Wajibi Ne Al'umma Su Ƙarfafa Makarantun Islamiyya - Tallafin Bosso

Wajibi Ne Al'umma Su Ƙarfafa Makarantun Islamiyya - Tallafin Bosso

 

Daga Awwal Umar Kontagorà a Minna

 

 

An nemi al'umma da su karfafa makarantun islamiyya dan samar da ilimin addini da inganta tarbiyar yara masu tasowa, rashin ilimin addini ga yara babban hasara ne da mayar da rayuwarsu baya. Tallafin Bosso karami, Ambasada Nura Hashim ne yayi kiran a lokacin walimar daliban da suka sauke Al-qur'ani mai tsalki aIslamiyyar Madarasatul Hudal Islam Watafizul Qur'an da ke Elwazir Estate da ke Bosso.

Tallafin ya cigaba da cewar yadda iyaye ke karfafa guiwar yayansu wajen karatun boko da haka suke karfafa guiwar yayansu wajen karatun addini da an samu cigaba da samar da shugabanni a gaba wadanda suka san addini da shugabanci na adalci. Yara na kammala karatun boko kuma ba aikin yi, ba yadda za a samu ilimin addini sannan mutum ya zama cima zaune.
Yayan mu masu tasowa a gaba na bukatar kulawar iyaye dan samun tarbiya mai inganci wanda ke zama silar kyautata tunani da kusanci ga Allah, makarantar nan an kafa ta a shekarar 2000 da dalibai ashirin da bakwai yau tana da daruruwan dalibai amma saboda rashin mayar da hankalin al'umma har yanzu tana da matsalilo jibge, dan haka ina kira da babban murya ga iyaye da masu hannu da shuni da su juyo su dubi irin gudunmawar da wannan islamiyyar ke bayarwa.
A na shi jawabin, shugaban karamar hukumar Bosso, Hon. Abubakar Gwamna da ya samu wakilcin Hon. Muhammad Danlami Ningau, yace tabbas matsalar islamiyyu na daya daga cikin abinda ya tsaya a zuciyarsa, dan haka a matsayinsa na kasancewa dan takarar majalisar dokokin jihar Neja a zaben 2023 mai zuwa, idan Allah ya ba shi nasara zai tabbatar ya gabatar da kudurin doka wajen zai baiwa gwamnati damar shiga lamarin islamiyyu dan tallafa masu saboda irin gudunmawar da suke bayarwa wajen inganta tarbiyar al'umma.
Hakimin Bosso da ya samu wakilcin Dagacin Arewan Bosso, Malam Musa Ibrahim Dodo, yace masarautarsa a shirye take wajen hada hannu da kwamitocin islamiyyu saboda irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ilmantar da al'umma.
Hakimin ya jawo hankalin iyaye wajen sauke nauyin da ya rataya akan su na baiwa yayansu ilimin addini da na zamani tare da koyar da sana'o'in hannu da wannan ne kawai za a iya kawo karshen dabanci da gurbacewar tarbiyar matasa.
Hudal Islam tana dalibai dari hudu da hamsin da takwas inda tayi walimar daliban da suka sauke Al-qur'ani mai tsalki su ashirin da bakwai, maza goma, mata kuma goma sha bakwai a harabar makarantar asabar din makon nan.