Sojoji sun hallaka ƴan fashin daji biyu da suka zo daukar kudin fansa

Sojoji sun hallaka ƴan fashin daji biyu da suka zo daukar kudin fansa

Sojoji sun harbe ƴan fashin daji guda biyu har lahira a yayin da suka yi yunkurin karbar kudin fansa na Naira 1.5 na mutane 4 da suka yi garkuwa da su a kauyen Mai-Iddo dake karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Daily Trust ta rawaito cewa rahotanni sun bayyana cewa mutanen da aka yi garkuwa da su sun hada maza 3 da karamin yaro daya da aka sace su makon da ya gabata.

Wani shugaban al'umma a yankin ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust.

Ya ce, an kashe ƴan fashin dajin ne a yayin da shugabansu ya umarce su da suje wani wuri, inda aka tsara ajiye kudin fansar tare da sakin mutanen da suka yi garkuwa da su.

Ya ce, "An kammala shiri da sojoji da mutumin da zai kai kudin fansar. A yayin da ya isa wurin da aka tsara sai sojoji suka yi abinda ya dace.

" A yayin da 'yan fashin daji biyu suka fito daukar kudin fansar, sai sojoji suka bude musu wuta inda suka kashe biyu daga cikin su nan take".

Ya ce sojoji sun ceto mutanen da aka sace tare da mika su ga iyalansu.