum 24 da jariri daya a ranar litinin data gabata macen da jariri ‘yan uwansa ne na jini “Mutum 24 suka mutu in ka hada da jariri 25 kenan, akwai mace mai juna biyu a cikinsu wadda ‘yar uwata ce za ta je ganin marar lafiya Abuja tsananin zafin wutar ya sanya ta haifi cikin nata bayan yaron ya fito duniya ya kone tare da ita.

“Daga garin ‘Yar bulutu ne an yi lodi fasinjojin 24 za su je Abuja  kan yarsu ne a Gidan Bawa barayin suka harbe su, suka cinnawa motarsu wuta, kuma suka zagaye su sai suka kone suka tafiyarsu kuma ga sojoji sun fi 500 a Sabon Birni.

“A duk ranar barayin sun shiga garin Sagerwa da Taka Tsaba da Garin Idi duk a wannan ranar, gaskiya sojoji ba matakin da suke dauka, muna kiransu ba su zuwa,” in ji Boza.  

Kwamishinan Tsaro na jihar Sakkwato Kanar Garba Moyi kokarin Magana da shi ya ci tura domin wayarsa ba ta shiga.

Jami’an tsaron Nijeriya da ke aiki a Sakkwato ba su fitar da wani bayani ba kan wannan lamarin.