Zulum Ya Ziyarci Abdulsalam Abubakar a Jihar Neja

Zulum Ya Ziyarci Abdulsalam Abubakar a Jihar Neja

Daga Yusuf Abacha.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a yau Juma'a, ya ziyarci tsohon shugaban mulkin soja, Janar Abdussalami Abubakar a gidansa dake kan tudu dake Minna, babban birnin jihar Neja.

Ziyarar da Zulum ya kai domin duba lafiyar tsohon shugaban kasa, Abdulsalam ya kuma nuna jin dadinsa kan kokarin samar da zaman lafiya a Borno wanda Gwamna Zulum ke yi.

A ziyarar da ya kai a Minna, Gwamna Zulum ya ba wa Janar Abdulsalami

Gwamnan ya ziyarci tsohon shugaban kasa ne tare da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello.

Zulum ya yi tattaki zuwa Minna ne daga Abuja tare da wasu jami’an gwamnati, daga cikinsu akwai Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume, da kuma babban mai shigar da kara na majalisar wakilai, Barista Mohammed Tahir Monguno, kamar yadda majiyar Yola 24 ta ruwaito.