Daraktan Shiri Mai Dogon Zango Izar So Ya Rasu
Allah Ya Yi Wa Daraktan Fim Ɗin Izzar So Nura Mustapha Waye Rasuwa
Yanzu muke samun labarin rasuwar daraktan shirya fim ɗin Izzar so wato Mustapha Waye rasuwa, kamar yadda producer ɗin fim Lawan Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook.
"Allah ya karbi rayuwar Nura Mustapha Waye Director IZZAR SO, za ayi jana'izarshi ƙarfe 11 na safe Insha Allah, Allah Ya yafe masa kurakuransa Amin, Allah yasa idan tamu tazo mu cika da imani Amin", Inji shi.
Shirin mai dogon zango da ake kira Izar so ya yi suna sosai a tsakanin makallata wasan Hausa na Kannywood.
DAGA Zaharaddeen Gandu
managarciya