Kujerar Gwamna:Ba Nadi Mu Kayi Ba Zabe Ne Halastacce- Jam'iyar APGA

Kujerar Gwamna:Ba Nadi Mu Kayi Ba Zabe Ne Halastacce- Jam'iyar APGA

 

Daga Awwal Umar Kontagora a Minna

 

Jam'iyyar APGA ta bayyana cewar zaben takarar kujerar gwamna Neja ta gudanar da sahihin zabe ne ba nadi tayi ba. Shugaban jam'iyyar a jihar Neja, Malam Musa Aliyu Liman ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala zaben da bada sakamakon zaben da ta gudanar.

Yace kujerar majalisar dattijai da na wakilai, da yan majalisun jiha yar jejeniya ce tsakanin yan takarar, saboda wasu sun janye ma wasu saboda muradin ganin mun samu nasara a babban zabe mai zuwa kamar yadda dokar zabe ta amince.
Musa Liman, yace a bangaren kujerar mutum biyu suka rage kuma an kasa samun daidaito yasa dole muka baiwa masu zabe damar yin zabe bisa sanya idanun hukumar zabe ta kasa. Takarar kujerar ya gudana ne tsakanin Injiniya Usman Muhammad da Hajiya Khadiza Abdullahi, inda Injiniya Usman ya samu kuri'u ashirin yayin da Hajiya Khadiza ta samu kuri'u dari da arba'in da daya, yanzu mace ce yar takarar mu ta kujerar gwamna a jihar Neja.
Shugaban ya bayyana cewar bisa tarihin wannan jam'iyyar wannan karon farko da mace ta samu nasarar yin takarar kujerar gwamna duk da cewar muna shiga takara kuma muna samun nasara a zabukan da suka gabata.-inji shi