Sama da Wata ɗaya da  ƙaddamar da jami’an tsaron Sokoto ba su fara aiki

Sama da Wata ɗaya da  ƙaddamar da jami’an tsaron Sokoto ba su fara aiki

Jami’an tsaron da gwamnatin Sakkwato ta kafa domin taya jami’an tsaron kasa yakar ‘yan bindiga da suka addabi jihar da kewayenta, sai dai tun bayan kaddamarwar jami’an tsaron ba su fara aiki ba.

Jami’an tsaron Gwamnan jiha Dakta Ahmad Aliyu ne ya kadammar da su a gaban gwamnoni 7 da suk fito daga Kano da Zamfara da Kebbi da Katsina da Bauchi da Filato da Benue, in da ya sanar da su matakin da ake bukatar dauka kan matsalar tsaron da ta addabi yanki.

"A yau da muke yaye wadanda aka baiwa horo domin kare jami'an tsaro don kowa yasan matsalar tsaron da ake fama da shi  wanda ya dauki shekaru ana fama da shi a jiha in da ake karbar kudin fansa da tarwatsa kauyukka, jami'an tsaron kasa suna kokari kwarai.

"Lamari ne na hadin kai gaba daya in za a iya magance matsalar matukar aka samu hadin kan jami'an tsaro da al'ummar gari, kan haka ne muka yanke shawara gwamoninin Arewa za mu samar da tsaro mallakar jiha domin su biya bukatar jami'an tsaron kasa a wurin samar da tsaro.

"Jami'an tsaron da yawansu ya kai 2600, an ba su horo ne bayan an tantance su da tabbatar da nagartarsu muna sa ran su bi dokar aiki, za su soma aiki da motoci 30 da babura 800 ne aka samar musu don yin aiki cikin lumana.

"Maganar yakar 'yan bindiga ba abu ne na siyasa ba don su ba ruwansu da jam'iyar siyasa, mun dauki hanyar karfafa harkar tsaronmu a jiha". Jawabin Gwamnan Sakkwato kenan a lokacin kaddamar da jami'an tsaron  jiha da aka sanaywa suna da dan gari a kan ci gari.

Tun ranar da aka yi bukin a watan Maris gwamnatin jiha ta sake kwashe motoci da babura ta mayar da su a gidan gwamnatin jiha ta ajiye tare da sanar da jami'an tsaron kowa ya tafi gida sai an neme shi.

Daya daga cikin jami'an da aka yaye ya yi magana da Aminiya ya ce tun sanda aka ba mu horo gwamnati ta ba mu dubu 50 bayan kudin ba mu sake ji daga gwamnati ba kusan tsawon wata  daya kenan.

Ya ce wasu daga cikinmu sun fara tunanin nemo wata harka domin wannan aikin da aka dauke mu ba san in da aka kwana ba, wata daya ba a yi maku magana ba bayan kuma an ba ku horo.

Ya ce ba su samn matakin albashinsu ba yanda tsarin aikinsu zai kasance an dai ba su horo amma ba wani tsari da an ka sanar da su a cikin tafiyar da aikin an barsu kara zube.

Shugaban riko a karamar hukumar Illele Alhaji Sahabi Isah Wakili ya ce bayan kaddamar da jami'n tsaro a matakin kananan hukumomi sun yi zama uku da jami'an kamar yadda gwamna ya bayar da umarni zaman na da alfanu sosai don ganin an yi wa kowane gefe adalci mun gudanar da sako na sirri gare su.

Ya ce duk sanda gwamnatin jiha ta shirya jami'an tsaron su fara aiki su a shirye suke domin su biyayya ya sa suka tura jami'an sika tafi Sakkwato karbar horo, kafin haka su ne abokanmu na shiga daji don ceto al'umma, yanzu haka jami'an namu a matse suke su soma aiki.

"Mutanen Illela suna da biyayya da bin doka gwamna ya ce su jira, kuma ai ba a basu kayan aiki ba, muna jiran umarnin soma aiki daga mai girma gwamna,"shugaban karamar hukuma.

Mai baiwa Gwamna shawara kan harkokin tsaro Ahmad Usman wakilinmu ya tuntube shi domin sanin dalilin tsaikon da aka samu na soma fara aikin jami'an da mi ya faru gwamnati ta aminta da gina masu ofis a jiha ba a yi ba, ya ce a same shi ofis don karin bayani da ya je baya ofis baya nan kuma ya ki daga waya bayan kiransa.