An Shawarci Gwamnati Ta Bude Iyakokin Shigo da Abinci Domin Magance Yunwa a Najeriya

An Shawarci Gwamnati Ta Bude Iyakokin Shigo da Abinci Domin Magance Yunwa a Najeriya

 

Hukumar kula da kiyaye hakkin masu sayayya (FCCPC) ta shawarci gwamnatin tarayya ta buɗe iyakokin kasar nan domin shigo da kayan abinci ta halastacciyar hanya. 

Hukumar na ganin ta hanyar bari a shigo da kayan abinci ne kawai za a rage yunwar da ta addabi 'yan Najeriya. 
Nigerian Tribune ta wallafa cewa mukaddashin shugaban hukumar, Adamu Abdullahi ne ya bayyana bukatar bude iyakokin kasar a Bauchi.
Hukumar kare hakkin masu saye ta Najeriya ta ce ta na sanya idanu kan yadda ake samun hauhawar farashi a kasuwannin kasar nan. Mukaddashin shugaban hukumar, Adamu Abdullahi ne ya bayyana haka a wani taro da ya gudana a dakin taron fadar Bauchi, jaridar Independent ta wallafa. 
Ya ce su na ganin yadda farashin kaya ke hawa a kasuwanni, kuma za su tabbata ba a rika shiga hakkin masu sayen kaya ba. Ya ce yanzu haka su na wayar da kan jama'a kan tsawwala farashi kan kayayyakin da su ke sayarwa jama'a.