SPANISH INDOMIE:Girki Mai Matukar Dandano

      SPANISH INDOMIE:Girki Mai Matukar Dandano
BASAKKWACE'Z KITCHEN
 
 
 
     
 
 
INGREDIENTS
Indomie
Sydin (kifin gwangwani)
Tattasai, attarugu, albasa.
Ƙwai
mai
jan onga
 
 
 
METHOD
Da farko aunty na ki daka Kayan miyanki amma banda ƴaƴan tattasan, ki juye a wani bowl Mai kyau, ki faffasa indomie inki har ya fara gari, sai ki xuba akan kayan miyan ki gwauraya, sai ki ɓare magin cikin indomien ki zuba akai kisa jan onga kaɗan, sai kisa sydin Amma banda manshi, ki gwauraya shi sosai, sai ki dinga mulmulashi kaman kwai kina ajiyewa a gyefe.
 
Ki fasa ƴwai kisa maggi da albasa, ki ɗaura frying pan akan wuta kisa mai, sai ki dinga daukan indomien kina sawa a ƙwan kina soyawa.
 
Bayida wuya Zaki Iya yiwa maigida da safe yayi breakfast dashi.
 
 
MRS BASAKKWACE