Ƙungiyar Makiyaya Ta Jinjinawa Hukuma a shirinta Na Sake Farfaɗo Da Arewa Maso Gabas
Daga Muhammad Maitela, Damaturu.
Kungiyar makiyaya ta 'Kulen Allah Cattle Rearers Association of Nigeria', wadda kungiya ce ta makiyaya zalla, ta yaba wa hukumar raya yankin Arewa Maso Gabas (NEDC) bisa nasarar kaddamar da sabon shirin sake farfado da yankin mai dogon zango na shekaru 10 masu zuwa.
Kungiyar ta bayyana hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ta na kasa, Hon. Khalil Mohammed Bello, a karshen wannan makon, a Damaturu. Inda ya ce masu ruwa da tsaki wajen yafiyar da muhimman ayyukan raya yankin a Hukumar NEDC sun taka rawar gani, saboda haka kungiyar su ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen jinjina da yabawa hukumar bisa kyawawan ayyukan da suke yi.
Ya kara da cewa, wannan sabon shirin raya yankin Arewa Maso Gabas, na shekaru 10 abin a yaba ne a matsayin muhimmin mataki wajen hanzarta bin diddigin matsalolin da matsalar tsaro ta haifar wanda ya nuna cewa za a dauki matakan da ya dace kan al'amarin, kuma samun nasarar hukumar suna bayyana a zahiri a yankin, tare da irin namijin kokarin da NEDC ke yi wajen samar da kayan aiki na zamani don inganta rayuwar makiyaya da kiwon dabbobi a yankin.
Tun bayan da gwamnatin Tarayya ta kaddamar da Hukumar NEDC a 2017, hukumar ta kasance abin alfahari ga mazauna wannan yankin tare da tabuka abin a zo a gani wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na gudanar da ayyukan jinkai, ga al'ummun da rikicin Boko Haram ya shafi rayuwarsu.
Hon. Khalid ya ce yana da kyau a bayyana irin ci gaban da hukumar ta samu kawo yanzu na gine-ginen dubban gidaje domin daukar dawainiyar ‘yan gudun hijira a yankin, samar da wuraren ruwan sha ga makiyaya tare da dabbobin su, ta yadda za a magance matsalar karancin ruwan sha, wanda a kodayaushe yake kawo cikas ga rayuwar makiyaya da dabbobin su. Wanda sau da yawa tilasta wa makiyayan mu kaura zuwa wasu wurare da yawa masu hadari don neman ruwa da abincin dabbobi.
“Wata nasarar da Hukumar NEDC ta yi a yankinmu na Arewa Maso Gabas ita ce shigar da bukatun makiyaya a cikin dukkan tsare-tsare da manufofinsu da shirye-shiryensu. Wannan ya sa mambobinmu su ka kasance cikin annashwa tare da samun ingantacciyar rayuwa a rugagen su, wanda ko shakka babu dole mu yi alfahari da manijin kokarin da NEDC ta yi a matsayinmu na yan Nijeriya, saboda samun hakan shi ne daidaiton kuma adalci da jinkan da suke yi wa kowa."
“Kamar yadda Hukumar NEDC ta bayyana waken kashe sama da Naira biliyan 5.6 wajen gudanar da muhimman ayyuka 647 a fannin noma, kiwon lafiya da sauran ayyukan da suka shafi gina wannan yankin da kuma samar da wadataccen abinci. Wannan abin a yaba ne.” Ya nanata.
Shugaban Kungiyar KACRAN ya kara da cewa, "bisa ga haka zan yi amfani da wannan dama wajen yaba wa gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari, yan majalisun mu na kasa baki daya; a majalisar dattawa da na wakilai bisa kafa kungiyar NEDC, wanda ya zama alheri tare da ceto rayukan miliyoyin al'ummar wannan yanki na Arewa Maso Gabas."
“Kuma muna mika godiya ta musamman ga hukumar NEDC karkashin jagorancin, Dr Muhammad Alkali, da Daraktanta, Alh. Muhammad Jawa Gashua, da jajirtattun ma’aikatanta bisa sadaukarwar da suka yi da kuma jajircewa wajen yi wa kasarsu Nijeriya hidima. Sannan muna kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya da ta kara zage damtse wajen ganin an ci gaba da wadannan muhimman ayyuka na ci gaba a kowane sashen kasar nan" Hon. Khalil.
managarciya