Taimakon Matasa Da Kishin Yanki Ya Sa An Karrama Zinariyar Yalmatu
Amsa Kira, Daga Bangon Zinariyar Yamaltu
Daga Muhammad Umar Faruk
Kungiyar Hinna Youth forum a taaronta na karshen shekara, na raya al'adu, wasanni da kuma sada zumunci, wanda aka gudanar a wannan shekarar a garin Hinna dake karamar hukumar yamaltu deba, a jihar Gomben Najeriya, ta baada labar yabo ga jaajirtattun muttanen da suka yi kokari matuka wurin taimakawa yankin na Hinna.
Wadanda suka yi fice wurin kawo cigaba da nasarori matuka ma wannan yanki sun samu shedar yabo, karramawa da kuma daraja ta farko a sakamakon hali, dabi'a, kyautatawa da kuma mu'amala da mutane, daga sassa daban daban na yaruwa.
A taaron da aka gudanar a kwanaki ne aka yi mutukar jinjina da yaba wa mai dakin Sen. Abdulallhi Idris Hinna. Wato "Hajiya Hauwa Abdullahi (Zinariyar Yamaltu) domin kawo skills aquisition center da tayi a kwanaki a baya, wanda sanadiyar hakan ya taimakawa matasa maza da maata na wannan yanki wanda a yanzu a akwai mutane da daama wanda suke ci, su sha, su kuma tufatartar da kansu da iyalensu a sanadiyan aikin da suka koya a wannan gurin horar wa.
Anyi launching na magazine akan farashi daban- daban, wasu sun bada kudi a take kuma anbasu magazine nan take, wasu kuma sunsa farashe amma ba'a basu ba, wanda kuma sai gashi kai tsaye labari yazo daga bangon Hajj.Hauwa Abdullahi Idris (Zeenariyar Yamaltu )
Ta tayi launching na magazine guda 10 akan naira dubu dari da hamsin. N150,000.
Gaggarimin bikin da ake gudanarwa a karshen shekaran ya samu halartan manya manyan baki ne daga gida Najeriya da kuma kasashen turai. Wasu daga cikin mahalarta bikin sun hada da Mai girma Hakimin Hinna,
Prof. Hauwa Ibrahim Esq. Hon. Umaru Musa Hinna, Sarkin Shanun Yamaltu, Barr. Nalado A.E, Rad Ismail Idris Hinna, Sen. Muazu Hinna (Matemakin shugaban kungiyan daliben Najeria) Da dai sauran su.
A wannan shekaran an bunkasa abubuwan kallo da nishadi, domin duk mutanen da suka halinci wanna taron sun bayyana matukar jin dadin su da annashuwan da suka ji a yaayin da bikin ke gudana, a wannan shekaran an baje kolin al'adonmu na gargajiya, don tasu da gargajiya a gurduman hinna, domin farfado da su saboda kar su gushe.
A wannan shekaran anyi wasanni da abubuwan daban_daban hada da hawa dutsan Bima, Rally na kai ziyara zuwa fadan dakacin dakum, girke_girke na abincin gargajiya, wasan kwallo don karfafawa hadin kan matasan, Wasannin gudun buhu, gudun kwai, wasan tsare, wasan cin apple da zumbaya kowani rana.
A taron dai an nuna aladu daban daban da abincin su, sannan akayi bayanai akan alfanon kawo "Gombe industrail Park" wannan yanki. Har ma wasu masana akan harkan yau da kullum sukayi jan hankali ga masu hannu da shuuni na wannan yanki da kar suyi wasa da daama wurin siyan pegi ko manyam filaye da wurwuri a wannan guri.
A cikin taron ne masana suka shawarci matasa da suyi bincike akan wani irin kampanoni ne zasu zo wannan yanki, kuma su tabbata sun koyi sana'a hannu wanda za'a fi bukata a wa'innan campanoni da zasu shigo wannan yanki, kar ya zamo sun kasa cin ma moriyar wannan industrial park domin a nan gaba kadan, wannan guri ze girma kuma kafun nan ze zamto sunada aikin yi da kuma abun dogaro da kai.
An ja hankalin masu hannu da shuuni da suyi koyi da halin Haj. Hauwa Abdullahi, an kuma shawarci matasa da su ji tsoron Allah, su guji shaye-shaye, pitina da taashin hankula, su kuma jajirce suga ce wa ba'a bar suu a baya ba, wurin biyaiyyah wa iyaye da na gaba da su, kuma su bada hadin kai domin cigaban kasar Hinna da Najeria baki daya.sannan Dan Allah muke hakuri da junan mu
Kungiyar hadin kan matasan hinna wato "Hinna Youth Forum" tana kaara farin cikin gayyatan Al'umman Gombe da ma al'umman duniya baki daya a ko da yaushe zuwa wasan shekara _shekara datasaba gabatarwa a karshen kowani shekara, a wannan shekaranma cikin ikon Allah wannan kungiyar ta kammala taron lafiya kuma tana fata Allah sa ayi na gaba a sa'a
Wannan taron za'a fara gudanar da shine ranan 26th ga watan December wanna shekaran zuwa 30th ga watan December wanna shekaran na 2024.
Taron na shekarar 2023 ya gudana a karkashen jagorancin hazikin shugaban kungiyar wato Comr. Musa Umar Hinna.
managarciya