'Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibbai mata 25   a Kebbi

'Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibbai mata 25   a Kebbi
'Yan sanda sun tabbatar da dalibai mata 25 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a dakin kwanansu dake Sikandaren gwamnati ta Maga a yankin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu.
A bayanin da jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda a jihar CSP Nafi'u Abubakar ya fitar ya ce jami'an tsaro tare da hadin kan 'yan sintiri sun shiga makwabtan dajin don kokorin karbo yaran.