'Yan Nijeriya Dubu 500 Za'a Dawo Da Su Daga Gudun Hijira A Maƙwabtan Ƙasashe
Ta kara da cewa "wani abu da ke kara ba da tsoro shine wannan matsala ta sa mutanen da suka rasa matsugunansu a Najeriya a yanzu ya kai mutum miliyan uku." Akan haka kwamishinar ta nemi a kara wa ma'aikatar karin kudin takalihun yan gudun hijirar, akan abinda aka ware a kasafin kudin 2022.
Kwamishinar hukumar kula da 'yan gudun hijira da ci rani ta Najeriya Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta ce rikice-rikicen da ke faruwa a kasar sun tilasta mutum sama da miliyan daya barin gidajensu a shekarar da ta gabata.
Imaan Sulaiman ta fada wa kwamitin majalisar tarayya da ke da alhakin kula da 'yan gudun hijira cewa, yanzu haka ana shirin mayar da 'yan Najeriya sama da 500,000 gida daga kasashe masu makwabtaka da ita.
" Irin ta'azzarar da rikici ke yi a Najeriya ya sa an samu karuwar mutanen da ke rasa matsugunansu sosai, don yanzu haka adadin yan gudun hijira da ake da su ya karu da fiye da mutum miliyan daya a shekarar da ta gabata." Inji kwamishinar.
Ta kara da cewa "wani abu da ke kara ba da tsoro shine wannan matsala ta sa mutanen da suka rasa matsugunansu a Najeriya a yanzu ya kai mutum miliyan uku."
Akan haka kwamishinar ta nemi a kara wa ma'aikatar karin kudin takalihun yan gudun hijirar, akan abinda aka ware a kasafin kudin 2022.
To amma a nasu bangaren, kwamitin ya bukaci a samar da cikakkun bayanan wadannan mutane kafin ya aiwatar da karin kudin da hukumar ke bukata.
managarciya