Yadda Wani Ɗan China Ya Kashe Budurwarsa A Gidan Mahaifanta A Kano

Yadda Wani Ɗan China Ya Kashe Budurwarsa A Gidan Mahaifanta A Kano

Wani ɗan ƙasar China ya je gidansu wata matashiya ya daɓa mata wuƙa abin da ya yi sanadin raba ta da duniya da misalin karfe 10 na daren ranar Juma’a ne mutumin ya yi wannan danyen aiki a yankin Janbulo dake unguwar Dorayi a Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce daga baya zai yi karin haske.

Kokarinmu na jin ta bakin ’yan uwanta ya faskara, amma makwabtansu sun ce matashiyar, Ummu Kulsum Sani Buhari, mai shekara 23, wadda aka fi sani da Ummita, budurwar dan Chinan da ya kashe ta ne

Sun ce ya kashe ta ne bayan ya ziyarce ta a gidan iyayenta, amma babu wani cikakken bayani kan abin da ya faru tsakaninsu har ya yi mata wannan danyen aiki.

Wani makwabcinsu, Abubakar Mustapha, ya shaida wa Aminiya cewa marigayiya Ummukulsum bazawara ce, kuma dan kasar Chinan maneminta ne, kuma ya kasance saurayinta kafin aurenta na fari.

Abubakar Mustapha, “Saurayinta ne tun kafin aurenta na fari, da aurenta ya mutu kuma suka ci gaba da soyayya kuma yana yawan zuwa gidansu.

“An kai ta Asibitin UMC Zhair wanda ke kusa da gidansu inda a nan ta rasu.

“Dan uwanta, Khaleed, ya hana mutane daukar mataki a kan saurayin nata bayan ya dawo ya dauki motarsa a gidan.

“Khaleed ya hana su daukar doka a hannunsu ne saboda kada hakan ya haifar da wata matsala, amma an kama mutumin na damka shi a hannun ’yan sanda,” in ji Mustapha.

Shi ma wani makwabinsu, Muhammad Sani, ya shaida wa wakilinmu cewa dan Chinan ya kusa kashe kansa saboda ita, amma aka yi nasarar hana shi, da taimakon ’yan sanda.

“A lokacin da za ta yi aure ya yi yunkurin kashe kansa saboda yadda yake tsananin son ta, sai da ’yan sanda suka shiga stakani aka sasanta,” in shi shi.

Ya bayyana cewa an mika wanda ake zargin a Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke unguwar Dorayi.

Ya ce tuni aka yi jana’izar marigayiyar da misalin karfe 10 na safe bisa tsarin Musulunci.