YANDA  AKE HADA TALIYA CUCUMBER SALAD

  YANDA  AKE HADA TALIYA CUCUMBER SALAD
BASAKKWACE'Z KITCHEN
 
   TALIYA CUCUMBER SALAD
 
INGREDIENTS
Taliya
karas
koren tattasai
kokumba
albasa
kantum
maggi
mangyaɗa
 
METHOD
Da fari aunty na za ki samu tukunyar ki ki ɗauraye ki zuba ruwa ki ɗaura kan wuta,ki rufe in ta tafaso kisa taliyar ki jujjuya, ki ɗauko yankakken karas ɗinki da kika kankare masa baya kika wanke kika yanka ki zuba,ki rufe tukunyar ki zuba ki rufe ya tafaso tare ki juye a matsami ki ɗauraye, se ki ɗauko bowl ki juye ki karwo yankarkan  kokumber ki ki zuba ,ki ɗauko kantum ki zuba,ki ɗako yankakkar albasar ki ki zuba,ki ɗauko koren tattasan ki ki zuba,ki sa magi kaɗan da ɗan gishiri ki zuba mai iya yanda kike so ki juya sai ci. 
 
MRS BASAKKWACE