Muna Iyakar Ƙoƙarinmu  Duk Wata Muna Biyan  Albashi----Tambuwal

Muna Iyakar Ƙoƙarinmu  Duk Wata Muna Biyan  Albashi----Tambuwal

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya jinjinawa gwamnatinsa kan duk wata tana yin albashi ga ma'aikatanta kan kari.
Gwamnan a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyar PDP reshen jiha da aka gudanar a gidan gwamnati a wannan litinin ya ce gwamnatin Sakkwato na ƙoƙarin ta yi albashi da gudanar da wasu aiyukka a jiha da yawa wasu jihohi albashin ya buwaya.
Ya yi kira ga 'yan kasuwa da su tausayawa bayin Allah a wurin sayar musu da kayan masarufi da abinci, kar su yi amfani da damar wurin matsar da mutane.
Ya kuma nemi a cigaba da yi wa ƙasa addu'a Allah ya yaye mana wannan matsatsin da ake ciki ya ba mu zaman lafiya a Sakkwato da Nijeriya baki ɗaya.