Tambuwal Ya Baiwa Ma'aikatan Gwamnati Masu Sha'awar Takara Awa 24  Su Ajiye Aiki

Tambuwal Ya Baiwa Ma'aikatan Gwamnati Masu Sha'awar Takara Awa 24  Su Ajiye Aiki

Gwamnatin jihar Sakkwato ta baiwa ma'aikatan da ke sha'awar tsayawa takarar wata kujera a zaɓe mai zuwa na 2023 wa'adin awa 24 su ajiye muƙaminsu.
A bayanin da aka fitar a ranar 7 ga Maris daga shugaban ma'aikata Abubakar Muhammad ya nuna matakin an ɗauke shi ne kan dokar zaɓe da aka yiwa gyara.

An naɗa wani jam'i a ofishin shugaban ma'aikata domin karɓar takardun waɗanda suka ajiye aiki.
Masana na ganin dokar bata nufin ma'aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa take magana.

Shugaban ma'aikata ya ce sun yi haka ne kan dokar zaɓe haka ta tanada.