Ramuwar Gayya: 'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Zamfara 

Ramuwar Gayya: 'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Zamfara 

A Najeriya rahotanni daga garin Nasarawar Zurmin a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar sun ce wani ɗan sanda ya rasa ransa yayin da biyu suka jikkata a harin da yan bindiga suka kai da yammacin jiya Lahadi

Rahotanni sun ce maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi tare da kone gidaje.

Wasu bayanai da BBC ta tattara, sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wani sumame da jami’an rundunar kare fararen hula da gwamnatin jihar ta samar suka kai maɓoyar ƴan bindigar, tare da kashe wasu daga cikinsu, da kuma kwashe makamansu, lamarin da ya sa jiya Lahadi, da yamaci, ƴan bindigar suka yi shiri na musamman suka tunkari garin na Nasarawar Zurmi, yayin da mutane ke Shirin yin sallar magariba, kamar yadda wanan mazaunin garin da muka sakaye sunansa, ya shaidawa BBC .

‘‘Muna hira dab da mu yi magriba, kawai sai muka ji ɗa-ɗa-ɗa, ƴan bindiga kawai sun fara harba bindiga yadda ka san tururuwa ta fito. Suka ɗauki hankalin ƴan caji-ofis don muna kusa da caji-ofis, haka suka shigo garin suna kabbara suna harbi kowa ya kama kanshi, ƴan caji-ofis sukai ta ɗauki ba daɗi da su. Cikin ikon Allah mataimakin DPO na yankin shi ma Allah ya amshi ranshi.’’