Zanga-zanga a Nijeriya: Abin da Tinubu Ya Gayawa Malaman Izala Da Darika

Zanga-zanga a Nijeriya: Abin da Tinubu Ya Gayawa Malaman Izala Da Darika
 
Malaman addinin Musulunci da suka hada da na bangaren Izala da Darika sun gana da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja. 
An ce wannan tattaunawar ta mayar da hankali ne kan tattalin arziki, sha'anin mulki da kuma batun zanga-zangar da ake shirin yi a ranar 1 ga Agusta.
Kamar yadda fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta na X, malam addinin sun samu jagorancin Sheikh Bala Lau, wanda kuma shi ne shugaban Izala na kasa. 
A nasa jawabin, jagoran tawagar malaman addinin, Sheikh Bala Lau ya baiwa shugaban kasar tabbacin bada goyon baya, addu'o'i da karin fadakarwa ga 'yan Najeriya. 
“Zaman lafiya shi ne babban abu a gare mu a kasar nan. Abu na farko da Ibrahim AS ya roki Allah shi ne zaman lafiya da shiriya. "Za mu ci gaba da gwamnati goyon baya tare da taya ta da addu'a, yayin da kuma za mu kara kaimi wajen fadakar da al'umma." 
Shugaban kasa Bola Tinubu ya shaidawa tawagar malaman cewa masu daukar nauyin gudanar da zanga-zangar sun dora burinsu na son rai fiye da kishin kasa. 
“Masu daukar nauyin zanga-zangar ba sa kaunar kasarmu. Ba su da soyayya ga al'umma. Ba su fahimci muhimmancin zama ɗan ƙasa ba, watakila suna da fasfo na barin kasar ne." "Ba za mu so Najeriya ta koma kamar Sudan ba. Muna maganar yunwa ne ba binne gawarwaki ba. Ya kamata mu yi taka tsantsan da siyasar tsana da fushin wani."