Likitoci 199 Cikin 280 a Jihar Zamfara Ma’aikatan Bogi Ne---- Gwamna Matawalle 

Likitoci 199 Cikin 280 a Jihar Zamfara Ma’aikatan Bogi Ne---- Gwamna Matawalle 
https://hausa.legit.ng/news/1514476-likitoci-199-cikin-280-a-jihar-zamfara-maaikatan-bogi-ne-inji-gwamna-matawalle/

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta gano likitoci 199 da ke kan tsarin biyan gwamnati alhali na bogi ne. 

Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar na biyan albashi ga likitoci 280 amma a zahiri akwai likitoci 81 ne a jihar, Daily Trust ta ruwaito. 
Matawalle ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema a gidansa da ke Maradun, hedkwatar karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara. 
Ya kuma kara da cewa, wannan lamari na ma'aikatan kwata-kwata babu su amma suna cin gajiyar kudi na ba gwamnati wahala wajen biyan albashi. 
Ya kuma bayyana cewa, ya gama kai da kungiyar kwadago ta NLC da sauran masu ruwa da tsaki don zakulo ma'aikatan bogin da suka dade suna lashe kudin jihar. 
A cewarsa, zai yi hakan ne domin tabbatar da gyara a fannin aikin da kuma tabbatar da hukunta wadanda ke cin haram, Osun Defender ta tattaro. 
"Masu ruwa da tsaki sun tabbatar min cewa abin da yasa ake samun jinkirin biyan ma'aikatan lafiya albashi yana faruwa ne saboda suna son tabbatar da abubuwa sun tafi daidai kuma muna kokarin magance duk wata kitimurmura da ke fannin lafiya nan kusa."