MD Galaxy ya taya Ministan Sadarwa Pantami murnar samun lambar Yabo ta CIISec

MD Galaxy ya taya Ministan Sadarwa Pantami murnar samun lambar Yabo ta CIISec

Daga Habu Rabeel, Gombe.

Babban Darakta na Galaxy Backbone Farfesa Muhammad Bello Abubakar, ya taya Ministan Sadarwa Zamani da tattalin arzikin kasa Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami murnar samun lambar yabo ta (CIISec) Charted Institute of Information Security.

Farfesa Muhammad Bello Abubakar, ya taya Ministan Murnar ne ta bakin mai taimaka masa  na musamman a bangaren yada labarai Tasiu Muhammad Pantami, inda yace Ministan ya zama gwarzo abun a yaba masa.

Farfesan yace Minista Ali Pantami, ya ciri tuta domin yana cikin kalilan din mutane yan Najeriya da suka samu wannan lambar yabo domin duk fadin kasashen Afirka su 89 ne kadai suke da irin wannan lambar yabo.

A cewar Tasiu Pantami, MD Galaxy,  ya bayyana Ministan ne da hazikin Minista wanda ya kawowa wa kasar sa ci gaba mai ma'a a bangaren sadarwar zamani tun shigar ofis a matsayin Ministan Najeriya wanda ya maida hankali sosai akan abunda ya shafi harkar tsaron kasa ta bangaren kimiyya da hakan kuma ya haifar da 'Da mai Ido.
 
Farfesa Muhammad Bello Abubakar, ya yabawa cibiyar CIISec na yadda suka zakulo Farfesa Isa Ali  Ibrahim Pantami Ministan sadarwa ganin yadda ya mayar da hankali wajen ci gaban kasa da kula da harkar sadarwar yanar gizo dan ci gaban duniya baki daya suka karrama shi da wannan lambar yabo.

Daga nan sai yace CIISec su kadai ne cibiyar kula da harkar sadarwa ingantacciya da suka samu izinin masarautar kasar Uk tun a shekara ta 2018 da aka daurawa alhakin kula da kwarewar harkar da ta shafi bangaren sadarwa kuma sune suka karrama Ministan

Sannan sai ya sake yin amfani da damar ya sake taya Ministan murna sosai saboda farin cikin da yake da shi wa Ministan..