A A Rano Ya Karyata Maganar Mayarda Farashin Mai Kan 400

 A A Rano Ya Karyata Maganar Mayarda Farashin Mai Kan 400
 

A yammacin Laraba, 5 ga watan Yuli 2023, rade-radi su ka fara yawo cewa kamfanin A. A Rano ya karya farashin man fetur. Kafin a je ko ina, kamfanin man ya yi maza-maza ya musanya wannan magana, ya nuna cewa babu alamar gaskiya tattare da batun. 

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa sanarwar ta fito ne daga wani shafi da mu ke kyautata zaton na kamfanin A. A Rano Nigeria Ltd ne. 
Gajeren jawabin da aka fitar da kimanin karfe 10:00 na daren yau ya tabbatar da farashin mai yana nan yadda aka san shi a kamfanin. 
Ba tare da wani kame-kame ba, kamfanin ya ce babu inda yake saida litar man fetur dinsa a kan N400 a duk gidajen man da yake Najeriya. 
"Shugabannin kamfanin AA Rano su na masu karyata wani bayani na karya kuma mai batarwa dangane da saida man fetur a kan N400 a wasu zababbun gidajen mai.
 Ayi watsi da wannan labari na karya kaco-kam dinsa." 
- Kamfanin AA Rano Nigeria Ltd