Yan Ta'adda Sun Kashe Ɗan Majalisa A Kaduna

Yan Ta'adda Sun Kashe Ɗan Majalisa A Kaduna
Gwamnan Kaduna

'Yan Ta'adda Sun Kashe Ɗan Majalisa A Kaduna

'Yan ta'adda masu garkuwa da mutane sun hallaka ɗan majalisar jiha, mai wakiltar mazaɓar ƙaramar hukumar Giwa, Rilwanu Gadagau, a Jihar Kaduna.

Tun da fari, an ɗauke dan majilisar ne wanda shi ne Shugaban kwamitin harkokin ƙananan hukumomi a yankin Dindin Rauga a kan titin Kaduna-Zariya a ranar Litinin da daddare.

Jaridar maganarciya ta rawaito cewa 'yan ta'addan sun kashe ɗan majalisar ne a kan hanyar su ta zuwa maɓoya a cikin daji.

"Tun Litinin da daddare wayar da a kashe. A cikin jeji a ka tsinci gawarsa da safe," inji majiyar.