Gwamnan Bauchi Ya Kaddamar Flyover Ta 10 Da Wike Ya Gina A Rivers 

Gwamnan Bauchi Ya Kaddamar Flyover Ta 10 Da Wike Ya Gina A Rivers 

 

Gwamnan Bauchi Bala Muhammad ya fadi yanda yake son a tsayar da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP don tun karar zaben 2023.

Ya bukaci takarar ta zama Muhammad/Wike su ne za su yiwa jam'iyar PDP takarar a zabe mai zuwa, don haka ya yi kira ga mutanen Nijeriya su ba da dama ga gwamnan jihar Rivers ya jagorance su a babban mataki.
Gwamnan ya furta hakan ne a wurin kaddamar flyover ta 10 daga cikin 12 da gwamnatin Wike ta samar a jihar Rivers.

Ya ce duk da ya kaddamar da kudirinsa na son ya yi takarar shugaban kasa kan haka yana bukatar nagartattun mutane a kusa da shi domin ya cimma muradinsa.
Ya yaba aikin da gwamna Wike ke yi wa jiharsa a lokacin da wasu gwamnoni ke kokarin hada kayansu domin barin ofis komi a jiha ya tsaya amma shi kam kamar yanzu ne yake wa'adinsa na farko.