YANDA ZA KI HAƊA DENDERUN KAYAN CIKI NA MUSAMMAN
DENDERUN KAYAN CIKI
Ingredients
Kayan ciki
Ginger powder
Black pepper
Curry
Spices
Nikakken attarugu da tafarnuwa
Yankakkiyar albasa
Seasoning cube
Oil
Procedure
Da farko zaki wanke kayan cikinki sai ki yanyankka girman da kike so ki tsane su.
Daga nan sai ki zuba ginger powder, black pepper attarugu, curry, spices, seasoning sannan ki saka yankakkiyar albasa da ɗan mai kaɗan. Ki cakuɗe su gabaɗaya har sai ya haɗa jikinsa.
Sai ki shimfiɗa parchment paper ko takarda a cikin baƙar leda ki ɗaure.
Sai ki ɗaura tukunya babba a wuta, ki saka ruwa kaɗan ki saka ƙaramin murfi da zai zauna a cikin tukunyar ki danne ruwan. Sai ki ɗora ledar a kai ki rufe da wani murfin ki bar shi ya turara sosai.
Idan ya zama ready zaki ji yana ta ƙamshi sai ki taba ki ji idan ya yi miki ki sauke. You can add yaji idan kina so.
Enjoy it.
managarciya