Zargin karkatar da kuɗaɗe: Tsohon ministan lantarki ya faɗi a kotu
Saleh Mamman, tsohon ministan wutar lantarki a karkashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya fadi a wajen kotu a yau Alhamis a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, sakamakon rashin lafiya.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa, NAN ya rawaito cewa Mamman, wanda aka tsayar da yau Alhamis a matsayin ranar da za a gurfanar da shi, ya kife a wajen kotun kafin a saurari karar.
Lauyan tsohon ministan, Femi Ate, SAN, ya shaida wa mai shari’a James Omotosho jim kadan da aka kira tsohon ministan da ya amsa rokonsa.
Jim kaɗan bayan an ci gaba da sauraren karar, tsohon ministan ya shiga harabar kotun, ya shiga cikin akwakwun da wanda ake tuhuma ke tsaya wa da wani sashi na rigar shi a jike.
Sai mai shari'a Omotosho ya tambayi dalilin da yasa Mamman ke zufa ko kuma ana ruwa a waje ne?
Sai tsohon ministan ya ce an zuba masa ruwa a wajen ne.
Lauyan Hukumar EFCC, Adeyinka Olumide-Fusika, SAN, yayin da yake jawabi a kotun, ya ce duk da cewa an tsara batun ne domin gurfanar da Mamman, amma an samu wani cikas a wajen kotun.
Olumide-Fusika ya ce ya tattauna da Ate a wajen kotun game da rashin lafiyar Mamman.
Daga nan sai mai shari’a Omotosho ya jingine shari’ar har zuwa karfe 1 na rana a yau.
NAN ya ruwaito cewa hukumar EFCC ta shigar da karar Mamman ne kan tuhume-tuhume 12 na karkatar da kudade.
Ana zarginsa da aikata laifukan karkatar da kudi har naira biliyan 33.
managarciya