Atiku Ya Shirya Zuwa Kano Domin Karbar  Shekarau Daga Jam’iyyar NNPP Zuwa PDP

Atiku Ya Shirya Zuwa Kano Domin Karbar  Shekarau Daga Jam’iyyar NNPP Zuwa PDP

 

Atiku Abubakar mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023 zai ziyarci jihar Kano domin zawarcin Ibrahim Shekarau. 

Kamar yadda muka samu labari daga BBC Hausa a ranar Asabar, Atiku Abubakar zai je jihar Kano domin karasa farautar magoya bayan Sardaunan Kano.
Wata majiya ta shaida cewa ‘dan takaran zai jawo tsohon gwamnan na Kano bayan an ji yana kukan cewa Rabi’u Kwankwaso ya yaudare su a NNPP. 
Wannan taro da za ayi gobe zai zo gabanin sanarwar da Sanatan jihar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau zai bada na sake shiga  jam’iyyar adawar. 
Rahoton da muka samu daga Sahelian Times yace tsohon Gwamnan na Kano zai shiga kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar a shekara mai zuwa. 
Malam Shekarau yana cikin wadanda za su jagoranci takarar PDP a yankin Arewa maso yamma. 
Ana sa ran zai taimaka wajen yakar gwamnatin APC.
Idan abubuwa sun tafi yadda aka tsara, gobe jirgin Wazirin na Adamawa zai dura jihar Kano. 
Har zuwa ranar Juma’a, dan takaran na PDP yana Ingila. 
The Cable tace PDP za ta bar wa Shekarau takarar kujerar Sanatansa a zaben 2023. 
Baya ga haka, za a ba tsagin Shekarau mukamai idan ya bi tafiyar Atiku. 
Tun tuni ake rade-radin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wa Shekarau alkawari masu tsoka, amma Sanatan ya musanya wadannan maganganu.