Kwamishiniya A Ma'aikatar Kimiya Da Fasaha Ta Jihar Sakkwato Ta Yi Murabus

Kwamishiniya A Ma'aikatar Kimiya Da Fasaha Ta Jihar Sakkwato Ta Yi Murabus

 

Kwamishiniya a ma'aikatar Kimiya da Fasaha ta jihar Sakkwato Dakta Kulu Haruna ta yi murabus daga majalisar zartawa a gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal.

Kwamishiniyar ta ajiye aikinta a yau Litinin saboda rashin daukar shawara da gwamnatin ke yi, a harkokin da suka shafi  cigaban jihar Sakkwato.
Managarciya ta samu labarin ajiye aikinta ga daya daga cikin makusantanta in da ya tabbatar da ajiye aikinta domin ita mutum ce mai son kawo cigaba.
Majiyar ba ta bayyana in da tsohuwar kwamishinyar ta sanya a gaba  a harkar siyasarta, sai dai a jira a gani matakin da za ta dauka a nan gaba kadan.
Wakilinmu ya yi hasashe sanannar 'yar siyasar da wahalar gaske ba jam'iyar APC za ta koma ba, kamar yadda wasu masu sharhi ke ganin jigo a harkar siyasa baya karamar jam'iya a Nijeriya.